Sashe 52
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
ce, To uwar soki burutsu zaki fara ba in surutun naki ba. A gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa da rana. auki awararki kici bana son magana Baki ta tura sosai, kamar zatayi kuka ta ce, Na rantse da gaske nake Umma. Kuma har wajensu naje ma, har naga wani mai irin kayan...... ALLAH idan baki min shiru ba sai na fasa maki baki, koki tashi ki wace wajen Inna in damuna zakiyi. Mi kuma tayi za'a fasa mata baki? Bayan azu kika gama dukanta Baba dake shigowa ya fa a. Sannu Umma tai masa sannan ta ce, Ta isheni da surutu ne. Wai taga fatalwa ko a gidan uwarwa ake ganin wata fatalwa Shi abin ma dariya ya bashi, ya ka a kai kawai yana ar dariyar da fa in, Uwa sarkin magana, Zakanyar Kawu Tanimu, in dai zance ne a bar miki abinki Baba banyi arya ba fa, kuma harda mai irin kayan...... Murfin kwano da Umma ta jawo ya sakata saurin dafe bakinta dan tasan ka an daga aikinta ta kwaf eta da shi. Shima Baba sai ya shige kawai yana murmurshi.. koda Nimrah taga Umma da Baba sun i sauraren labarinta na fatalwoyi sai ta surare ta koma sashen kakarta Inna. Acan ta fara bata labari, sai dai anyi rashin sa'a itama Inna ta kwa eta batare data maida hankali a zancen ba ta auka soki burutsinta ne kawai data saba. Daga arshe ma korota tayi daga sashen akan ta tafi ta bata waje barcin zatayi. Daga haka Nimrah ta fice cikin yara suka kama wasa. Can kamar an tsikareta taba yaran labari suma, abinka da uruciya sukace arya ne, sai ta dage akan suje ta nuna musu. Aiko haka suka ha a gayya suka fita bada sanin iyayen ba bayan gidan. Tafiya takanas babu ko gargada ta kaisu har wajen mangwaron nan dake cikin gonar Baban Zakiru kamar yanda ta fa s, sai dai a yanzu babu kowa wajen mutanen sun tashi sai robobin ruwa da suka sha da takardun nama, wata ledar ma ba'a cinye naman ba. Haka sukaita tsincewa suna ci, suka tattaro robobin ruwan dana lemo suka dawo gida. Yawancin iyayen sun gansu da wa an nan robobin ruwa dana lemo, amma sai basu tambayesu daga ina ba saboda a wasu lokutan kawunsu Tanimu kan raba musu dan su dinga zuba ruwan zuwa makaranta, shima kuma yana zuwa dasu ne daga birni. Da yamma gab da magriba Umma ta gama aikin tuwon dare. Ruwan data umama ta iba taima Nimrah dake ta damunta da surutu tana cin gya a wanka. Ta shafa mata mai ta saka mata kaya. Tuwon Inna data zuba a langa ta saka a botiki ta tura gaban Nimrah in. auki tuwon Inna kikai mata, sai ki dawo ga miyar nan itama zan saka miki a wannan botikin ki auka ni zan shiga wanka bana son a kira magriba, saura kuma dan ALLAH kiyi abinda ban saki ba, ALLAH bazaki bini gidan Malam ba in har kikai min wata ar nan To Umma, ALLAH ba abinda zanyi, dan ALLAH kada kice bazaki je dani ba, ina son na gaida Malam da Iya Nimrah ta fa a cikin tsalle-tsalle tana daukar botiki. Ita kuma Umma ta auki ruwan wankanta ta shige bayi tana fa in, In da kinso ganinsu ai afarki tasan inda suke Nimrah da bataji mi Umman ta fa a ba ta auki tuwon Inna ta fita cike da murna zasu gidan Malam, (Malam dai shine mahaifin Umma, babban malami ne a yankin kuma dattijon arzi i da kowa ke girmamawa) koda Nimrah ta shiga sashen Inna babu kowa, dan dama ita ka aice a sashenta tunda kishiyarta ta rasu sai dabbobinta. aki ta shiga ta ajiye mata kwanon tuwon ta fito, ta sake komawa sashensu ta akko miyar ma ta kawo. Harta juya zata tafi ta hango wayayen kazar Inna dake akurkin jikin katanga gab da fita a sashen. Kwana tayi ta koma wajen akurkin ta du unna ta auki wai aya ta saka a botikin hannunta, sai kuma tayi an tsai kamar mai lissafin sauran wayayen, hannu tasa ta ara aukar aya, ta ce, aya Umma aya. To Baba fa, shima bari na aukar masa, idan Inna taji harda shi akaci ai bazata dake shi ba tunda yayi babba sosai. tana maganar tana le a cikin akurkin duba wasu wan. Sai dai maimakon ganin wari taci karo da wata jaka. Hannu tasa ta jawo jakar. Tare da fa in, Lah Inna har cikin jaka take oye wai, aiko saina ibawa Babana da Kawu . Tana maganar tana kici-kicin bu e jakar, sai dai ta kasa. Abinka da yaro tana jiyo maganar Inna ta yayimi jakar ta jefa a botikin ta auka da gudu ta shige bayi, sai da Inna ta shigo ta shiga akinta Nimrah ta fito da gudu nan ma ta fice zuwa sashensu da wannan ar jaka da zato ta ke ita wai ne Inna ta oye a ciki. Lokacin da take shigowa sashensu Umma ta shige aki dan anata kiran sallar magriba. Anan tsakar gida ta ajiye botikin da jakar duka ta nufi akin gayama Umma takai wa Innar tuwon. Koda ta fa a mata sai tace taje tayo alwala suyi salla su tafi. Cikin farin ciki ta fito, dan tasan koba komai zatayi wasa da ruwa ai. Sai da ta gama facaccalinta kuwa sannan ta tafi akin tayi sallar. Ta mance da batun wai taci tuwo suka tafi gidan Malam. Kafin su dawo ta ingire barci, sai goyota Umma tayi ma. Sanda Baba ke shigowa gidan ta jima da yin barci. Misalin sha aya na dare Umma da Baba sun gama cin abinci da hira Umma ta fito kaye-kaye tsakar gida sai ga Tanimu ya shigo sashen da sallama. Amsa masa tayi, tana murmurshi da fa in, A'a kawun Nimrah baka kwanta ba? Wlhy kuwa ban kwanta ba Yaya, nace bari nazo nai muku sallama dan in sha ALLAHU gobe zan koma birni. Amma sai yamma zan wuce da safe dai zanje hayi wani aurin aure, daga can nake son nabi wasu abokanmu da zasu zo aurin auren suma daga birni. Kai kawun Nimrah da wuri haka, wannan karon ai baka da e mana ba, kwata-kwata bakafi sati biyu ba Wlhy naso yin sati uku ne fa, to ganin mota a sau e yasa zan wuce kawai. Amma bazan jima ba nanda arshen wata zan dawo yin dashen albasar nan. Ato da gaskiyarka, ALLAH to ya kaimu. Ka shiga Yayan naka na ciki ai, bari nima na arasa kaye-kaye dan karnuka na shigo mana da dare . Amsawa yay da to yana shigewa, ita kuma ta cigaba da tattare kayan tsakar gidan. Ciki harda botikin nan da Nimrah ta sakawa jaka a ciki. Batare da Umma ta damu da miye cikinsa ba ta rufe shi da murfinsa dan dama tana kwa in fulawar taliya ne a ciki idan zata murza. aki ta shiga da su ta ajiye, daga haka ta zauna suka cigaba da hira da Baba da Tanimu.... >>>>> <<<<< Tunda ragamar jejin ta koma hannunsa a daren jiya duk ya kasance a tsarguwa. Ko barcin kirki baiyi ba, dan haka kawai yake jin wani abu mai nauyin gaske a zuciyarsa. Ga yawan fa uwar gaba dake samunsa. Bafa yau ne karo na farko da Zak-Shadow ke barin jejin shugabanci ya koma hannunsa ba, amma sai yake jin na wannan karon da girma sosai. Wajen misalin arfe uku na dare barci ya gagaresa gaba aya, sai kawai ya tashi. Wayar sadarwa ya auka, yay kira kai tsaye ga dukan Captains dake cikin rundunar, cikin bada umarni ya bu aci ganinsu. Basu ko ata lokaci ba, dan kafin arfe hu u na asuba sun tattaru a sansanin nasu. Meeting Major Imran yay da su na minti talatin kawai, kafin biyar na asuba ya sallamesu kowa ya nufi komawa sansaninsa....