← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 107 OF 126

Sashe 107

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Ko ina yayi kura a part ɗin tun daga kan falo kitchen dakunan barci toilets da sauran su, gashi kuma yamma yayi, hakan yasa cikin sauri ta kau da duk wani tunani da damuwan ta gefe, cike da himma ta fara gyara falukan ta cikin kankanin lokaci ta ƙalƙale shi fess nan kuma ta koma kitchen shima haka tamai ta goge na goge wa ta wanke na wanke wa, dakin barcin ta ta shiga yana nan yadda ta barshi ga kayayyakin ta nan ba'a kawar da komai ba, toilet ta shiga ta fara wanke wa sannan ta dawo dakin shima, ko kafin ta gama duk wadannan abubuwan magrib ta gaba to alwala ta daura, tayi sallah, sannan ta duba store kayan abincin ta data bari na nan yadda ta barsu komai akwai amma bata jin zata iya cin komai a cikin suu, ga kuma little dake ta dan mata kukan rigima alamar yana jin yunwa, hijjab ta zura tare da dauko kudi ta nufi bakin get, mai gadi na ganin ta cike da mamakin ya shiga gaishe ta, rabon shi da ita tun ranar da ya kira hajiya makofciyar su, suka dauke ta rai a hannun Allah zuwa Asibiti,tun daga ranar kuma bai gani ko jin labarin ta ba, yau kuma koda yaga Alhaji babba ya sauke mace da yaronta ta shiga ciki bai taba tunanin ita bace, yadda ta amsa mishi a mutum ce ba kamar a baya ba da wani bin ma sai taga dama zata daga mishi hannu shi karan kanshi abin ya bashi mamaki, cikin girmamawa da dan jin nauyi ta gabatar mai da bukatar ta nasan ya siyo mata ruwan gora saboda sha, taliya idomie da kayan shayi sai mai dasu magi, da dai sauran abin da zata bukata nan kusa irin su sabulu da amo sannan ya biyar ya mata takeaway a safara foods, ba tare da damuwa ba kuwa ya amsa da to ta kawo ba damuwa, kudi mai yawa ta bashi wanda yafi karfin abin da ta bukata tace harda na napep amma dan Allah yayi sauri saboda yaro. Sai lokacin ya kalli yaron, zaro idanu yayi cike da al'ajabi magana fal bakin shi amma ba daman yi, haka ya tafi aiken yana tafe yana sambatu, to abin ne da daure kai, shidai yasan ance ciki ne a jikin ta a ranar da suka kaita asibiti kuma ya ɓare, yanxu kuma ya ganta da yaro mai kama sak da mai gidan.

~Asmah~

Bacci tayi sosai dan sai bayan la'asar ta farka, mummy kam koda akayi azahar bata tashe ta ba, ta barta ne tayi barcin sosai ko zata samu natsuwar zuciya, sai dai tana yi tana leka ta lokaci lokaci, ganin anyi la'asar bata farka ba yasa ta nufi dakin da nufin ta tashe ta, tayi sallolin dake kanta kuma taci abinci. Tana shiga dakin ta tarad da ita a zaune bakin bed ta dafe kanta alamar tashin ta kenan, itama jin motsin an turo kofar yasa ta dago kai mummy ce, kamar yadda dama ta zata, murmushi mummy ta sakar mata, tare da nufar ta ta taba jikin ta don taji koya zazzabin ya sauka, salam kuwa babu alamar zazzabin, alhmdllh ta furta tare da cewa "sannu Asma'u kin tashi ya karfin jikin kuma." Gyada kai kawai tayi alamar da sauki don ji tayi bakin ta ya mata nauyi, mummy tace "to sannu kinji ki daure ki tashi ki lallaɓa kiyi wanka da ruwan dumi zaki ji daɗi sai kizo kiyi sallolin dake kanki kinji." Nan ma sake gyada kai tayi, tana yunkurin tashi, taimaka mata mummy tayi ta mike a hankali ta nufi toilet din wanka tayi da ruwa dumi kamar yadda mummy ta umarce ta, ta kuwa ji daɗin shi sosai, alwala ta dauro ta fito daure da towel, samu tayi mummy ta ajiye mata abaya mai kyau sabo fil da hijab gashi kuma ta shimfida mata pray mat, ko mai bata shafa ba ta saka rigar bayan ta maida kayan ta na ciki data cire tunda bata da wani a gidan, tana cikin sallah mummy ta shigo dauke da tray da kuloli a kai, ajiyewa tayi a gefe, ta zauna tana jiran ta ta idar.

A nutse ta gabatar da sallan ta, bayan ta gama kuwa daga hannun tayi ta shiga kwararo addu'o'i sosai akan lamarin dake tunkaro ta, da kuma rokan allah ya sassauta mata kishi ya bata hakuri da juriyar jure abin da zata fuskan ta a gaba.Tun tana yi a ciki har bata San sanda ta fara yi a bayyane ba, karshe ta fashe da kuka, duk mummy najin ta tana kuma amsawa da amin, a tare suka shafa addu'ar da mummy, tasowa tayi daga kan pray mat din ta iso gaban mummy dake zaune a bakin bed, daura kanta tayi akan cinyar mummy ba tare da tace komai ba, hannu mummy ta daura akan ta, ta shiga shafa mata kai a hankali, sauke ajiyar zuciya ta shiga yi, sun dauki tsawon minti 10 a haka, kafin mummy cikin rarrashi tace "Asma'u ki kwantar da hankalin ki, na fahimci abin da kike tsoro, kar ki saka ma kanki damuwa Aslam yana sonki bazai taba wulakan ta ki ba, idan ma yace zaiyi ninan zan tsaya miki sai inda karfina ya kare, ki kwantar da hankalin ki kinji, in sha Allah kema zaki samu naki ɗan da yardan ubangiji ki cire tsoran komai a ranki kinji." Gyada kai tayi alamar to! Mummy ci gaba tayi da kwantar mata da hankali tana gaya mata maganganun masu sanyi ma zuciya natsuwa. Daga yadda ta nutsu tayi shiru ta daina sauke ajiyar zuciyar da take yi mummy ta fahimci zancen ta na shiga ta sosai, hakan yasa cikin dabara ta shiga kowar da ita dabaru zama da mutanen cikin hikima yadda baza ta cuci kowa ba kuna baza a cuce ta. Kwarai ta samu nutsuwar zuciya sosai daga kalaman mummy, ta samu karfin gwuiwar da ta rasa a ɗazu, zafin da zuciyar ta ke mata da ragu sosai daga kashi talatin cikin dari. A baki mummy ta bata abinci don tasan idan tace ta ci ba ci zata yi ba, duk da haka bata wani ci ba. Bayan sun gama still mummy bata gaji ba ci gaba tayi da koya mata wasu abubuwan da zasu taimake ta a zamantakewar ta na yau da kullum.

A massallacin kofar gidan yayi sallan isha'i, ana kuwa idar wa bai ba bata lokaci ba ya shigo cikin gidan a kagare yake daya sanya ta a idanun shi, ya damu matuka da son sanin halin da take ciki, haka kawai zuciyar shi ke bashi tana cen tana kuka, duk da yasan mummy baza ta bar ta tata kuka ba.
Chapter 107 · 0% Book details