← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 94

Sashe 74

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

goyon baya saboda wani burinta na banza da wofi. Kasancewar Ma'aruff ya iske Dadan su na wanka sai da ya jirashi, dan haka kusan lokaci aya suka shigo falon Mammah da Uncle Nasiru. Suna zama Imran na shigowa. A can kuwa Biebah dake kitchen tana aiki taji komai tuni ta fice can baya tana kuka ta kira Aunty Ummi da Aunty Mommy da ma Aunty Mimi ta gaya musu abinda ke shirin faruwa. Ai tuni suma kowa ya akko hanyar zuwa gidan. Yo ubanwa ya isa ta a musu Dada a zauna lafiya ba'atada ya in duniya na uku ba. Ai wlhy Mammah ce kawai keda wannan isar, itama dan uwa ce babu yanda zasuyi da ita. Duk wannan abin dake faruwa Bilal baya gidan, ya tafi saka Nimrah a islamiyyar su Mu'azz, boko ma in sha ALLAHU gobe-gobe za'a kaita. Dan tunda Mammah ta gama jin komai a wajen Zak-Shadow ta yanke shawarar a yau in nan za'a saka Nimrah islamiyya gobe boko ko hakan zai sa ta saki jikinta. Dama gashi anyi sa'a cikin satin nan aka koma hutu kuma zangon farko ne. Tunda Zak-Shadow ya shigo falon yaji zuciyarsa ta sake zuwa wuya. Da yar ya iya daurewa ya gaida Uncle Nasiru ya samu kujera ya zauna, tare da jingina bayansa ya lumshe idanunsa kawai yana sauraren zagin da Uncle Nasiru kema Nabeeha da ke neman komawa fa a tsakaninsa da Momynta data saka baki. Sai da Mammah ta basu ha uri da nuna musu kuskuren abin kunyar da suke neman yi agaban yara sannan sukai shiru kowa na huci. Dai-dai nan Imran ya shigo da sallama shima. Kai tsaye ya araso falon dan shima an gida ne, har bedroom in Mammah shiga yake. Yanzu ma sai da ya gaida su ita da Uncle Nasiru da Momyn Nabeeha su Ma'aruff suka gaisheshi shima. Da ido Mammah taima su Ma'aruff in umarnin fita a falon. Badan sun so hakan ba suka fita. Amma sun san duk rintsi Mammah bata maganar data shafi Dada a gabansu in har bata farin ciki bace, amma a ganinsu wannan tasha banban ai, sai dai duk da haka an kora su waje. Bayan gama fitarsu da rufe ofa suka koma jikin windows suka ma e, dan sun fi son jin komai yanda zasu ci aniyar Nabeeha da lasisi. Mammah da bata san suna la e ba kai tsaye ta maida kallonta ga Zak-Shadow. Muhammad Ta kira sunansa kamar yanda ta saba. Idanunsa da suka rine ya bu e, sai kuma ya gyara zamansa cike da girmamawa ya amsa mata. Miya ha aka da matarka haka da zafi har kake zaginta da korota daga akinka cewar zaka daketa A karo na biyu ya an juya ya kalli sashen da Nabeeha take manne da Momynta, sai kuma ya dawo da kallonsa ga Mammah. aramin murmurshin takaici yayi, mamakin wannan arya ta Nabeeha na cizonsa, amma sai ya danne, cike da girmamawa ya ce, Tazo min da wata maganar banza ne akan yarinyar nan da kuka taho da ita daga asibiti Mammah A gani na ai bayani ya kamata kai mata ba kakkausan lafazi ba..... Miye wani kakkausan lafazi zagi dai. Momyn Nabeeha ta katse Mammah a hasale. ALLAH kika ara magana sai kin bar falon nan . Cewar Uncle Nasiru yana nuna Momyn Nabeeha. Itama a hasale ta ce, To ubana Dan ALLAH kuyi ha uri Yaya . Mammah ta fa a cikin tausasawa, sai kuma ta cigaba da fa in, Muhammad ita yarinyar wacece a wajenka? ar waye? Miyasa kazo da ita nan? . Ta jera masa tambayoyin duk da kuwa ita ya mata bayanin komai azun.. Iska ya furzar mai acin gaske, dan haka Imran yay saurin fa in, Mammah bara nai muku bayanin komai Ai bakai aka tambaya ba Momyn Nabeeha ta fa a tana hararar Imran. A hasale Uncle Nasiru ya ce, Shine kuma zai bada amsa, kai Imrana fa i muna jinka. Kai Imran ya jinjina ma Uncle Nasiru yana gyara zama. Yayin da a jikin Windows su Ja'afar kejin kamar su tsallako falon su daki bakin Momyn Nabeeha, dan zuwa yanzu suma su Aunty Ummi sun iso, tuni kuma su Ma'aruff sun musu bayanin komai dan haka suka nema wajen ma ewa suma ayi komai da su. Wannan yarinya sunanta Naja'atu, amma iyayenta na kiranta Nimrah saboda sunan kakarta taci........... tsaf Imran ya zayyane musu komai, sai dai banda ainahin halin da mahaifinta ke ciki, hasalima kamar yanda Umma ta ro a sai ya sanar musu mahaifinta ya rasu a rikicin kamar mahaifiyar tata. Ba aramin da in hakan da yayi Zak-Shadow da Mammah sukaji ba. Dan ita Mammah komai sai da Dadan ya sanar mata bai oye ba. Cikin damuwa sosai Uncle Nasiru ke jimanta al'amarin, da tsakanin jin tausayin Nimrah a ransa. Amma a mamakin kowa sai ji sukai Nabeeha ta ce, Wlhy ban yarda ba, Imran kai dama ai munafuki ne nasani, tun ba yau ba nasan ba aunata kake yi ba. Banda ma rainin hankali in har da gaskene abinda ka fa in ai ba ita ka ai bace aka kashewa iyaye, miyasa su sauran yaran kuka barsu can ita kuka taho da ita nan. Ba sai ku barta acan camp in ba kamar sauran. Ni wannan labarin anzon kuregen bazan ta a yarda da shi ba, dan dama na jima ina zargin ana cin amanata, idan har ana son na yarda ba arsa bace sai dai muje asibiti ai musu gwaji shi da ita..... A matu ar fusace Zak-Shadow ya mi e, cikin bu iyar muryarsa dake fita da kaushi da aci ya nuna Nabeeha, Baki isa ba, kinyi ka an wlhy. Kije labarin aryar aka baki, kuma ana cin amanar taki kiyi duk abinda zakiyi, dan ke baki isa sakani yin abinda banyi niyya ba wawiya kawai A fusacen itama ta mi e tana kuka, kai da ka ganta kasan kishi ne da zuga suka rufe idannunta, itama cikin araji ta ce, To wlhy kuwa sai dai mu rabu, dan nima baka isa na cigaba da zama da kai ba. Jaka ka auke ni ko dabba?, shekara da shekaru ina fama da kai muje muga likita akan matsalar haihuwa amma ka i saboda kasan mi kake shiryawa, kaje ka ajiye wata ar iska a jeji kana dadiro da ita ku haihu dan yanzu an kasheta ka akko ar ka kawo gida mu sha i iska aya da ita, mu kwanta muhalli aya da it..... Tasss! Tasss!!! Kake jin saukar mari har biyu a kan fuskarta irin mai gigitarwar nan, ai ko ara ta walla, dai-dai da mi ewar Momyn ta ta ri eta tana shiga tsakkaninta da Uncle Nasiru mai marin........ Gaskiya awata Nabeeha baki yauta ba, ya zaki mana haka kuma _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ _Chapter 56_ __________________ https://chat.whatsapp.com/L3BXH7JYlBRHIkFRiOjeW3?mode=ems_copy_t UMMU KHALIFA COLLECTION Ina Mata Yan kwalisa ina mata masu san kayan ado kamar Egyptian abaya sleeping drees kids were shos bags musk dahara original. To kukanku yazo karshe domin ummu khalifa sun zo muku da duk wadannnan kayan dierct suke order dinsu daga Egypt zuwa gida Nigeria kaidai kawai kashiga link dinsu domin gani ya kori jiii.. Ba nan ummuh khalifa suka tsaya ba suna nemawq mutane visa masu shaawar shugowa kasar ta Egypt karatu ko yawon bude ido ko kasuwanci ku tuntubeta a number dinta +201017018846/07048811474/ KO kuma shafinta na tiktok https://vt.tiktok.com/ZSU1F __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ .......... Miyasa zaka mareta? Naga akan gaskiyata take dai ai? Sai a daki yarinya a hanata kuka. Idan yasan yana da gaskiyar mizai sa ya i yarda suje suyi gwajin? Cikin kuka Nabeeha ta ce, Momy ki barshi ya kasheni, Abba ka kasheni, dama mun san ai ba son mu kake ba yanzu, shi da yay laifin ka kasa yimasa magana saboda kana tsoronsa sai ni, sai ni da nake da gaskiyata za'a tauye ni...... Wani marin ya ara kawo mata, dan yama kasa magana saboda abinda ya tsaya masa a ma oshi. Da sauri Momyn tata dai ta sake tarewa. Wlhy bazaka sake dukanta ba Mammah da al'amarin ya girmi kanta ma sai yanzu ta iya aga baki da yar tace ma Uncle Nasiru, Dan ALLAH Yaya kayi ha uri ya isa hakan, duka ba shine mafita ba, ku barta ta huta ta huce dan yanzu shai an yayi tasiri a zuciyarta. Sannan kuma tunda gwajin take so ni zan masa magana zaije suyi, ba shike nan sai a zauna lafiya ko A gatsine Momynta ta ce, Da dai yafi kam . Taja hannunta suka nufi ofa. Gagara sake yin magana kowa yayi a falon, dama Zak-Shadow tunda ya gama ya ata zancen farko ya koma can dining ya zauna, ya i fita ne dan kar ya atama Mammah rai, Uncle Nasiru kuma yaga kamar ya raina shi, dan kallon uba yake masa. Amma ya tabbatar ya cigaba da zama inda Nabeeha take zai iya fara kai mata duka a karo na farko na rayuwarsu, shiyasa ya za i komawa can ya zauna in... Salatin da Mammah ta saki ita da Imran a lokaci guda ya sashi bu e idanunsa ya kallo falon, ai baima San ya mi e ba da sauri ganin Imran ya taro Uncle Nasiru alamar fa uwa zai yi. Ganin Uncle Nasirun na neman sumewa ya i ruwan da Mammah ta mi o da sauri, alle murfin yay kawai ya zuba a hannu yana kaiwa du e shima ya
Chapter 74 · 0% Book details