← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 94

Sashe 87

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

biyu suka bu aci ganinsa. Bai gayama Zak-Shadow ba ya baro gidan akan zai je wani waje ya dawo. Shima Zak-Shadow bai tambayesa ina zai je ba ya wuce cikin gida dan akwai aikin da yake so ya kammala. Zuwa gobe da safe yake so ya zauna da Ojo. Sojoji hu u ne a matsakaicin akin binciken da aka shiga da Major Imran Abbas, duk da kuwa yasan akin ba ba onsa bane. Cikin nutsuwarsa ya kai zaune bayan ya mi a gaisuwar girmamawa a garesu, sai dai a zuciyarsa ya fara wasi-wasi amma ya danne.. Brigadier General Abraham Yohana ne ya fara magana. Major Imran Abbas ka sani wannan zamane na sirri. We expect full honesty from you . Ya an ja numfashi yana jujjuya biro a yatsansa, kafin ya an matsa kusa da teburin da takardun ke kai. Before we proceed Major, ya sake fa a cikin murya mai sanyi sai dai cike da iko, this is an official military inquiry. Anything you say here will be part of the record. Are you willing to cooperate fully with this Board? Cikin girmamawa Imran ya ce, Yes, sir! I ll cooperate fully Takardar gabansa ya an duba, sai kuma ya ago yana sake kallon sauran jami an da ke gefe, kafin ya dawo da idanunsa kan Imran. Good. Let s start simple. A ranar 17 ga watan jiya May a ina Zak-Shadow ya kwana? Ba aramin dukan zuciyar Imran wannan tambaya ta bazata tai ba. Sai kawai ya samu kansa da zubama Brigadier General idanu na sakanni. A zuciyarsa hasashen miya kawo wannan tambayar yake? Brigadier General ya sake katse masa tunani da maimaita tambayar. Ajiyar zuciya Imran ya sauke. Kai tsaye ya ce, Sir yana sansani tare damu Washe gari 18 fa? Gaba aya Imran ji yake kamar zai rikice, amma ya ce Itama haka.... Ka tabbatar? Shiru yay ya kasa cewa komai. Brigadier General ya cigaba da fa in, To amma miyasa kuma anan bayanansa ya sa a da abinda ka fa a yanzu? . Yay maganar yana yin nuni da projector daya bada umarnin a kunna. Ana kunnawa kuwa videon ranar da Zak-Shadow ya koma jejin bayan an kai hari na biyu garin Marke da Gangare ya bayyana. Tun daga isowarsa sansani a mashin da shigarsa mota shi da karnukansa har isowarsu Gangare da bayanin da yayi cikin acin rai kan abinda ya faru, inda yace baya nan cikin kwana biyu kacal sun bari an musu irin wannan illar ya maimaita kansa yafi sau hu u dan a sake tabbatar da aryata abinda Imran in ya fa a ma. Har yanzu kana akan bakan ka na cewar yana nan in komai ya fara faruwa? . Lt. Col. Peter Okon ya fa a yana tsatstsare Imran da idanu. Shiru Imran yayi zuciyarsa na wani irin dokawa, zuwa yanzu ya fara hasaso al'amari mai girma, dan kuwa ba rami miya kawo rami. Babu dalili miya kawo aukar video sirri akan su a lokacin da suke kan aiki. Imran nada ha uri da sanyin hali, amma akan Zak-Shadow bashi da ha uri da kawaici. Dan haka cikin tsaurara harshe a karo na farko ya ce, Sir! Akwai makirci a wannan al'amarin kwarai da gaske. Eh naji kai tsaye zance Haysam baya cikin sansani tun daga ranar farko da aka kaima sojojinmu hari. Domin kuwa yazo ziyartar gida akan abinda ya shafesa, hakan kuma bawani abu bane a hukunce mun sani, musamman da idan mukai dubi da dalili mai arfi ne ke iya saka Haysam motsawa daga sansani, sai kuma ya tabbatar babu wata matsa sannan baya iya wuce kwana biyu duk tsanani Eh muma bamuce laifi yayi ba na zuwa gidan, sai dai miyasa ba'a kai harin ba sai bayan ya tafi? Kuma yanayin harin yay dai-dai da abinda ya faru shekaru uku da suka wuce. Aka sake kunna wani video da aka auka daga rikicin shekara uku da ta wuce, lokacin da Special Recon Unit ta jagoranci farmaki a yankin Gulmadu. Hoton ya nuna Zak-Shadow yana magana da sojoji, sai kuma a nan gaba aka ga wuta ta tashi, kamar umarnin harin daga gare shi ne. Wani kalar rinewa idanun Imran sukayi, sai dai kafin yay magana Colonel Galadima ya ce,........ _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ _Chapter 66_ __________________ https://chat.whatsapp.com/J92XqvWDRch1EJPdGDBa41?mode=wwt https://vm.tiktok.com/ZSHWHk4ULWbMN-geqJz/ This post is shared via TikTok Lite. Download TikTok Lite to enjoy more posts: https://www.tiktok.com/tiktoklite https://chat.whatsapp.com/KfkKd9vD8MrAst8i8CQDsj?mode=wwt Assalamu alaikum, Mutanen arziki Ina musu capacity kuna Neman Inda zaku Samu ingantattun Kaya masu kyau da quality sosai Kamar Kayan Yara Zannuwan Gado Kayan kitchen Shoes and bags Jewellery Laces, atamfa,shadda Dadai sauransu. To nesa tazo kusa, Maza Danna wannan link din domin Samun Kaya masu inganci da ayatarwa da idan kika saka ko ina kika shiga sai an kalleki an ara kallo. Ko ku nememu ta wannan number 08165751018 __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ........Yanda hankalin su Janar ya tashi a wannan ga ar har ba'a magana. Dan gaba aya komai ya juye a yanda basa fata kuma basa zato da tsammani. Ga takurawa da suke samu daga gidan gwamnatin. Dole a karo na farko kwamitin bincike ya aikama Imran takardar gayyata. Wannan takarda kuma ta riskeshi a dai-dai lokacin da yake fitowa zai zo gidan su Zak-Shadow domin dubashi da duba jikin Nimrah. Harda matarsa, sai Ru ayya da bataje makaranta ba jiya ta kwana da zazza in mura. Ai ko tanata murna zata ga sabuwar awar da Dada yace ya kawo mata. Komai Imran bai kawo ba game da wannan takarda ta gayyata, dan tunaninsa ma ai ana kan bincike ne game da su Dagger, yasan kuma za'a iya nemansu akan hakan. Suna shigowa gidan Zak-Shadow na fitowa daga sashen Mammah a zuciye, kallo aya yay ma motar Imran ya auke kai zai wuce. Imran ya san Zak-Shadow sani bana wasa ba, dan haka shima a kallo aya da yay masa ya fahimci akwai matsala, ko gama kashe motar baiyi ba ya alle murfin ya fito, cikin hanzari da arfin jini irin na masu ammara ya sha gaban Zak-Shadow dake gab da shiga sashensa. Kallon kallo suka zubama juna shi da Imran in. Cikin fushi Zak-Shadow ya ce, Bani hanya Mi kake shirin yi? Zan bigeka na wuce Sai dai ka bugeni in, amma in dai sai na matsa ka wuce bazaka shiga sashen nan ba. Sannan ina ro onka ka ara ha uri akan wanda kayi jiya. Nasan an maka ba dai-dai ba Haysam, amma ka dubi Uncle Nasiru ko dan nagartarsa ka yale yarinyar nan da halinta. Kasan mita sake min ne? Kayi ha uri indai ba wani raunin ta sake jima wani ba. Haysam Please ina ara ro onka kada ka biye mata ku zama aya. Ka barta ita da kanta zatai dana sani wataran Bazan iya cigaba da zama da ita ba Dan girman ALLAH kar kace haka, dan dama abinda nafi tsoro kenan fiye da komai. Kai jigo ne ga wannan gida, abinda kayi zai zama mai sau i wajen koyi gasu Ja'afar. A wasu lokutan idan mata suka kuskure mana, ba rabuwa da su bane mafita horasu a cikin gidan ne mafita. Karka manta kaine kake min wannan hu ubar fa. Miyasa yanzu idanunka zai rufe? Ita dai bata isa sakaka sakin Nimrah ba, ta dinga kallon yarinyar kawai a matsayin matarka duk da arancin shekarunta ya isheta hukunci mai zafi da zai fi kowanne. Amma dan ka rabu da ita ai tamaci nasara kenan Kallonsa kawai Zak-Shadow yake yi, amma ya gagara sake cewa komai. Sai dai har yanzu zuciyar na'a ma oshi, bai kuma gama tantance amsar kalaman Imran in ba ko in amsar. Dai-dai nan Ru ayya da basu san da zuwanta ba ta kama hannunsa cike da farin ciki tana fa in, Dadana nazo Idanu ya lumshe a hankali, sai kuma ya juyo yana kallonta, yanda yarinyar ke masa murmushi cike da farin ciki sai shima bai san ya mata murmushi ka an ba, sai kuma ya auketa gaba aya yana sauke ajiyar zuciya. Batare daya sake kallon Imran ba ya juya sashen Mammah. Imran ya girgiza kai yana murmurshin shima. Dan ya tabbatar badan zuwan Ru ayyan ba da wahala ya fasa shigar. Shima bayansu yabi, dama matarsa harta shige. Ba aramin farin ciki Mammah tayi da ganin Zak-Shadow ya dawo ba, ta sauke ajiyar zuciya idonta akan Imran. Dan ta tabbatar badan zuwan nashi ba za'ayi mara da i ne yau a gidan. Murmurshi Imran yayi shima, cikin girmamawa yay mata nunin ta kwantar da hankalinta. Cikin jinjina kai tace, ALLAH yay muku albarka Da Amin ya amsa yana hararar su Ma'aruff da suka tuttura baki alamar basu so ba, sun so yau Dadansu yaci aniyar Nabeeha ne wlhy, amma Yaya Imran ya hana. Garga i ya shiga musu da ido, dan haka suka ha e hannaye alamar ban ha uri. Daga nan suka maida hankali akan Aunty Hafsat matarsa dan an gidanta ne sosai. Hasalima shi Ja'afar anwarta zai aura mai suna Shariffa. Ma'aruff kuma anwar su Imran ce sunanta Lailah. Dada kam tunda ya shigo bai kula kowa ba dama, kai tsaye inda Nimrah take ya nufa, itama hankalinta nakan Ru ayya tunda suka shigo. Itama Ru ayyan hankalinta akan Nimrah yake. Dada na ajiyeta kuwa ta koma kusa da ita ta zauna, cike da farin ciki ta ce, Dada itace wannan? Kansa ya aga mata yana kallonsu su duka, dan daga gani hali
Chapter 87 · 0% Book details