Sashe 90
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 4 min read
wannan kwamiti da wasu bayanai kan wasu ayyukan da kai ne ka jagoranta kwanakin da suka gabata. Muna sa ran cikakken ha in kai daga gare ka Lumshe idanu ya anyi ka an, sannan ya sake bu esu, babu alamar wani fargaba ko damuwa a fuskar tasa ya ce, Yes, sir. I m ready to answer your questions. Kai Brig. Gen. Abraham ya an jinjina yana juya takardar gabansa, sannan ya cigaba da da fa in, Kafin mu ci gaba, Lt. Col, muna son tabbatarwa ko kana da masaniya game da acewar wani Lieutenant mai suna Ojo, wanda ya kasance cikin rundunar da ka jagoranta a aikin karshen nan daya gabata? Shiru na an lokaci kamar bashi da niyyar bada amsar, sai kuma yay wani an malalacin murmurshi, Yes sir! Na sani, sannan ba ata yay ba yana hannuna, kuma yarona ne na kusa da kowa ya sani. Wasu dalilai ne kuma yasa na ri esa, nasan kuma yin hakan ba laifi bane a angaren bincike Hall in ya yi shiru tamkar babu mai rai a ciki, kowanne da abinda yake tattaunawa da zuciyarsa game da amsar daya fara badawa kai tsaye da babu gargada ko shakka, sun san wanene Haysam, bashi da tsoro, bai yarda ya ajiye gaskiya ba koda zata e. Suko manyan jami an da ke zaune a teburin gefe masu saka ido a madadin gwamnati kowannensu cikin matsanancin mamaki suke kallon Zak-Shadow in, dan sun fahimci ya ma wuce yanda ake labarinsa ashe. Ji yanda yake bada amsa kai tsaye fuskarsa a ha e, babu wani shakka ko tanka e abinda zai fa in. Ba ruwansa da yay musu da i ko kar yay musu. Brigadier General Abraham Yohana ne ya katse shirun da an murmushi. Cikin son gyara tambayarsa ya ce, Hakane, sai dai a wannan yanayin kasancewar Ojo a hannunka ya canja labarin daga bincike zuwa son kare kanka a dalilin wata gaskiya da akace ka fahimci shi Ojo in zai fitar data shafeka. Shiyyasa report ya nuna inda da gaske akan tuhuma kake son kama Ojo office zaka kawo shi ba wani waje daban ba da baida ala a da wajen aiki. Domin kuwa an samu wasu videos a kayan Ojo da bincike ke ganin saboda shi ne ka killaceshi Zak-Shadow yay wani sakaran murmurshi a karo na biyu yana an kauda kansa gefe, sai kuma ya maida dubansa ga Brig. G. Sir! I'm sorry, mizai hana muje kai tsaye ga abinda kuke bu atar ji kawai. A lokuta da dama ana min kallon bahagon mutum, sai dai a zahiri mutane ne basa fahimtata, a komai nafi son abu kai tsaye, maida gaba baya a zance nakan kallesa kamar aikin mata ne. Dan ALLAH cikin girmamawa kawai muyi abinda ya dace Cikin taushi yayi magana, amma ga mai tsatsar zuciya zasu kalli kalamansa a masu zafi. Kamar jami'an gwamnatin dake wajen da wasu a membobin zaman. Sai dai shi Brigadier General yasan Haysam sani na amana da gaskiya, shiyyasa ko ka an bai auki kalaman nasa a komai ba face na mazan fama. Sai kawai ya murmusa idanunsa akan Zak-Shadow in. Shi ko Lt. Col Peter Okon cikin jin zafin kalaman Zak-Shadow in ya ce, Lt. Col Haysam Abdul-rasheed Shehu. An samu wasu video clips daga ayyukanka da suka gabata, musamman wanda ya faru a yankin Bankaura, wannan video clips kuma a cikin kayan Ojo amintacen yaronka aka same su kamar yanda kaji tun farko. Gasu za'a kunna maka ka gani Ko kallon inda yake Zak-Shadow baiyi ba, bai kuma amsa masa ba. Koda aka kunna tvn ma yaja wasu sakanni kafin ya kai idonsa kansa. Zuciyar sa ta an buga musamman a wajen harbin Umman Nimrah da mahaifinta, amma bai nuna ba. Sai dai har videon ya kai arshe bai auke idonsa akan tvn ba, sai da ma Brig. G. Ya an buga table in sannan. Su duka ya kalla cikin idanu aya bayan aya, sai kuma ya an yi murmurshin da su kuma ya daki zukatansu. Kai tsaye ya ce cikin murya mai arfi, Sir! Ai ban san a aikin namu harda masu aukar aikin videos ba ma sai yanzu, ba zan tsaya ina kare kaina da magana kawai ba, sannan ban damu da sanin dalilin daya saka a aukemu videos in ba. Sai dai ko bayan na ata kamar yanda masu aukar ko ogannin da suka saka a auka in ke bu ata ina so a bincika comm log in mu da footage in asali dan wannan edited video ne. Sannan akan Ojo ban yarda da fallasa abokin aiki ba tare da hujja ba. Mun fi son tabbatar da gaskiya kafin mu kai rahoto. Tabbas bu un kalaman Zak-Shadow ba aramin tasiri sukai a zukatan su Brig. G. Ba, dan haka hall in yay shiru na wani lokaci, kafin Col. Haydar ya nisa cikin jimami da nauyin furuci ya ce, Lt. Col. Haysam ka fahimci cewa wannan kwamiti ba yana tuhumar ka da laifi bane bisa son kai ko wata manufa, amma muna bukatar gaskiya. Wannan al amari ya wuce duk abinda muke tunani. Musamman daya kasance mun samu tabbacin Ojo na hannunka kai da Major Imran