← Book details Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 126

Sashe 30

Da Izzata Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Su kamal ne suka shigo dakin , ganin haka yasa kamal tambayar ba'asi ,nan ta shiga labarta mishi abinda bash yace tana yi, kamal kunshe dariyar shi yayi yace,

"Kai ammafa Dr ka samu kanwata da yawa ita kake kira da me espo a class, to kiyi hakuri wasa yake miki ai,da'ker ya lallabata ta hakura ,"

Daga nan sukayi sallama da Dr bash, a waje suka dauki Amira suka koma gida,

Kwanan Aslam uku jiki yayi sauqi sosai , nan yace shi ya gaji da zaman asibiti a sallame shi , ƙin sallaman shi bashir yayi yace sai yayi sati, tada balli yayi ba shiri Dr bash ya rubuta mai sallama,............

Oum ummeetarh
07041130088

Share
And
Comment
Fi sabilillah🙏
💖DAMA TA BIYU💖

BY

~AYSHA NALADO~

FREE BOOK

{Nasadaukar da wannan littafin ga duk wacce ta rasa mahaifiya, Allah kajiqan mahaifan mu}

Page 63 & 64

Bayan kwana biyu Aslam tuni ya gyagije , kamar bashi bane aka kai asibiti rai a hannun Allah, saidai fa karfin hali kawai yakeyi , bai bari ya saka damuwa a ranshi ba , ƙokari yake ya yakice ta daga zuciyar shi,amma Abu ya gagara, kullum burin shi ya ganta , duk randa bai sakata a idanun shi ba baya iya barcin kirki, zee kam gaba daya ya tattara al'amarinta ya watsar don yanzu bata gaban shi, kullum cikin yawanta take , ita da beebalo, abu daya ya sani, ya saka ana bibiyar mishi ita duk inda kafar ta ta taka a garin minna , akwai masu bibiyarta,idan kuma ta dawo da daddare, idan ta kowo kanta gare shi zai biye mata, saboda fita hakkin ta, idan kuma bata kawo ba , a sauka lafiya kowa na dakin shi , da safe kuma ba lallai suga juna ba , saboda Aslam da sassafe yake fita, zaije can farkon layin shiga family hause yayi parking ya zauna ya jira har bello ko kamal ya dauki su Asmah zuwa school, a nan yake samu ya ganta kullum , duk kuma ranan da bai ganta a nan ba . har school yake binta a boye a boye, dan kawai ya ganta, idan ba haka ba kam ranar ba zaman lfy , da daddare ma saiya manna hotanta akan kirjin shi yake iya samun bacci,

Yau dai daya kama kwana ashirin cif da sallamar sa daga , asibiti ya gaji, muryarta kawai yake son ji, gashi ba daman yaje family hause, a halin yanzu, dana sani ya shiga yi na cewa da yayi bazai kara zuwa gidan ba yanzu gashi yana son zuwa kodan yaji muryarta amma ba hali, zuciyar shi Ce ta shiga bashi shawarwari iri iri na yanda zaiyi ya samu jin muryarta,

Ya yanke shawaran kawai gidan zai tunkara ya fuske ya shiga falon mummy ya zauna , wata zuciyar kuma tace yayi ɓadda kama ya shiga gidan , a mastayin abokin Amir q
Ƙila ya samu ya ganta, wata kuma tace yayi shigar mata yaje, shawarwari dai marasa kan gado iri iri,

Karshe dai yaga ba ta yadda zaiyi ya shiga gidan ba tare da angane shi ba a haka ya ajiye batun zuwa gida ya barshi a zai tare a school kawai ayi wacce za'ayi , imma zagin shi zatayi tayi, shidai kawai yaji muryarta,

A family hause kam shirye shiryen biki ya kankama , ƙannen mahaifin amir sunzo , neman auren amira kuma an basu, abinka da tuwona maina , ba wani bata lokaci aka gama komai, haka ma batun Asmah da kamal, shima dai duk na gida ne ba wani tsatstsayawa ,

Soyayya tsakanin Barr Adam da zahra kam abin ba"a cewa komai kullum suna maqale a waya, cikin kankanin lokaci yayi nasaran sace zuciyata, tun tana jin kunyar shi tana ɗari ɗari dashi har ta zage ta shiga mayar mai da martanin zafafan kalaman soyayyar da yake gaya mata, don Barr Adam ya iya bi da ita sosai, dama kuma can zahra akwai sauƙin kai ba kamar batool bace, suma dai magana tayi karfi don har an shiga gida an gana gemu da gemu,

Matsalar su ɗaya maryama uwar gidan Barr Adam , tana can ta tada balli, ita bata son kishiya ,saidai ya zaba ko ita ko zahra, shi kuma yace duka yana sonsu, har wayar shi ta dauka ta kira zahra ta zageta tass wai ta rabu mata da miji, zahra kam shiru tayi, aiko batool dake gefenta ta fisge wayar ta shiga mayar mata da martani, kaca kaca sukayi a wayan, Wanda na tabbata da a kusa da juna suke ba abinda zai hana a doku,

Kuka zahra ta fashe dashi wai ita ta hakura da auren Barr Adam aiko batool ta mata ca aka tace " tab tunda nake nikam ban taba ganin wawuyar mace irinki ba, dan kawai kishiya ta kiraki ta miki wannan dan barazanar shine zakice kin fasa auren masoyin ki, to wlh sai anyi auren nan kodan mu gyara ma wancen karkatacciyar matar tashi zama, " ƙwafa tayi tace "kai Allah yaga aniyar jaki yasa baiyi shi da kaho ba, da nine a matsayin ki,da saina ci uban wannan wawuyar matar tashi la'ada waje, kema dole ki ƙarfafa zuciyarki inba haka ba zaki sha wahala a hannun kishiya". Zahra cikin kuka tace "wlh batool bana son tashin hankali ko kaɗan "

Kiran Barr Adam ne ya katse musu maganar da suke, kin dagawa zahra tayi, batool Ce ta daga ta saka shi a hands free , cikin rawar jiki tana dauka ko gaisawa basuyi ba Barr Adam ya shiga bama zahra hakuri cikin lallshi , da kwnatar da kai, tsoran shi ɗaya kar tayi fushi tace ta fasa auren shi , saboda abin da maryama ta mata, don yasanta sarai bata son tashin hankali, don idan ta fasa auren shi shikam ya shiga uku,

Tausayin shi ne ya kama batool ganin yadda ya ruɗe lokaci ɗaya , lallai yana son yar uwarta sosai, tatabbata idan ta shiga gidan baza ta wahala ba, kwandon masifar da tayi niyyara sauke mai ta mayar ta Adana abinta, miƙama zahra wayar tayi ta mata alamar ta amsa mishi,

Amsa tayi ta nuna ba komai ta hakuri nan ya shiga zuba godiya , abin tausayi,

Aiko suna gama wayar ya haura dakin maryama a fusace, kamar wani mayun wacin zaki,

(to nidai nace Allah ya huci zuciyar Mallam adamu,)

Bangaren bash kam ya riga ya gama gane soyyayar batool ta gama mai mugun kamu , har fiye ma da yadda yaji son Asmah, a kwana kin baya,

Saidai kuma shi kaɗai yake kiɗan shi kuma ya taka rawar shi don ita a maƙiyi ma ta ɗauke shi, yanzu gidan ya zame mishi wurin zuwa kullum, haka zaije yata tsokanar ta ita kuma tana zuba mai masifa,

Shima ko a fuska bai taba nuna mata yana sonta ba kullum cikin hade mata rai yakeyi karta raina shi, dan yasan halinta,

tsokananta dashi kullum tayi kwantai bata da farin jini an kawo kudin auren kowa banda nata, kilama ko saurayi bata dashi,

Aiko wadannan kalmomi na fusata batool , nan zata shiga zuba ruwan bala'i , randa mummy kuma ke kusa ta tsawatar mata , to ranar kuwa har kuka sai tayi, tayi tayi ya daina zuwa gidan , ya daina shiga harkarta yaƘi,

Kowa na gidan ya dasa musu ayar❓ gadai su ba wanda zaice soyyaya sukeyi an rasa takamaimai meye a tsakanin su, ko mutum yayi tunanin soyayya suke , idan kuma kaga yanda suke yar tsama sai ka cire wannan mutanin a ranka,

Asmah da Amira kam tsokanan ta sukayi da ta Dr bash , kodai da bash za'ayi, tako ce Allah ya kiyaye wannan dan banzan mutumin, ni wlh ku daina haɗani dashi , don wlh nafi karfin sa ko maza sun kare, Amira tace umumfa batula karfa muzo rashe ya juye da mujiya ,

Ɗan wannan kwana kin da Dr bash ya kwashe yana zarya gidan , ba ƙaramin sabawa batool tayi da, yanayin tsokanar shi ba, a kullum har Allah Allah take yi lokacin zuwan shi yayi , haka zata zarya tana duba agogo,

Yau dai bai samu zuwa ba, luƙuss tayi a kan bed bini Bini ta duba agogo har wurin ƙarfe yadan dare babu shi babu labarin sa ,

Zahra ta dubi Asmah dake gefenta ta nuna mata batool , da zunɗe, kallon batool din tayi suna dariya ƙasa ƙasa, cikin rada zahra tace "yau mutumin ta baizo ba duk ta wahala , in anyi magana tace bata sonsa Allah ya kiyaye," Asmah tace "aiko dai yau zan gwada ta naga karshen karya,"

Tashi tayi ta fita daga ɗakin tadan labe can kuma ta shigo da sauri hankalinta adan tashe, tana cewa" innalillahi wainnailaihi rajiun, Allah sarki Dr bashir " zahra itama cikin pretending, tace "subhanallahi me ya samu Dr din'. tace "yanzu aka bugo ma mummy wai yayi accident,"

Batool da dama tunda Asmah ta shigo ta miqe daga kwance da take , jin kuma abinda akace yasa ta miƙe a zabure , tana dafe kirjinta dake bugawa da karfi kamar zai fado kasa tace " da gaske kike Asmah? Innalillahi wainnailaihi rajiun na shiga uku na lalace " gani sukayi ta zube akan gado dabass, tana wani irin numfashi kamar zata sume,

Cikin dan tsorata Asmah ta kalli zahra suka hada ido aiba shiri Asmah tace"kefa da wasa nake miki, kawai munyi ne muji bakin ki,"

Dagowa tayi ta kalli Asmah tace"da gaske wasa kike" tace "wlh wasa ne kinji na rantse " ajiyar zuciya ta sauke kafin ta koma ta kwanta rigingine,

.aiko dariya suka shiga kwasa suna mata tsiya , wai wannan wane irin gulmammen soyayya ne, gara inza a fito fili tun lokaci bai ƙure musu ba ehee,

Duk rawan kan batool kasa tanka musu tayi , don da gaske maganar ya dake ta sosai, itadai baza tace ga dalilinta na damuwa har haka ba dan kawai ance bash yayi hatsari, dan ita dai tasan bata sonsa shima kuma yasha gaya mata shi me zaiyi da ita,
Chapter 30 · 0% Book details