← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 126

Sashe 116

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A fusace Dad ya bar gidan Aslam da nufin ya nufi police headquarter ya debo ƴan sanda ya biya manyan su kudi dan suzo suci mutumin Aslam sumai dukan tsiya sannu su tafi dashi su kulle shi kuma ya dauki yar shi ya tafi da ita, yana tafe yana sambatu yana zage zage kamar wani taɓɓaɓe gaba daya hankalin shi baya jikin shi burin shi kawai ya ganshi a police station, yazo tsalleke titin domin ya koma hannu da zai samu taxi cikin rashin sani wani tsohon Sharon ya shararo da gudu birke ya tsinke mai tun daga nesa yake ta danna ma Dad horn amma ina baiji ba hankalin shi baya jikin shi idanunshi sun rufe kunnuwan shi sun ɗoɗe tsabar bala'in dake cin zuciyar, aikuwa cikin hukuncin ubangiji mai Sharon ɗinnan yayi sama da Dad kuma ganin ba kowa abin ka da unguwan yan gayu yasa mai Sharon dinnan fece wa ya bar Dad nan kwance rai a hannun Allah, me gadin dake farkon Layin ne ya fito da nufin yin wani uzirin sai ganin mutum yayi kwance cikin jini shine fa yayi kururuwa mutane suka dan fiffito yawancin su ma masu gadin gidajen unguwan ne, koda suka fiffito tsayawa suka yinyi cirko cirko ana shawara an rasa wa zai taimaka mai zuwa asibiti, suna cikin wannan tsayuwar ne motar Aslam tazo ta wuce su da mugun gudu, kasancewar cikin tashin hankali yake yasa bai kula da abin da ke faruwa ba, wani he ya bada shawara a shiga gidajen dake kusa a gaya musu suzo su duba ko dan uwan su ne moto ya buge dan ga dukkan alamu daga cikin wannan unguwar ya fito, da wannan shawaran suka fara bi gidanjen da ke kusa cikin haka ne suka zo gidan Aslam, me gadi dake nan duk cikin shi ya duri ruwa ya kasa zaune ya kasa tsaye don duk abin da ke faruwa akan idanun shi ne abin da yafi daga mai hankalin shine yadda yaga Aslam ya figi mota a tsiya ce , ya tarbi mutum biyu da suka yi sallama a kofar gidan , jin abin da ke tafe dasu kuwa baiyi kasa a gwuiwa ba yace suje ya gani duk da ko kusa bai kawo tunanin Dad bane yama fi ba cewa to ko Aslam ne ya buge mutumin tunda yaga ba cikin hayyacin shi ya figi motar ba. Ko da suka je kawai sai yaga mutum da ya fita a gidan su mintuna ƙalilin da suka wuce mutumin da ya mare shi yanzu yanzu ba tare da ya mishi komai ba, "Allahu Akbar." ya furta lallai dan Adam ba'a bakin komai yake ba yanzu wannan bawan Allah idan da yasan zai shiga cikin wannan mawuayacin halin nan da yan mintuna me zai kai shi aikata abin daya gama aika ta wa yanzu yanzu. Zuciyar musulumci take yaji tausayin Dad ya kama shi, dan kuwa duk wani mai imana idan yaga Dad dole ya tausaya mishi bai yi kasa a gwuiwa ba wurin cewa bai san shi b, amma ya bada shawaran a taro napep akai shi asibiti in yaso su likitocin saji dashi, take fa yawa suka amince da zance, ya samo me napep akayi general hospital da Dad kafafuwa na lilo alama

Likitoci sun sha matukar fama sosai kafin su samu su tsaida jinin daya barke mata da'ker suka ceto rayuwar ta, Aslam da Asmah kam sunan nan a kofar emergency room din Asmah sai kuka take yi Aslam yayi rarrashi har ya gaji ya kyale ta, shi karan kanshi karfin hali kawai yake yi, dan ya kasa zaune ya kasa tsaye, sai safa da marwa yake yi, lokacin da daya daga cikin likitocin dake duƙufe akan zee ya fito har rice rige sukeyi da Asmah wajen tambayar shi halin da take ciki, be basu amsa anan ba sai cewa da yayi su biyo shi office, bayan sun zauna file din ta ya bude ya shiga dan rubuce rubuce, Asmah kam ta kosa taji wani hali zee ke ciki hakan yasa tace "Dr pls wani hali take cike meya samu yar uwata." kallon su yayi tare da gyara zaman siririn farin glass din dake idanun shi yace "patient din da kuka kawo mana wato zainab Abdus-salam, ta samu miscarriage sakamokon wani tashin hankali da firgici data shiga na lokaci daya." Kamar saukar aradu haka Aslam yaji saukar maganar Dr a zuciyar shi Asmah kam tuni ta rushe da wani irin kuka kwace ce mata akayi zee din ta rasu, Aslam kam innalillahi wainnailaihi rajiun ya shiga furtawa a zuciyar shi, Dr ne y shiga rarrashin ta yana kwantar mata da hankali, dan Aslam bashi da karfin halin iya rarrashin ta a halin da yake ciki, ji yayi zuciyar ta kara daukar zafi,rintse idanu yayi yana jin tsanar Dad na kara baibaiye lungu da sako na zuciya shi, alkawari ya dauka tare da lasar takobin wannan karon bazai bari mahaifin zee ya shashi silla ba shari'a zai yi dashi bakin rai bakin fama daga nan har kotun koli na duniya sai anbi mishi hakkin shi akan Dad koda duk abin da ya mallaka zasu kare, jajayen idanu shi bude akan Dr cikin murya mai dauke da tsananin bacin rai yace "Dr wani hali matata take." Shi karan kanshi Dr abin ya bashi mamaki amma ya dauka duk bakin cikin rasa cikin ne yasa yake mai magana a haka, cikin muryar rarrashi Dr yace " matar ka tana lafiya munyi duk abin da ya kama ta muyi, harta wankin ciki duka munyi mata, yanzu haka barci take yi allura muka mata nan da awa 4 zata farka, ku kwantar da hankalin ku, babu wani wani matsala zata farka lafiya insha Allah." Rubutu ya ɗanyi a jikin wani dan paper ya mika wa Aslam gashi wannan magunguna ne zaka siyo mata na jini sunfi yawa aciki wanda zata din ga sha ba sai mun mata Karin jini ba idan tasha wadannan magungunan amsa Aslam yayi suka yi ma Dr godiya sannan suka fito Asmah ta shiga dakin da aka kwantar da zee shi kuma ya tafi pharmacy dan siyo magunguna.

Bayan ya dawo ya samu Asmah zaune a kan kujera hannunta cikin na zee dake ta sharar barci, ajiyar zuciya ya sauke ganin ta dawo daga suman da tayi yanzu barci take sai lokacin tunanin kiran su mummy ya fado mai, take kuwa ya lalubi waya ya kira Mami, kan kace kwabo asibiti ya cika da yan uwa, sai bayan isha'e zee ta farka kuma alhmdllh jikin da sauki sai dai Dr yace bazai sallame ta ba sai zuwa gobe, Mami da Asmah ne suka kwana a Asibiti, shi kuma Aslam ya tafi gida a gurin mai gadi ya samu little har ma yayi barci abin shi cikin net a kan dan karamin gadon dake dakin mai gadi, me gadi kamar ya gaya mai halin da dad ke ciki sai kuma kawai ya share,

A cen general hospital kuwa bayan sun kai Dad asibiti, cikin gaggawa a kayi cikin emergency dashi aka bashi gado,wadan da suka kawo shi wucewa suka yi bayan sun sanar wa likitocin cewa tsintar shi suka yi yayi accident a bakin hanya da alama mota ce ta buge shi kuma mai motar ya gudu.jin haka yasa akayi banza dashi tun da babu wanda zai tsaya mishi, sai bayan isha'e daker dai aka samu wani likita mai dan tausayi ya kula shi, jikin shi aka duba cikin sa'a aka samu wayar shi, a kulle wayar take hakan yasa aka cire daya daga cikin sim uku dake wayar aka saka a wani wayar take lambobi guda uku suka bayyana. Daughter, wife, Brother, ganin, haka yasa suka San duk wadannan makusantan shi ne, wani je ya bada shawaran a kira Brother saboda shi namiji ne zaifi matan saurin fahimtar lamari, Alhaji Abdur-rahman na zaune a falon shi yana hutawa shida matar shi kira ya shigo wayar shi, sunan daya gani ya matukar bashi mamaki kwarai sanin irin bakin zuciya na kanin nashi yasan sarai a yadda suka yi rabuwan baran baran karya ne ya neme shi nan kusa sai dai idan shine ya gaji ya neme shi, ajiye mamakin shi a gefe yayi ya daga wayar, maimakon ya tsinkayi muryar ƙanin nashi kamar yadda ya sakankance zai ji sai ya tsinkayi muryar wannan Dr , a gurguje ya sanar dashi abin da ke faruwa da me wannan lambar Alhaji Abdur-rahman yasha mamakin jin cewa a Nigeria ne ƙanin nashi yayi hatsari har ake neman shi a general hospital, jiki a sanyaye ya amsa wa Dr da cewa gashi nan zuwa nan da 20 minutes, suna ajiye wayar Mom ya kira yake tambayar ta ina Dad nan take ce mashi rabon da shi tun jiya, take ya sanar mata da abinda ke faruwa aiko dai hankali ba karamin tashi yayi ba nan ta fashe mashi da kuka a waya, daker ya dan rarrashe ta sama sama ya tashi ya kamo hanyar asibiti, sai da Alhaji Abdur-rahman ya iso ya bude ma Dad file yayi duk abin da ya kamata yayi sannan Dr din suka taba shi.
Chapter 116 · 0% Book details