Sashe 45
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
bayan wucewarsa. Da kuma sa on daya dinga aiko musu da baya zuwa hannunsu. Kwanansa aya a garin kano ya shiryo yazo Abuja. Ranar yaci kuka da takaici kwarai da gaske, ya rantse ya maya akan sa on da ya dinga aikowa garesu ta hanyar wani abokinsa, saboda tunda ya tafi hankalinsa na kansu ne. Sai gashi koda yasa aka nemo wanda yake bama sa o ashe shi yanata hidima ne da abinda yake aikoma marayun ALLAH, takaici ya saka shi sawa a rufe shi, sai da yar daban ha uri ya bari aka sake shi. Amma duk da haka sai da Zak-Shadow yasa aka cimasa ubansa ta bayan fage dai-dai gwargwado. Dawowar Uncle Nasiru ta sake canja rayuwar Mammah da ahalinta zuwa ni'imtacciyar rayuwa, duk da Alhamdullah dama zuwa yanzu basu tare da kowace damuwa. Dan sana'arta ma tayi girman da a yanzu har shago suke da shi a ofar gida da Zak-Shadow ya gyara musu. Karatun yaran kuma duk yana tafiya yanda ya kamata. A wani weekend da Zak-Shadow yazo ya samu babbar iyar Uncle Nasiru a gidan tazo hutu. Yarinya yawa son kowa in wanda bai samu ba, sunanta Nabiha, girman turai rainon biscuits da madara. Ga ilimi ga shagwa a ga gata. Tunda ta yalla ido akan Zak-Shadow ta kafa ta tsare tace tayi mijin aure. Ko damuwa da sharetan da yake ma batayi, dan ita ba komai ma yaja hankalinta a kansa ba sai wannan jin kan nashi da tarin izza da nutsuwa. Harga ALLAH tana matu ar son namiji maiji da kansa da kamun kai. Da in da awa ga jarumta, dan ko makaho ya shafa Zak-Shadow yasan sojan ne na gaske ba wasan yara ba. Ga yawun ga gayu ga ilimin addini. Kannensa na girmamashi tamkar mahaifi a garesu. Mammah kanta na ji da shi sai dai bata nuna wa saboda kawaicin an fari. Babu wani kunya ko tsayawa jan aji tace tana so shi. Shi kuma a take yace mata no. Shi bashi ma da burin aure nan kusa. Aiko ta sanya rigima harda kai ararsa wajen Mammah. Mammah kuwa najin wanga batu ta hau ta zauna abinta. Dan dama kullum cikin tunanin ta yanda Haysam zai nema auren mace take yi. Dan ta kula sam hankalinsa baya akan auren, ga Imran har an kai ku in nashi auren shi, hakama Ummi yayan Imran ya kafa ya tsare yana sonta. Ko tsayawa yin shawara da shi batai ba ta sanar ma Uncle Nasiru. Shima ba karamin farin ciki yayi ba da hakan, sai dai mahaifiyar yarinyar ta nuna bata so, a ganinta su Mammah talakawa ne sannan aikin soja ma kamar wani aikin wahala ne. Dama kuma a tsakanin tanata faman tafka tsiya da Uncle Nasiru in akan su koma asar waje ita bazata iya zaman Nigeria ba shi kuma yace ya dawo asarsa kenan, sai kawai wannan batun auren Zak-Shadow da arta ya ida tunzurata suka rikice har ya sake ta. Ya kuma aurama Zak-Shadow Nabeeha, dan itama dai ta bijirema uwar akan itafa babu gudu babu ja da baya. Haka takaici ya saka uwar tattarawa ta tafi ta barsu shi da arsa, ta wuce da sauran anen Nabeeha in guda biyu. Shi ko Uncle Nasiru ya ara sabon aure. Anyi bikin harda na anwarsa Ummi da Secondary kawai ta kammala, aka kaita gidan su Imran itama.. Matar Zak-Shadow kuwa anan gidan Mammah aka ajiye amarya, dan gefensu ka an aka yanki fili shima akai masa gini. Zak-Shadow bai fahimci son Nabeeha yake ba shima sai da akai musu aure, dan cikin anin lokaci suka ulle. Wata irin soyayya suke ma juna mai tsayawa a rai da zuciya. Sai dai a zahiri baka isa kace hakan ba saboda yanda shi gogan ke kame kansa. Shima Imran anyi nashi bikin da amaryarsa. Anan kuma cikin anguwar su Zak-Shadow yay ginin gidansa mai yau aka sakata. Rayuwa ta cigaba da tafiya nasarori na cigaba da zagaye Zak-Shadow, arin girma akai-akai har UBANGIJI ya addara a 2003 ya zama Captain, a Kuma lokacin wani sabon guguwar rikici ta taso a wani yankin asar, an turasu matsayin naya a, turawar data basu nasarori masu yawa har takai sun kada rundunar an ta'addan wanwar, suka samu arin girma kuwa Zak-Shadow ya zama Major. A 2006 kuma rikicin ya sake sauya salon da aka sake turasu wannan jejin dai sai dai a wani yankin ne daban, a inda suka ha u da wa an nan mata harda mace mai ciki da tai masa al awarin bama anta. Ya kuma tabbatar mata zuwa ya amsa da hannunsa. Zak-Shadow ya matu ar taka rawar gani a wannan jeji shi da maya ansa, dan kuwa ya hana an ta'addan kowane irin motsin kirki koda na numfashi mai arfi ne. Sannan ya da ile ha o ma'adanan da ake a tsakanin auyukan wanda kowa ya tabbatar da saboda su ne ake haddasa rikicin dan masu ibarsu su samu damar diba cikin salama a lokacin da su al'ummar auyukan yankin keta rayuwarsu. Sai kuma wata babbar kasuwa dake ata wajen data ha a kasuwancin wasu asashe itama aka tarwatsata domin cimma wani buri da manufa. Amma zaman Zak-Shadow da yaransa komai ya canja daga yanda yake. Ya sake samun arin girma zuwa Lieutenant Colonel a 2010, har kuma a yanzu 2013 yake a matsayin tare da rundunar maya a a wannan jejin dai da suka samar da zaman lafiya bisa girma da udirar UBANGIJI. Zuwa yanzu kuma anensa mata duk sunyi aure Biebah ce kawai a gabansu. Mazan dai bayan shi babu wanda ya sake aure, kuma har yanzu matarsa bata haihu ba.... Wannan kenan. ________________ A CIGABA DA GASHI..... 2013... Sosai Zak-Shadow yasha barcinsa, dan bai farka ba sai kusan goma da rabi. Har lokacin kuma da alama babu wanda yasan yana gidan bayan aninsa Bilal. Wanka yay ya kimtsa cikin shigar kamala duk da kuwa ananun kaya ne na shan iska a cikin gida. Hankalinsa nakan mahaifiyarsa Mammah, dan haka bai ata lokaci ba ya fito. Gaba aya falon ya kacame da surutu, yara ne ammata da zasu iya kaiwa shekaru 17-20-25. Suna akan dining table kowacce kayan barci ne a jikinta. Wata mata da ba tsohuwa ba kuma bazamuce yarinya bace tsaye a dining in tana zuba musu abinci a plates in gabansu. A mistake ta an zubama yarinyar dake kusa da ita da zata iya kai shekaru 20 suger akan waya data ajiye saman table in. Ji kake tasss saukar mari na bazata a fuskar matar, ba kowa bane kuwa da wannan aiki sai wannan yarinya. Cikin acin rai da masifa ta ce, Amma ke wawiya ce ko? Dan jakanta a kan wayata ma zaki zuba shuger salon ya shiga min speaker in waya Jikin mai aikin na rawa idannunta cike da walla ta shiga girgiza kai hannunta dafe da kumatu. Dan ALLAH Aunty Amima kiyi ha uri, wlhy kuskure aka samu.... Uwar kuskure ba kuskure ba jaka kawai ba auya. Dalla tashi min aka kona watsa miki ruwan shayin nan a wannan ba ar fuskar taki mai kama da daddawa Da sauri mai-aikin da har hawaye sun fara ma gudu a fuska tai yun urin barin waje. Yayinda sauran ke dariyar eta da izgili wai Amima ta kirata mai ba ar fuska kamar daddawa. Koma ki rama!! Razananniyar muryarsa dake a bu e kuma a dake irin ta jaruman maza tsayayyu ta ratsa kunnuwansu. Ta kuma saka mai aikin sake rikicewa da daburcewa amma ta tsaya cak. Haka suma yaran a mugun zabure duk suka mi e jikinsu na mazari, sai kuma duk suka zube asa du e suna fa in, Dada sannu da zuwa Idan kujerun dining in sun tanka ya tanka, hasalima ko kallon inda suke baiyi ba. Mai-aikin ya sake tsarewa da idanu cike da bada umarni ya sake furta, Baki jini bane? Hawayenta ta share da sauri tana jinjina kai, ta ce, Naji Dada kayi ha uri, amma na yafe mata Ni kuma ban yafe ba, kar kuma ki bari na sake maimaita abinda na fa Sosai Hinde mai aiki tasan wanene ubangidan nata, dan kuwa shekaru kusan hu e kenan take zaune a gidan tana aiki. Ai baima gama rufe baki ba ta isa gaban Amama. Ji kake auuuu! Tasss-tasss! Na saukar marin data rama, har sai da Amama ta tuntsura zata fa ara mata Ya sake fa a cike da umarni. Haka Hinde ta sake saukema Amama mari na biyu daya sakata walla arar azaba. Dan da alama itama dai Hinde ta da e tana fatan wannan ranar, shiyyasa ta bu e kwanji ta sauke ma fuskar Amama duk wani takaicinta. Cike da sassarfa wata mata ta fito a wata hanya tana fa in, Mike faruwa? Wa yake kuk...... Cak ta tsaya batare data iya arasa abinda ta faro fa ar ba sakamakon saukar idannunta akan wanda batai zaton gani ba. Shi ko tamkar ma bai san ALLAH yayi ruwanta a wajen ba yayi wani kicin-kicin da fuska yana danna waya hankali kwance. Ga Amama tasa hannu ta danne bakinta dan kar kukan da takeyi ya fito, dan inta bari hakan ta faru lallai zata gwammaci Hinde taita marinta fiye da hukuncinsa. Jiki a sa ule matar ta araso inda yake, itama dai bazata wuce 30years ba, sai dai daga gani kasan anaji da gayu sosai. Cikin kame kai da aro nutsuwar dole ta ce, Sannu da zuwa My D! Shigowar yaushe haka babu labari? Maimakon amsa maganarta ko kallonta ma baiyi ba. Sai da yaja iska tafi ta minti aya batare da ya kalletan ba ya furta, Su tattara su wuce gida . Daga haka ya mi e abinsa ya fice a falon gaba aya. Sororo ta bishi da kallo zuciyarta na bugawa da sauri-sauri, haka suma yaran gaba aya firgici ya bayyana akan fuskar su. Balle Hinde da take jin har fitsari ya fara iga mata a jiki, dan tasan uwar akin nata sai ta huce a kanta, itace zata sha wahala bayan ya koma. Yana gama ficewa ta afka kitchen da tafiyar baya-baya. Su kuma ammatan suka zabura kan Nabiha suna hawaye......... _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My