Sashe 21
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Babban ya i kam _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ _Chapter 16_ __________________ https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6 *_Kowace mace na matu ar son taga ta gyara kitchen inta kodan ta kalla itama taji da *_Dun ule ku in ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_* *_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_* *_To kwantar min da hankalinka awata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sau i da rahusa._* _Ta bu e adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da da i, akan farashi mai sau i, kaya an zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._ *_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k *_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. Ga sau i abaka tamkar yauta __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ......Aiko dai akwai aikin babba ma kuwa. Dan kuwa da asuba dai koda Inna tasa su Alawiyya su rakota gida suna juyawa suka fita tai alwala sai ta shige akin girkinsu dake a tsakar gidan, da yake ba girkin ta ta a yi ba babu komai a ciki sai icce da aka tara da kayan ruwa da abubuwa da take kaiwa ciki ta aje, anan tayi sallar sai da gari ya waye sannan yaji motsinta zata fara shara. Fitowa yay daga akinsu yana kallonta. Dan massalaci ma kasa zuwa yayi saboda ciwon daya kwana da shi na ciki. Tana ganinsa ta ajiye tsintsiyar zata gudu ya ce, Kinga yi ha iri tsaya. Cigaba da shararki in dai nine ma na koma . Ya koma cikin akin ya yaleta. Baki ta tura itama, ta auki tsintsiyar ta cigaba da sharar. Haka yau ma sukai wannan yini tana masa wasan uya. Da yaga ta takura a gidan sai ya lalla a ya fita ya koma tsohon akinsu dake soron gidansu ya kwanta a can. Abinci ma aikowa yayi aka amsa aka kai masa can duk da kuwa daga gidansu aka aiko. Hajjaju amarya Indo ba jiya taji da in gudu ba, yau ma ana yin sallar magriba ganin ya shigo yace zaiyi wanka a lokacin dan bai samu yayi da rana ba, yasan kuma bazai iya barci ba in baiyi ba. A arare takai masa ruwan bayi, yana shiga ta sulale zata gudu, sai dai ta samu ofa a rufe ta gidan. Kamar zatai kuka ta juyo ta dawo. Amma mi sai dabarar shigewa asan gado tazo mata. Dan haka sauri-sauri ta shimfi a tabarma ta kawo wasu orai da babu komai tasa a gaba-gaba ta yanda bazaka kawo da mutum a ashin gadon ba ta shige abinta ta kwanta ko tsoro ma bata ji. ALLAH sarki bawan ALLAH Abdul-rasheed, hankalinsa kwance ya fito yasan dai bazata iya bu e gidan ba, koda ya shigo akin bai ganta ba yayi tunanin tana inda ta ma ale azun da asuba. Sai ya ajiye kayan wankan yaje ya lallasota ta dawo, amma mi babu ko alamarta, da sauri ya nufi soro kofa a rufe yanda ya bari, ya sake dawowa ciki neman duniya ba A'isha. Mamaki da tsoro suka kama shi, to ta ina tabi ta fita? (Katanga), zuciyarsa ta ayyana masa. Zama yay yana dafe kansa kawai, dan wlhy kunya yake ji bazai iya zuwa gidansu ba yau kuma. Idan jiya basu gano shi ba ai yau sai su gane. Haka ya ha ura ya mi e ya tafi massalaci sallar isha'i. Duk abinda yake tana jinsa, daya fita kuma bata kawo a ranta ya fito ba ta fice gidan ta cigaba da kwanciya a ashin gadon har barci yay awon gaba da ita anan. Bayan sallar Isha'i Abdul-rasheed ya dawo, haka ya zauna shiru zuciyarsa na masa sa e-sa e, gefe yana alubalantar kansa da rashin ha urinsa, dan ila da bai mata abinda yay matan ba da hakan bata faru ba. Ga tsaraba ma ta kasa zama ta duba sam. In sha ALLAHU zai daure ya ri e kansa ya bita a hankali. Da wannan tunanin ya ingire. Da asuba fitsari ya kama A'isha har yana neman zubowa, dan haka ta fito cike da sukur-sukur in daya tada Abdul-rasheed, dan haka ya haska fitila da tunanin ko era ne ya shigo musu. Amma yana kunnawa ya haske A'isha na fitowa a asan gado. Mamakin duniya ya ishe sa, ya zuba mata ido kawai. Itako tayi tsuru-tsuru kanta a asa tana matse afafu dan fitsarin neman kufce mata yake. Fahimtar hakan da yayi ya saka shi sakin murmurshi, muryarsa a sau e yace, Amshi fitila kije kiyi Da sauri ta amsa kuwa ta fice. Shima ya mi e ya sauka a gadon yana sauke ajiyar zuciya. Amma lallai yarinyar nan ta cishi wasa jiya. Yanzu nan tana asan gado dama duk bulayin daya dinga yi. Wato ita dai mace duk antarta akwai wayo da dabara. Da wannan tunanin ya fito da buta a hannu, baice mata komai ba ya auki fitila data ajiye zata fara alwala ya wuce bayi, sanda ya fito ta gama zata wuce. Dan haka cike da lallashi ya ce, Dan ALLAH ki zauna a gida to kada kije ko ina na dawo na baki tsarabarki da sa on Inna, kada yazam akwai abin lalacewa a ciki kinga zai lalace Kanta dake asa ta jinjina masa. Sannan sum-sum ta shige ciki. Shima yay alwala ya fita. Koda ya dawo da wannan bu e tsaraba yaja ra'ayinta, har hantsi ya fito ya fita ya sayo mata shayi, sai kuma ga kayan kari Inna ta aiko. Da lalla a, da lallashi da kwantar da kai ya samu wannan yini dai aka yi shi lafiya. Da dare kuma ya kafa ya tsare ya nuna mata shi tayi duk yanda take so. Ganin ya i kulata da abinda take gudun a yinin ma ko kusa da ita bai zauna ba balle ya ta a mata hannu sai ta ha ura ta kwanta a gadonta, amma acewarta da ido aya zatai wannan barci. Da yake shi barcin ya fita wayon bata ma san ya kwasheta ba har wanda take tsoron ya zauna a bakin gadon kusa da ita yay mata addu'ar barci sannan ya koma nashi gadon. Wannan sabon yin biris daya auka ya kawo masalaha a tsakaninsu, itama ta sake jiki suka koma kamar da. Sai dai kwana kusan shida kuma yaji fa yana neman halaka, a daren ya kasa ha uri ya sake maimaita na wancan daren, koma muce abinda yafi na wancan daren dan ya sameta fiye da waccan ranar, sai dai kuma ta fitgice masa dole ya barta batare da cimma buri ba. Daga nan ne fa ta sake birkice masa. A daren washe gari kuwa bata kwana a gidan ba, ta sake gudawa gidansu cikin su Nana ta kwana. Ita kanta Innar da su Nanar basu farga da ita ba sai da asuba da Inna ta tashesu suyi salla. Rasama abin fa a tayi, yau ma sai tace su Alawiyya su rakata gida kawai. Kwanakin da suka biyo baya har hu u A'isha bata daina yo tsere ba. Abdul-rasheed kuma ya zuba mata ido, hasalima ya koma maida hankalinsa batun bu e wajen inkinsa ya yaleta. Hakama Baba yana sane A'isha a gidan take kwana, amma bai ce komai ba sai dai yayi murmushi kawai. Koda Inna tai masa magana a cikon kwana na hu un sai cewa yay, To mizance, tunda shi bashi da ha uri da kawaicin barin yarinya ta sarara ka an ma kenan. Ke kuwa naga kema haka kika dinga yi min Karima, arshe sai da Baba ya rakoki da tsumagiya gidan nan saboda can kike zuwa. Ai kai ka jika Malam, ana maganar arzi i saika dinga sakko wadda ba'a tambayeka ba. Amma ka bani dabara nima da tsumagiyar zan korata yau. Ina laifin yaron nan ai yayi kawaici ma. Aure wata shida haba ai a yaba masa. Abdul-rasheed da ha uri da zurfin ciki. Su sauran an uwansa wa yayi wannan ha urin. Tijjani ma da yafi kowa rashin ta idonsa ko tsallake rana yayi Haka ta fita tana sababi. Baba kuwa sai murmushi yake abinsa kawai... Washe gari kuwa Inna ta shiryama A'isha tsaff, dan yanzu dai sune iyayen tunda babu wani nata a kusa. Kuma a wannan zamanin nasu na adalci a na kowa ne. Babu wani surukutar mugunta ga matar a da uwar miji, yanda suke ma ansu haka suke ma matan ansu saboda adalci da yawar zuciya, haka suma surukan suna aukar iyayen miji iyayensu ba irin na yanzu ba da suke ganinsu kamar koshiyoyi. Kamar ko yanda ta saba ana cikin sallar isha'i sai gata ta shigo soron gidan da san arta. Caraf Inna dake a soron ta dalleta da Torchlight, A'isha tai tsaye cak tsuru-tsuru da idanu, sai kuma ta du a tana gaida Inna dake tsaye kawai tana kallonta. Batare da Inna ta amsa mata ba ta ce, Juya muje Kallonta A'isha tayi kamar zata fasa kuka, Inna ta ha e fuska kuwa ci in-ci in. Sum-sum ta nufi ofa dan tasan dai yau ruwa ya arema an kada kam. Haka Inna ta sata a gaba har gida da ar tsumagiyarta a hannu, badan ta daketa ba sai dan ta tsoratata. Karo na farko da Inna tazo gidan kenan, suna isa ofar aki taci karo da buta, auketa tai ta maida gefe suka shiga akin. A