← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 126

Sashe 49

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Kallon Aslam yayi yace "bari na sauke a gida tunda dare yayi gobe bello ya kawo maka motar da safe", da sauri yace "A'a Abba ba damuwa muje kawai na dauke," Abba yace"kaidai bari tunda gashi har mun kawo gidan goben bello ya kawo maka motar, kaje gida kabar min daughter ita kadai" ba yacce Aslam ya iya dole haka yayi shiru, ya kudiri aniyar Abba na ajiye shi a bakin get inya bada baya shi kuma zai fice abinshi, ga mamakin shi gani yayi Abba yana danna horn a bakin get, mai gadi kuwa cikin azama ya wangale get, Abba ya kutsa motar shi ciki.

Yana parking ya fito ya bude bayan motar ya dauko manyan ledodi guda biyu, har lokacin Aslam na zaune jiki a mace baida niyyar fitowa daga motar, Abba yace "fito mana son kai nake jira fah" jiki a sanyaye ya balle marfin motar ya fito, mika mishi ledar yayi tare da cewa "oya ga tsarabar daughter akai mata saida safe" karba yayi yana sakin murmushin yake yace"to Abba ta gode saida safe" jira ya danyi irin Abba ya shigayi motar nan shi kuma ya samu ya gudu amma ga mamakinsa gani yayi Abba ya jingina da jikin motar ya nuna mai hanyar plat din da ke gabanshi,.

Sai lokacin Aslam ya fara hasashan wani abu to kodai Abba ya gano shine, wani busasshen miyau ya hadiye mukut, tare da kama hanyar nufar kofar plat din, har ya kai bakin kofa ya tsaya ya waigo still idanunta Abba nanan akan shi, dole yayi shahada ya murda handle din kofar ga mamakin sa gani yayi kofar ya bude, a zuciyar shi yace lallai ma yarinyar nan haka take barin kofa a bude abinta, shigayi yayi da sallama a bakinsa kasa kasa...................

Ba editing🙏

Oum ummeetarh
07041130088

💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacceta rasa mahaifiya, Allah kajiqan iyayen mu}

Page 87 & 88

Tun daga ranar da aka kawota cikin gidan a matsayin amaryar mai gida, har yau da take cikin kwana na biyar bata saka angon a idanunta ba, hakan kuma ko kaɗan bai dameta ba, harkar gabanta takeyi hankalinta kwance, ita rashin zuwan nashi ma ya mata daidai dan bata buƙatar ganin fuskar shi a halin yanzu.

Yau data kama kwana na hudu tun safe data tashi baƙi takeyi, yan ganin zuwa ɗaki, basu suka sarara mata ba sai wurin magarib, gyara gidanta tayi dukda ba wani datti yayi ba ta kunna burner turaren wuta take ko ina ya ɗauki kamshi,bayan ta idar da sallah isha'i ta shiga kitchen ta dafa jellop din couscous, daidai cikin ta, kwashe wa tayi a kula ta ajiye,ɗakinta ta koma tayi wanka tana fitowa gaban mirror ta tsaya tayi shafe shafenta, tare da feshe jikinta da daddaɗan turarukanta, masu shengen ɗaɗin kamshi da tsadar gaske, wasu sleeping dress ta ciro sababbi fil, ruwan light pink ta sanya, dogon gashinta dake daure da ribbon ta warware, dan bata iya kulle shi in zata kwanta damunta yakeyi, cumb ta dauka ta kwantar dashi, take kuwa ya sakko har kusan tsaki yar kafaɗunta, dan man leɓe ta shafa kaɗan, sanna ta fito ta nufo kitchen ta dauki couscous dinta ta hada da kwalin exoctic, da ruwan gora ta dawa palo, tana ci tana kallon, kwana casa'in, a tashar areaw 24.

Koda ta gama cin abincin saida ta jira aka gama shirin sannan ta kwashi plate da cup ɗin da ta bata ta kai kitchen ta wanke su.

Dawowa falon tayi ta kwanta a 3 sitter ta kunna data, ta shiga WhatsApp tana dan chart a groups, wani program ake gabatarwa a wani group , mata saida ado, da take ciki, program ne akan yadda mata zasu kula da tsabtar jikinsu, shirin ya dauki hankalinta sosai, gaba daya ta tattara hankalinta da nutsuwarta ta mayar kan wayarta, domin kuwa abin karuwa ake gabatar wa.

Murda handle din kofar yayi a hankali ya buɗe ya shiga bakin shi ɗauke da sallama kasa kasa , yana shiga, wani daddaɗan kamshi hade da sanyin ac yamai salama , baisan sanda ya lumshe idanun shiba, jingina bayan shi yayi da jikin kofar bayan ya mayar ya kullu, har zuwa lokacin idanun shi a lumshe suke yana shakar daddaɗan kamshin dake tashi a falon.

Ganin ya shige yasa Abba dake tsaye jikin motar shi sakin murmushi tare da, komawa cikin motar yayi ya tayar ya shiga ya bar gidan, yana me rakasu da addu'a zaman lafiya da zuri'a ɗayyaba.

Ya kusa kwashe 10 minutes a haka kafin a hankali ya ware idanun shi a cikin falon yana bin ko' ina da kallo, idanunshi ne ya sauka akanta, gaba daya hankalinta yana kan handset dinta dake hannunta, ji yayi gaban shi ya bada rasss, da sauri ya lumshe idanun shi ya sake budewa still dai ita ya sake gani again, bai yarda ba ya dauka gizon data saba yi mai ne wasu lokutan yauma ta ke mai, kara saka hannu yayi ya murza idanun shi ya kara budewa, sai lokacin ya tabbatar ita ne ba gizo bane.

Karfin bugun zuciyar shi ne ya linku, jikinshi take ya fara wani irin tsuma,me hakan ke nufi, yanzu hakan na nufin itace amaryar da aka aura mai, itace dama zabin da alhaji baba ya mai na biyu, kokuwa dai Abba gidan kamal ya kawo shi, kokuwa dai mai kama da itace.

Wata zuciyar Ce tace Aslam ka nitsu karka ruɗa kanka, wannan gidan ka ne, kuma Abba da kanshi ya kawoka, kasan dai bazai kaika gidan kamal a matsayin naka ba ko? Tambayar zuciyar nashi ya kara yi, to ita kuma husnah mai takeyi a gidana, bayan tana matsayin matar kamal.

Amsa zuciyar shi ta bashi da cewa, tunda ka ganta a gidan ka , to tabass itace zabin da alhaji baba ya maka, tabass dama ta biyu Ce ka sake samu akanta.

Wayyo Allah dadi Aslam rasa ina zai tsoma ransa yayi dan farin ciki, har zuwa lokacin hankalinta nakan wayarta bata san da wanzuwar mutum a kanta ba.

Daidai lokacin aka gama program din da ake gabatarwa a group din, mikewa zaune tayi tana sakin murmushin ta mai kayatarwa, wayar ta ajiye tayi ɗaga hannayenta sama tana miƙa, still fuskar ta a washe dan program din ya fadakar, da ita kuma ya ilimtar da ita ta karu sosai da wasu abubuwan masu muhimmanci.

Sai lokacin ya kara tabbatar da ita ɗince ba mai kama da ita ba, da wani irin doki, azarbabi, shauƙi, ya dira a gabanta, shi kanshi da za'a tambayeshi baisan yadda akayi ya iso gabanta ba, shidai kawai yaji wani irin Abu na janshi gareta kamar magnet.

Ganin mutum a gabatan ta kamar daga sama yasa ta saki wani irin ƙara,kafin ta shiga furta a'uzubi kalmatillahi, ba karamin tsorata tayi ba, hakan yasa ta kasa tantance wanene, mutum ɗinne ma ko aljan.

Ganin haka yasa Aslam da shauƙi ke dibanshi ya tashi ya rungumota jikin shi, ya kamkame ta.

Luf kuwa tayi a faffaɗan kirjin shi, tana shakar kamshin daddaɗan turarenshi mai kwantar da hankali, idanunta a rintse sai sauke ajiyar zuciya takeyi, shi kuwa a hankali ya miƙa hannu ya shiga shafa bayanta, yana dan bubbugawa, alamar yana rarrashinta,ita dai batasan a ina take ba, dan gaba daya hankalinta baya jikin ta

Zuciyar shi kamar ta fito daga kirjin shi, tsabar azalzalan shi da takeyi, wai yau shine rungume da husnah a jikin shi, wayyo dadi kashe shi, ji yayi tunda yake a duniya bai taba riskar wani yanayi mai dadin da yakai Wanda ya riski kanshi a ciki yauba.

Saida suka kwashe minti biyar a haka kafin ta samu nutsuwa hankalinta ya dawo jikinta, jinta tayi dare dare a rungume jikin mutum, yana shafa bayanta, a hankali ta dago fuskarta daga kan kirjin shi, ta kai kallonta a fuskarshi, zaro manyan idanunta waje tayi, kafin ta zabura ta mai wani irin kyakkyawan hankaɗa, daya zo mishi bagatatan, ba shiri ya saketa tare da hantsilawa da baya kamar zai fadi,Allah ya taimakeshi bai fadin ba, dan gaba daya jikin shi ba kwari.

Mikewa tayi a zafafe tana binshi da wani irin kallo, gashi nan shi ba harara ba amma mutum zai gwammace dama hararan shi akeyi akan wannan irin kallo.

Duk da tariga tasan Aslam shine kaddaran ta ,wannan karon ma shine mijin da aka aura mata a karo na biyu sabanin zaɓin zuciyar ta kamal, ta kuma yi kukan hakan kamar hawayenta zasu kare, tayi baki ckin hakan kamar ta hadiyi zuciya ta mutu ta huta, tayi zazzafan zazzabi akan hakan kamar bazata kara lahiya ba, amma daga karshe ta fawwalawa Allah komai ta amshi kaddaranta da hannu bibbiyu.

Amma yau ganin shi a gabanta har yana wani sakata acikin jikin shi yasa taji gaba daya mikin da tayi kokarin dannewa kwanaki biyu da suka wuce ya dawo sabo dal, ji tayi kamar a lokacin, ake sanar da ita , Aslam ne mijinta ba kamal ba, ta tsani Aslam tun bata San kanta ba, bata sonshi bata kaunar shi daidai da kwayar zarra a zuciyar ta.

Ganin tana jifan shi da wani irin kallo yaji gaba daya jikin shi yayi sanyin, bazai iya juran irin wannan kallon daga gareta ba, zuciyar shi tarwatsewa zatayi,a hankali ya shiga takawa zuwa gabanta.

Ganin yana nufota yasa ta juya da wani irin sauri sauri gudu gudu, ta haura upstairs ta shige dakinta ta banko kofa da karfi.

Ganin haka yasa ya zube guwowin shi a kasa, cike da tsantsar farin ciki, rasa ma me zaiyi,yayi ji yake kamar ya daddage ya kurma ihu tsabar farin ciki, yesssssss ya furta da karfi yana dunkule hannayenshi kamar zai kai naushi, na sameta na mallaketa Allah na gode maka, goshin shi yakai kasa yayi sujud, ya shiga rerowa ubangiji kirari da godiya, yana dagowa kuwa, ya fashe da wani irin dariya kamar sabon kamu, take duk wani kulle mai nauyi da yakeji a zuciyar shi ya kau, komawa yayi da baya ya kwanta rigingine akan titles yayi filo da hannunshi yana kallon pop din falon yana sakin murmushi.
Chapter 49 · 0% Book details