Sashe 67
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ka ewa akan Imran in. Saboda itace mai aure na? Humm bazaka fahimta ba, kasan mata da kishi, bana son maimakon ri e amanar da bani da haufi a kanka wajen ri ewa al'amarin ya koma wani abu daban. Taya kake tunanin zata ri e yarinyar nan a wannan yanayin data fara nunawa? Sai ta kasheta ai, ince dai arshen kishin nasu kenan ko. Mtsoww, ni kada ka ata min rai ma Shiru Imran yay bai sake magana ba, amma tabbas shi yasan akwai rigima. Dan kishin Nabeeha ba oyayye bane ga kowa. Tunda har akan an uwansa da Mammah ba oyewa take ba. A haka likita ya dawo ya duba Zak-Shadow in, ganin ya akko allurar barci ya dakatar da shi. Ka sallame ni kawai Cikin girmamawa sojan likitan ya ce, Kayi ha uri Sir ko zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu ne, dan jikinka na bu atar hutu sosai Wani kallo ya watsa masa kawai. Da sauri likitan yace, I'm sorry Sir Murmurshi Imran yayi a karo na farko. Sai kuma ya kalla likitan. Karka damu ka sallame shi kawai, idan baiji dai-dai ba sai ya dawo Okay Sir A ranar aka sallami Zak-Shadow daga asibiti. Shi mutum ne mai adalci da duba na asa da shi akan komai daya dace. Dan haka maimakon tafiya gida ya samu hutun jiyya da aka basu sai ya koma jihar da auyukan su Bankaura suke ashinta ya duba sojojinsu da aka kwantar a asibiti. Ba aramin tashin hankali ya shiga ba da ganin irin arnar da akai musu. Dan sojoji da yawa sun jikkata. Hakama ya shiga har inda aka killace gawarwakin wa an da suka rasa ransu, ciki harda Captain Musa. Lokacin daya ora idanunsa akan Captain Musa sai da suka sake juyewa, Captain Musa jarumin soja ne an amanarsa, ya taka rawar gani matu a akan wannan ya in, babu abinda zasu masa sai addu'a. Lokaci aya aka harbesu da Major Imran, shi da yake kwana ya are tun a jejin ya rasu, shi kuma Imran ya suma. Bayan ya gama zagaya su kaf daga asibitin cikin barrak inda sojojin suke su, babban asibitin jihar ya nufa itama. Nan ko mutanen auyukan ne da suma suka samu raunuka. Kamar yanda yay fata suna samun kulawa ta musamman daga gwamnati, akwai kuma jami'an sojinsu a tare da su, da an sandan farin kaya. Suma ya dubasu. Daga nan ya wuce sansanin da aka samawa wa an da suka tsira. Ganin yanda aka barsu a wula ance sai a tsakar wajen suke kwana damma zafi ne ransa ya aci. Dama akwai zaman da zasuyi da Gwamnan jihar da shi da wasu manyansu a washe gari. Ai gaba aya ya tattara takaicinsa ya ajiye har zuwa lokacin zaman. Daga sansanin cikin jejin da nasu sansanin yake suka koma. Komai ya lalace, sai dai anata kafa sabbin tantuna an kuma kawo wasu rundunar sojojin dan bazai yiwu abar yankin a haka babu tsaro mai arfi ba. Har dare suna a cikin jejin, dan har cikin auyukan Bankaura, Gangare, da Marke sai da suka shiga. Anan dama abubuwan sukafi tsamari musamman Bankaura a arshe- arshe. Dan an musu arna matu a da zasu da e basu maida gurbinta ba. Har a yau ana za ulo gawarwaki a cikin jejin da auyen Bankaura irin na wanda suka uya a wasu wajejajen suka kasa fita. A lokacin da suka wuce ta ofar gidan su Nimrah ya kwashe mintina uku yana kallon gidan da tuna abubuwan da suka faru tun daga farkon zuwan su Imran da sanda yay kiransu. Randa Nimrah tai musu zancen falawa har zaman da sukayi da Ummanta. Rayuwa kenan, cikin abinda baifi sati hu u ba komai ya lalace, dan gidan ya rurrushe sosai sakamakon bomb da yaran Dagger suka tayar musu suma tamkar gidan iyayen Umman Nimrah. Shiyasa suma baya jin akwai wani sauran zuri'ar data rage, idan kuwa sun rage to alilan za'a samu kuwa a ciki, suma yara ne ko wanda basa a garin al'amarin ya faru. Tunda suka baro jejin zuwa masaukin da aka bashi a cikin barrak na jihar wanka kawai ya iya yi ya zauna yana wasu rubuce-rubuce, bayan ya kammala kuma ya hau salloli. Bai kwanta ba sai da yay sallar asubahi. Zuwa arfe goma dole ya farka dan suna da meeting da zasu zauna da Gwamna akan harkar tsaro. Amintaccen yaron nan nasa, kuma munafukinsa a bayan fage da tunda ya iso yake nane da shi ya kira a waya. Babu jimawa ya iso. Bayan mi a gaisuwar girmamawa tamkar wani mutumin arzi i kansa a asa ya ce, Sir! Akwai abinda kake bu ata ne? Batare da Zak-Shadow ya dubashi ba ya mi a masa wata aramar takarda da ATM insa. Kaje Boutique ka sama min kayan da zanyi amfani da shi. Saura ka ata min lokaci . Ya arashe maganar arshe cikin dakewarsa da rashin aukar raini. I'm sorry Sir, bazan da e ba in sha ALLAHU Zak-Shadow bai sake tanka masa ba, hasalima ya auke kansa ya koma gaban takardun da yay ta rubutu a daren jiya. Koda Ojo ya fito sai ya harari akin da Zak-Shadow yake, kafin ya kalla ATM in daya bashi da takardar mai auke da pin insa ya ta e baki. Baiyi yun urin komai ba sai da ya fita a barrak in gaba aya. Nesa sosai ya samu waje ya tsaida mai mashin in daya akko shi. Sauka yayi ya bashi ku in, ya samu asan wata bishiya ya zauna. Kamar yanda ya saba kai duk wani motsi da bayanan Zak-Shadow ga iyayen gidansa yanzun ma haka yay kira ya rattafa bayani. Tun daga dawowar Zak-Shadow a jiya har komawarsu jejin nan da auyukan, da takardun da yaga ya baza a akin daya kwana. Daga can wanda yake gayawar ya ce, Su kayan daya aikeka ka saya na miye? Sakawa zai yi sir! Sai dai kamar akwai inda zasuje shi da wasu manyanmu dan jiya bayan mun dawo barrak in sunyi wani aramin meeting su uku Na baka daga nan zuwa awa aya, nasan ina zai je. Idan ba haka ba kada ka kirani. Sannan ka sani, dolene a yanzu sanya idonka yafi na baya, dan mun rasa yara biyu a wannan tafiyar, an kashe aya, aya na cikin wanda aka jima rauni a asibiti Babu wata damuwa Sir, komai kuke bu ata zanyi fiye da hakan, kada ka manta na shiga rigar soja ne kawai saboda aikin ku badan zama soja ba. Shiyyasa ma a ya in nan ban yarda na cusa kaina a halaka ba Good! Da kake tuna hakan. Yaushe zai koma Abuja? Bani da cikakken bayani akan hakan shima, amma nasan bazai jima ba tunda yana ashin hutun jiyya ne shi da aminin nashi dama sauran Captains in mu. Dan shi ka ai ma yazo jiyan alamar akwai abinda yazo yi, duk da dai nasan shi mutum ne azababbe akan aiki shiyyasa ake shan wahalar cimmas cikin sau Mtsoww! Zai kuwa gane kuransa a wannan karon . Daga haka ya yanke kiran. Ojo dake dariyar mugunta zaram ya mi e yana cire layin daya saka a wayar tasa yay kira, ya maida ainahin layinsa da kowa ya sani sannan ya sake tare mashin ya hau ya tafi aiken Zak-Shadow.