Sashe 92
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Sauke numfashi Dr bala yayi yace "hakika kinga rayuwa kema,amma kinsan duk waɗanda suka jefa ki cikin wannan walagigin rayuwar." Girgiza kai tayi alamar A'a yace "mutum biyu ne, na daya sune iyayenki wadanda suka haifeki, na biyu kuma wacce itace ummul kaba'isin din faruwar komai, wacce kika dauki yarda da soyayyar gaskiya kika daura mata ita kuma taci amanar ki, ba kowa bafe face ƙawar ki beebaloo." Zaro ido waje zee tayi tare da cewa "meye haɗin beebaloo da faruwar wadannan abubuwa." Murmushin takaici Dr bala yayi, kafin kuma ya shiga zaiyane ma zee komai da manufar beebaloo akan zigata da tayi ta zubar da ciki, da kuma kiran Aslam da tayi ta gaya mishi.
Tun kan ya karkare labarin hankalin zee yayi matuƙar tashi, take hawaye suka fara ambaliya a fuskarta, jikin ta ya kara yin sanyi, ta kara yadda Allah abin tsoro ne, duniya abin tsoro ne mutanen cikin tama abin tsoro ne, ta karajin lamarin mutane ya kara fice mata a kai, lallai beebaloo taci amanar yarda taci amanar aminta taci amanar soyayya, da zuciya daya ta riƙe ta, ta dauki ragamar komai na rayuwar ta ta bata duka wani sirri nata ta fallasa mata, bayan Aslam daya kasance miji a gareta a Nigeria beebaloo ce mutum ta biyu da zee ke tsananin kewa da begen gani, lallai ta yarda mutum mugun ice.
Idanunta da suka rine sukayi jajur ta sauke a kan Dr zuciyar ta a dake ta jeho mai tambayar, "dan Allah Dr bala ka fada min gaskiyar abinda ka sani, shin beebaloo tayi nasarar auran min miji bayan barowata 9ja kokuma Allah bai bata nasara ba."
Girgiza kai yayi yace "banajin ta samu narasa akan mijin ki domin kuwa naji daga majiya mai karfi cewa......
~BEEBALOO~
Bayan ta sauke zee a gida ranar da ta kaita asibitin Dr bala aka mata alluran zubar da ciki, da wani irin farin ciki da anushuwa tabar gidan dan ta tabbatar boom ɗin da ta dana zaiyi gagarumar tashi, duk abinda ya faru tsananin zee da Aslam tana da labari komai dan renting ɗin waɗanda zasu dinga bibiyar mata komai tayi na musamman, tun daga kan dukan da Aslam yama zee har zuwa kan barin zee naija tana da labarin komai.
Ranar da zee tabar naije ranar ta fara bibiyar Aslam, ta takura rayuwar shi da kiraye kiraye a waya da message, tun yana dauka har ya gane number ta ya daina dauka, daya gaji ya daga kiran ya mata wankin babban bargo, sannan yayi blocked dinta, hankalinta ba karamin tashi yayi ba hakika tana kaunar Aslam burinta bai wuce a ce yau ta mallake shi a matsayin miji ba, domin ta cika burin ta na auren kyakkyawan namiji mai kuɗi dan babban gida, Wanda kowa yasan wannan dalilin ya hanata zama gidajen aurarrakin ta na baya.
Batayi kasa a gwuiwa ba ta sake siyan wani layin taci gaba da bibiyar Aslam, tana ci gaba da yada manufar ta bata fasa ba, kwatsam ta zo ta daina samun shi kwata kwata a waya duk wani hanyar sadar wa da take bibiyar shi ta yanke, a lokaci guda, (idan Baku manta ba lokacin da ake tsaka da tirka tirkan nan kenan, lokacin da ya kwanta rashin lafiya kafin bikin shi da Asmah).
Hankalin beebaloo yayi matukar tashi fa kasa samun Aslam da tayi kwana biyu, ita fa ta lashi takobin ko ta halin ƙaƙa saita mallaki Aslam, domin wahala da faɗi tashin ta bazai tashi a banza ba, ta shiga damuwa a cikin kwanakin nan taje gidan shi yafi sau a kirga tana samun gidan garƙame da kwado, har ciwo tayi a cikin yan kwanakin nan.
Tana cikin wannan halin Allah ya haɗata da wata tsohuwar kawar ta tun na yarinta, wata rana taje asibiti ganin likita, nan kawar ta mai suna hajo ta tambayeta meke damunta, bata boyema hajo komai ba ta gaya, murmushi hajo tayi tace"kawata kwantar da hankalinki in-sha Allah kakar ki ta yanke saƙa nizan taimaka miki ki mallaki koda uban Aslam ne bama Aslam ba, ki tanadi kudi masu dan kauri ki shirya jibi zan raka ki gurin mallan kamsusi, aikin shi kamar yankan wuƴa yake."cikin tsananin farin ciki beebaloo ta shiga jerowa hajo godiya gida ta koma ta shiga buga buga ta saida wance ta saida wannan ta samu ta haɗa kudin ta masu kauri, bayan kwana biyu suka dauki hanyar gurin malam kamsusi ko sallama da gida beebaloo batayi ba.
Tafiya sukayi sosai a mota kafin su sauka a bakin hanya, suka tari me kabu kabu Wanda zai shigar dasu cikin kauyen, tun a gurin cinikin kudin me kabu kabu beebaloo ta sha jinin jikinta, dan cewa sukayi su bada dubu uku uku, ga mamakin ta gani tayi hajo tace muje "ba tare da wani damuwa ba" ita dai bata tanka ba amma a zuciyar ta tace "dubu uku sai kace mutum zaije kano daga minna" haka ta dai ta hau mashin suka dauki hanya, tun ana tafiya ta marmari har aka gaji, har tafiyar ta koma ta fitar hankali, tuni hantar cikin beebaloo ya fara kaɗawa dan ta sadakar hajo ta siyar da ita, take ta fara jero kalmar shahada tun tanayi a zuciya har ta fara yi a baiya ne, babban tashi hankalinta yadda hanyar kwata kwata bashi da kyau, sai shiga ramuka suke yi suna fita, wani tudun kuwa idan mashin ya hau daga ita har driven mashin din sai sunyi sama duwawunsu ya rabu dakan sit din mashin din sannan su dawo su zauna daɓar, tuni beebaloo ta fara kuka hawaye uku uku, basu suna sauka akan kabu kabu ba saida sukayi tafiyar awa biyar kwarara.
A wani dan tsukukun kauye suka sauka, a tunanin beebaloo sun ido ne, amma sai taji hajo na cewa "a nan zamu kwana beebaloo gobe da asuba ba sai mu daura da kafa mu karasa aslin kauyen da mallam kamsusi yake, da kafa zamu karasa domin daga nan ne mashin ke iya tsaya wa a gaba babu hanyar mashin."
A wargaje beebaloo ta zaro idanunta da suka kankance sukayi jajur tsabar azaba tace "hajo kina nufin dama ba nan bane asalin inda muka zo." Hajo tace "eh ba nan bane karki damu kawata munyi rabi, ni na saba zuwa ,kema dan yaune zuwanki na farko yasa kike ganin wahalar shi.
(Hmmm akace sa kai yafi bauta kuji hajo wai ta saba zuwa)
A nan dan tsukukun kauyen suka kwana, inda suka dunga bin gida gida daker suka samu wacce ta amshe su ta basu dakin awaki su kwana a ciki, ba tare da damuwa ba hajo ta shiga ta nemi guru ta zauna, babu alamar damuwa a tare da ita da alama dai ta shiryama faruwan hakan.
A darare bebalo ta samu guri itama ta rakube, a haka gari ya waye musu, hajo tadan gyangyada yayin da beebaloo idanunta Kamas, yadda taga dare haka taga rana, duk wannan azabar wahalan da suke sha,idan ta tuna at the end zata mallaki aslan ɗinta sai ta saki murmushin farin ciki.
Da asuban fari suka dauki hanya suka fara shatatawa da ƙafa babu batun sauke farali bare salati, tun suna tafiya suna dan taɓa fira har kowa yayi gum sai Jan kafa sukeyi shakataf shakataf, jefi jefi sunan hadu da mutane a hanya wasu na shiga kauyen wasu na fitowa, a haka suka hadu da wata a gwai suka sayi fura da nono babu ko suga suka shiga kwankwaɗa, basu suka shiga asalin kauyen da mallam kamsusi yake ba saida rana ta take, sun tarar da layi sosai, amma basu damu ba, hankalin beebaloo ya kwanta ganin ta gata ga bukkar mallam kamsusi, inda take da tabbacin zai share mata kukan ta gani takeyi kamar ta auri Aslam ta gama.......
Shin mai ya faru ne burin beebaloo na auren Aslam bai cika ba har yau, duk da kuwa zuwa wajen mallam kamsusi da tayi, ku biyo diyar nalado danjin yadda z
aka kaya.
Oum Ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wanna book din ga suka wacce ta rasab mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}
Page 118
Saidai sukayi zaman fiyye da awa uku sannan layi yazo Kansu, zuciyar beebaloo wasai yau tazo inda take da tabbacin za'a share mata kukan ta, tare suka shiga cikin bukkar mallam ɗin ita da hajo, guri ya nuna musu suka zauna kan shimfiɗar buzu, so ɗaya beebaloo ta iya kallon fuskar mallam kamsusi da sauri ta dauke kai gabanta na faɗuwa, duk inda muni yake Allah ya tattarawa mutumin nan, baƙi ƙirin dashi, gashi dan cukuli kamar a kife da kwando sai katon kai, yasha wani uban rawani ƙato a kanshi, gaban shi kuma kasa ne mai kyau fari tas , hannun shi rike da wani dogon carbi irin mai guda dubu ɗinan yana ja sai wani musmus yake yi da baki.
Tun shigowar su ya kafe mici micin idanunshi akan beebaloo, yana kare mata kallo daga Sama har kasa, yana sauraren radar da aljani dan misra ke mai a kunne game da ita, lallai ta tafi da nutsuwa shi, gani ɗaya yaji ranshi ya biya kuma bawai na lokaci daya ba inso samu ne yana bukatar ya aureta, ido ya zura mata kamar mai bukatar hango wani abu a jikinta yayin da ita kuma ta kasa kara dagowa ta kalle shi.