← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 126

Sashe 34

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A Amenity word aka bama zee gàdo tun jiyan da sukazo likitoci sun dubata nan suka yi iya kokarin su suka tsayar mata da jinin da take zubarwa, sannan suka daura mata ruwa, sannan sukace aje a siyo jini za'a kara mata, don ta zubar da jini ya wuce misali, hajja fati tambayar zee tayi ko ina mai gidanta taga har sun kwana bai zo ba , bayan jiya zee ta tabbatar mata da cewa yasan abinda ya sameta, cewa kawai tayi baya nan,

Tun daga haka hajja fati bata kara mata wani tambayar ba, ita dai tana taimakon ta ne saboda Allah da kuma kasancewar ta mace mai tsananin tausayi,

Daidai lokacin kuma dad ya iso. cikin asibitin, Amenity ya nufa kamar yadda zee ta fad'a mai a waya, ganin yadda zee ta koma ba ƙaramin tashi hanakalin dad yayi ba , take ranshi ya kara baci fushin shi ya lunku sosai fiyeda da, take ya ciro waya ya kira wani tsohon abokin tun na yarinta, ɗan sanda ne mai babban muƙami, ya sanar dashi yana son a kama Aslam a mai duka , a kulle shi a cell, kullum ana dukan shi, kuma kar a bada beli shi ga ko waye har sai shi ya bada umarnin a sake shi,

Nan ya buƙaci da mutumin ya turo account number, take kuwa ya tura da account number din ganin yawan makudan kuɗin da dad ya mai transfer yasa ba shiri, ya aika yara mota uku zuwa gidan su Aslam domin a kamo shi,

Dad daga nan kuma ya nufi office din Dr don jin taka maimai meke damun zee, Dr yamai bayanin komai harda batun jini Leda daya da akeson za'a kara mata, take Dad yace a dibi jininshi tunda iri daya ne da nata haka ko akayi,

Da asuba ma Aslam bai fito masallaci ba, a daki yayi sallah asubah don kwata kwata baya jin dadin jikinshi ma,

Daddy bayan sun idar da sallah ,ya tambayi me gadi Aslam ya shigo gidan ne, nan kuwa mai gadi ya tabbatar ma da daddy cewa ya shigo tun jiya da yamma kuma dai baiga fitar shi ba yana da tabbacin yana cikin gidana, har yanzu,

Tun kafin su fito daga masallacin jini yar motar police ya karade layin gidan gaba daya, koda suka fito sunyi matuqar mamakin ganin motocin police ɗin a kofar gidan su, da sauri suka karasa wurin su bayan sun gaisa Abba yake tambayar ko lafiya wa suke nema, nan wani baki me murtukakken fuska gabjeje da shi yace, "Aslam muke nema", abba yace "lafiya dai ko" mutumin Wanda da alama shine shugaban tawagar ya kara cewa"zamu tafi dashi office idan kana son jin Karin bayani zaka iya bin bayan mu" Abba yace" Aslam baya gidan nan banan bane gidan shi,"daddy ne ya katse Abba da cewa yana "cikin gidan ku shiga ku taho dashi,"

Abban da sauri ya maida kallon shi ga daddy da yayi wannan maganar,

Daddy ne ya musu jagora har zuwa part ɗin su Aslam ɗin, sauran mutanen gidan basu San meke faruwa ba , kasancewar da sassafe ne kowa na daki wasu ma sun koma baccin bayan asubahi,

Yana zaune akan sallaya yana mika kukan shi ga mahaliccin shi yaji bugun kofa, ba kakkautawa, gaban shi ne yayi wani irin faduwa haka kawai yaji hankalin shi bai kwanta da wannan bugun kofa ba, amma haka ya daure ya bude kofar,

Mamakine ya kusa kashe shi ganin mutane har biyu sanye da kakin police abakin kofar dakin shi,

Kallon su yayi yace "malamai lfy , " daya daga cikin su yace"u ar under arrest, munzo mu tafi dakai office ne" yace "saboda me zaku tafi dani office me nayi, zakuzo har cikin gidan ubana kuce zaku tafi dani,"

Dayan ne yanzu ya amsa da"Mallam da Allah kar ka wahalar damu , kazo muje office duk abinda kake son sani kaji daga baya acan"
Shiru ya danyi na some seconds kafin yace"muje to zan biyo ku a baya da mota ta, " kin amincewa sukayi, kasancewar suma ogan yadan san musu wani Abu cikin abin da ya samu akan case din, kuma ya gaya musu no mutunci,

Hannunshi suka kama zasu saka mishi handcuffs yaqi amincewa , dole yana ji yana gani ya shiga motar police suka tafi dashi,

suna fita Abba ya kalli Daddy yace " me yasa ka yi haka yaya," Daddy yayi murmushi yace" idan nace musu baya nan baza su yadda ba , sai sun shiga sun dudduba, haka kawai su tasar ma iyalan mu da hankali suna cikin hutawa ba laifin fari bana baki, gara dai su tafi dashi cikin salama, ai tsunstun daya ja ruwa shi ruwa kan duka" Abba yace "to yanzu zamubi bayan su ne" Daddy yace"A'a nifa baza ni ba idan kai zaka bisu bismillah"

Abba yace "aikam banga ta zama ba bari na shirya nabi bayansu" dage kafadu daddy yayi alarmar, I don't care ya nufi part dinshi ,shima Abba part dinshi ya nufa don ya shirya yabi bayan su zuwa station,

Suna isa station ba'a bashi daman yin wani magana ba aka shiga da shi cell , ogon su ya bada umarnin a mishi dukan tsiya, Aslam na tambayar me yayi ba Wanda ya saurare shi, mutum biyu ne jibga jibga suka shiga dukan shi da kulake baji ba gani,

Ko kafin Abba ya karaso sun hada mishi jini da majina, Abba daya nemi jin ba'asi folder case din Aslam ɗin da ka bude aka dauko mishi, mahaifin matar shi ya shigar da kara akan dukan tsiyan da yama ƴar shi da karamin ciki Wanda hakan yayi sanadiyyar zubewan cikin, yanzu haka tana asibiti a kwance rai a hannun Allah,

Dukar da kai Abba yayi ya shiga maimata innalillahi wainnailaihi rajiun, dagowa yayi idanun shi sun rine, yace "yanzu oga meye abinyi," oga yace" abinyi shine zamu rike shi anan gurin mu har sai yarinyar ta samu lafiya, sannan mu mikashi kotu a yanke hukunci daidai da laifinsa,"

Abba yace "ko za'a iya bamu bellin shi kafin, komai ya daidaita" ba,
Oga yace "ba zaiyuwu ba"

Abba zai ci gaba da magana oga ya dakatar dashi ta hanya daga mai hannu yace "na gama magana, bana sonjin wani magana data shafi beli"

Abba ganin yadda ya daure fuska alamar yana so yaci mai mutunci, yasa dole yayi shiru da bakin shi , ya mike ya fice daga station din, jiki a sanyaye.

A gida kam ba Wanda yasan abinda ke faruwa, don daddy dama abin ko ajikin shi, bai damu ba, balle har yaje gayawa mummy, Abba kuma kin gayawa mami yayi don karta shiga damuwa,

Koda ya sanar ma daddy abinda oga ya fad'a mai , na cewa Aslam ya daki matar ya zubar mata da ciki. Mahaifinta, ya shigar da kara gurin yan sanda , da yadda sukayi na batun beli, daddy cewa yayi Allah ya kyauta,

Wasa wasa kwanan Aslam uku a station kullum kuma sai am mishi dukan tsiya safe da rana da yamma, Abba kam kullum cikin zarya yake amma oga yaki sauraren shi,

Alhaji baba Abba ya sama da maganar , shima dai Allah ya kyauta kawai yace,

Mami kam ta shiga zullumin don tun ranar da Aslam yazo mata da batun zee ta zubar da ciki take ta saka ran kara ganin shi amma shiru kakeji,ta zuba ido shiru ta kirashi a waya shiru,

Bayan kwana uku zee ta warke ta samu karfin jiki sosai , nan Dr ya sallameta,

Dad ɗaukanta yayi sukaje station din da aka rufe Aslam sawa yayi aka fito mai dashi,

Innalillahi karkuso kuga Aslam yanda ya koma abin tausayi, duk jikin shi yayi shedan duka wani gurin ma ya fashe, fuskar shi kam ya kumbura sintim kamar ba Aslam ba kwata kwata ya fice daga haiyacinsa , taso shi gaba yan sandan sukayi, har gaban dad, kallon banza ya watsa mai kafin yace," Aslam kake kowa,kayi babban kuskure da daga hannu ka dukarmin yarinya, koni Dana haifeta ban taba dukanta ba sai kai, don kawai ka mata asiri ka aure ta kuma sai ka hada da duka, so yau asirinka ya karye, daga yau babu kai babu zainab, ko a hanya karka kuskura ka kara nuna ka santa, " kallon oga yayi dake ta washe baki kamar gonar auduga yace a "sake shi haka",

Kallon zee yayi data miqe tsaye ta dafe girjinta , tun fitowar Aslam ganin yadda ya koma yasa tuni hawaye ya fara bin kuma tunta, tana son Aslam sonda ko iyayenta bata yi musu irinshi, koda take cewa ko shine autar maza ta barshi , fad'a kawai takeyi, don ita kanta tasan karya takeyi, kawai bacin Raine ya saka fadar haka ,

Ganin yanda take kuka, yasa dad mikewa a fusace ya figi hannunta suka bar cikin station, daga nan kuma airport suka nufa, basu zame ko inba sai Malaysia,

Aslam kam rigar shi wani kurtun dan sanda ya miko mai ya karba ya saka wasu takaddu ya sassaka hannu kafin suka sallameshi daga station din..............

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fisabilillahi🙏.

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan page din ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 69 & 70

Keke napep ya hau zuwa London road, babu ko sisi a aljihun shi, don ƙananan polisawan nan tass suka yashe shi, jiran shi me keken yayi ya ƙwanƙwas get din gidan me gadi ne ya taso ya buɗe yana tambayar waye,sauran maganan ne ya maƙale ganin Aslam tsaye cikin wani mawuyacin yanayi, da'ker Aslam ya buɗe baki yace, " ka sallami mai keken nan, "
"To yallabai to yallabai" haka me gadi ya dinga maimaitawa jiki na rawa.

Bayan me gadi ya biya kuɗin napep dawowa yayi yana ta jerawa Aslam sannu tare da tambayar shi meya same shi haka, Aslam ya bashi Amsa da cewa"tsautsayi na samu amma da sauki sosai alhamdulillahi"
bayan haka bai ƙara cewa komai ba ya wuce cikin gida.
Chapter 34 · 0% Book details