Sashe 51
Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Riko hannun shi Alhaji baba yayi suka koma suka zauna,ya dubi mallam yace " na amince ce saboda kai da kuma amintar mu, amma wlh baɗan Aslam ba, kuma zan bashi auren Asmah kamar yadda ka bukata amma harga Allah bada son raina ba, yaci darajar ka da darajar aminta, tunda wancen lamarin ya faru Aslam baisan ya bada hakuri ba, har yanzu zancen da nake maka daga ni har iyayenshi bai ba hakuri, sannan Abu na gaba Asma'u nidai wannan karan bazan iya kallonta nace mata zan baiwa Aslam aurenta ba, bayan nasan sarai tana soyyaya da kamal, gaskiya ina ganin mun shiga hakkinta da yawa tunda dai munsan bata son Aslam kamal take so, kuma a yanzu bamu da ikon zabar mata miji tunda matsayin bazawara take," murmushi Alhaji mallam yayi yace" indai ta Asma'u ne babu wani matsala yarinya Ce mai biyayya , nasan zata min biyayya ta karbi Aslam a karo na biyu, kuma ita kanta baza ta so Aslam ya mutu ta dalilin taba, ni zan sanar mata komai, amma sai bayan daurin auren" Alhaji baba yace "to shikenan Allah yasa hakan shine mafi alkhairi, saidai kafin nan akwai wasu jarabawar da zanwa Aslam, idan ya ketare yayi nasara, amma idan ya fadi kasani ya rasa Asma'u har abada"murmushi mallam yayi a zuciyar shi yace wannan mutum bazai taba canzawa ba , a fili kuwa yace "yace ba damuwa kana iya mai ko wani irin test insha Allah kuma nasan zai ketare" nan ya labarta mai maganar boye ma Aslam asalin gaskiyar magana yace mai wa tace ya zabar mai ba Asmah ba idan yayi biyayya a karo na biyu ya karba to idan kuma ya butulce yama kanshi.
Bayan sun gama tattaunawa sun tsaida magana nan Alhaji mallam ya bukaci da suje asibiti tare ya duba Aslam fir yaqi saida suka sake kai ruwa rana ya amince badan yaso ba suka tafi, inda suna zuwa kuma komai yazo musu da sauki, Aslam ya nemi yafiya shi kuma alhaji baba ya nuna yamai wani zabi, bayan su Abba sun dawo gida ya Tara su tare da matayensu ya gaya musu halin da ake ciki, kusan dukkansu sunyi farin ciki da hakan dan a lokacin ba karamin tausayi Aslam yaba kowa ba.
Hakance ta kasance haka aka daura auren Asmah da Aslam, Khadijah da Kamal, bayan daurin auren mallam kamar yadda yayi alkawari shida kanshi ya sanar ma Asmah bayan ya damka mata sadakin ta a hannu..............
Oum ummeetarh
07041130088
Share
And
Comment
Fisabillilah🙏
💖DAMA TA BIYU💖
BY
~AYSHA NALADO~
FREE BOOK
{Nasadaukar da wannan book din ga duk wacce ta rasa mahaifiya Allah kajiqan iyayen mu}
Page 89 & 90
A nan kan tiles din Aslam ya kwana dukda ma ba wani baccin kirki yayi, tunani ya lula ta yadda akayi aka bashi Asmah, kai shikam koma waye ya mai wannan babban alherin , saiya tsuguna har kasa ya gode mai, inda halima har goyo saiya mai ya zagaye gari dashi, ya kudiri aniyar gobe zaije ya samu Abba ya fayyace mai komai, daga karshe kuma ya koma tunani da tsare tsaren yadda zasu gudanar da rayuwar auren su shida husnar shi , har adadin yayan da zasu haifa tare saida ya tsara su a cikin daren nan, sai gabanin asubah bacci ya kwashe shi cike da mafarkai barkatai, gashi nan shida husna da yaran su.
Kasancewar bai samu bacci da wuri ba yasa bai farka ba sai da gari ya waye garass karfe bakwai na safe.
A zabure ya mike yana salati, ganin haske ya cika falon, anan toilet din falon yayi alwala ,ya dawo ya kabbara sallah, addu'o'i yayi sosai akan Allah ya taimake shi yasa Asmah taso shi itama ko kwatan sonda yake mata ne, bayan ya gama ya mike ya nufi hanyar dakin ta, a hankali yake tafiya har wani dan sanɗa yake yi kamar Wanda yazo sata, cike yake sosai da daukin ganin kyakkyawan fuskarta da ya kwana yana mafarkin shi, saida ya kwashe kusan minti goma tsaye yana tunanin ta yadda zai shiga ɗakin, karshe dai yayi shahada ya murda handle d'in kofar ya tura, saidai kuma gam yaji kofar amalar ta murza key, a hankali har yana wani kashe murya ya fara kwaɗa sallama a bakin kofar yanayi yana dan yin knocking kasa kasa
Jiya da'ker bacci ya kwasheta, saida ta gama shan kukanta, da tunanin kamal dinta, sai ayyanawa take, yanzu kamal nacen tare da Khadijah, ko a wani hali suke oho ko sun daidai oho, kai tasan ma zasu daidaita ne, dan Khadijah ma ba kanwar lasa bace, take taji wani tausayin kanta ya kamata, itafa son kamal daidai da kwayar zarra bai ragu a zuciyar ta ba,
(aikam dai kina ruwa yarinya inzaki kama dahir ki kama, don kamal dai tuni deejah yar gayu tamai formatting heart d'in shi😅)
Duk da rashin bacci da wuri da batayi ba jiya hakan bai hanata tashi da wuri ba don tun, karfe hudu ta tashi, tayi ta idabah har aka kira assalatu ta kabbara sallah, bayan ta idar ma bata kwanta ba, azkar dinta tayi, tare da addu'o'i sosai, ta roki Allah da ya yaye mata son kamal a zuciyar tunda yanzu ta zama mallakin wanin shi, bayan ta gama kuma ta shiga karatun alkur'ani mai girma.
Daidai lokacin kuma Aslam ya shiga yi mata knocking yana sallama, sarai taji shi amma haushin shi da takeji bai bari ta iya koda kallon kofar bane balle takai ga budewa, ganin haka yasa ya shiga magiyan ta bule amma fir taki, dan ko muryarta baici arzikin ji ba balle yaga fuskarta da yake maitan son gani.
Gajiya yayi da magiya ya bar kofar ɗakin jiki a sanyaye, falo ya koma ya zauna yana jiran fitowarta shiru shiru awa daya awa biyu, bata ba labarin ta, tashi yayi ya koma ya sake bugawa, zuwa lokacin kam bacci ta koma bata San ma yanayi ba,jin shirun yayi yawa, yasa ya hakura da knocking, tunani ya shigayi me zataci gashi har ana neman karfe goma na safe, yanke shawaran girka mata breakfast yayi yasan idan ta fito ta samu yayi breakfast zataji dadi, shi kuma fatan shi a yanzu bai wuce yayi abinda zai burgeta ba.
Kitchen ya shiga nan kuma yaja ya tsaya yana tunanin mai zai girka mata, wani irin abinci tafi so, tunawa yayi rannan yaji suna fira da batool kowacce na fadin abincin da tafi so idan bai manta ba da kunnen shi yaji tace masar shinkafa da miyar taushe , gashi shi kuma bai iya masa ba, wayar shi ya dauka ya shiga Google ya dubo yanda ake masa , take yaga abin Ashe ba sauki, don sai anjika shinkar,kuma sai barshi ya tashi wannan duk bata lokaci ne, kar ta fito ta bukaci abincin ya zama bai gama ba, dan haka fasa yin masar yayi , ya duba yanda ake doya da kwai, nan yaga yafi sauki, dan haka ya dauki doya ya fere da kyar duk ya zafzaftare doyan ya gama ya yayyanka, ya kunna gas ya daura, yana dahuwa ya tsiyaye ya fasa kwai ma'ishi ya zuba kayan dandani ya hau suya, ya gama ya dafa mata ruwan shayi mai peppermint ya juye a flask ya kwasa ya jera a dinning, kar kuso kuga Aslam at dat time, ya hada wani uban gumi, bayan ya gama ya koma kitchen din ya wawwanke kayan daya bata, ya share ko'ina ya goge dama ya iya share share dan ko lokacin zee shikeyi idan ya gaji da ganin gidan da datti.
Sai kusan sha daya saura ta farka, toilet ta shiga ta sheka wankanta tayi su brush da sauran uzirorinta ,ta fito gaban mirror ta tsaya tana daure da tawel, kallan kanta tayi taga duk ta dan rarrame,ta kara haske," murmushi ta sakarma kanta tunowa da yan uwanta da tayi, a fili ta furta"Ooh su hajiya batool ko a wani hali ake ciki, nasan dai Dr bash zai sha jaraba, Allah yasa dai kar ya raga mata, dan batool inta samu miji laku laku ba karamin wuya zaisha a hannunta ta ba".
shafe shafenta tayi nasu mayukanta da turarukanta, harda su humra da hajiya addawiyya ta hada musu na magani ,fuskarta kam hoda ta dan shafa sama sama da zizara kwalli, sai dan man lips data dan shafa mai danƙo.
Bude tafkeken wardrobe dinta tayi ta dauki kayan ciki ta saka pant da bra, maida kallon ta tayi wurin manyan kayanta dake nan Jere rerass a cikin wardrobe d'in, wani lace ta zaro kalan dark green da ratsin milk, dinkin Riga da zani ne saidai rigar karamine mai play, ta sanya abinka ga faran fata, kalon ba karamin kyau ya mata ba, abin wuya ta dauka fation ne mai kyau da dan kunnayensa da warwaraye ta sanya, dauri ta kashe mai kyau na yan matan zamani,bayan ta yi fakin din dogon gashinta, sai ta fito da jeler shi ta tsakiyan ɗaurin, nan ta fito dass da ita, amarya sak, dirinta mai kyau ne ko wani irin dinki ta saka kyau yake mata, bata taran dinki ko wanne yi tajeyi skirt, zani ko dogon riga, duk Wanda ta saka karɓar ta yake yi, plate shoes ta saka mai kyau, ta bude kofar ta kamo hanya kitchen danta samawa cikinta abinci.
Bata taba tsammanin samun shi a kitchen ba, amma ga mamakinta tana shiga ta ganshi lokacin ya gama mopping yana wanke hannu a cikin sink motsinta yasa shi saurin juyowa, idanunsu ya sarke da na juna, take fuskar shi wa washe da fara'a yayinda ita kuma tayi kicin kicin da nata, ganin shi a kitchen d'in gaba daya yasa yunwar da takeji ma tuni ya koma, cikin tsananin jin dadin ganin ta yace "gud morning my luv fatan kin tashi lafiya ya bakunta," jin abin tayi wani banbara kwai a zuciyar ta tace, wai my luv, waye my luv d'in, wlh badai ni ba, can dasu gada, a kai kasuwa.