← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 94

Sashe 31

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

zai wuce yakan gaisheshi, wani lokacin kuma yakan gansa tsaye can nesa yana kallonsa, a farko ma ya dinga tsarguwa ko aiko yaron ake ya cutar da shi, sai daga baya ya fahimci sam ba haka bane, hasalima ba rumfarsa Haysam ka ai ke la ewa yana kallon abubuwa ba harda wasu rumfunan na abokan kasuwanci. Yau koda Haysam yazo ya gaida shi sai ya dubesa da murmushi. A'a an baba dama kai an makaranta ne amma kullum kake zuwa kaita yawo a kasuwa? Haysam baida yawan magana, amma akwai ladabi da girmama manya, gashi yaro akwai na tsuwa. Cike da ladabi ya ce, Baba yau ne na cigaba da zuwa makarantar dai, da ba'a nan nakeyi ba Malam Zakiyyu ya ce, Oho to ALLAH ya bada sa'a, sai a dage da karatu kaji, ALLAH yayi maka albarka. Kaga ga wannan maza kaje gida kar Innarka ta nemeka ko Kallon ku in Haysam yayi, maimakon ya amsa duk da yasan suna da bu atarsu, amma sai ya girgiza kansa da fa in, A'a baba na gode ba ku i nake so ba, da dai zaka min wani taimako Cikin mamaki Malam Zakiyyu ke kallonsa, amma sai ya danne ya ce, Wane irin taimako an Baba? Kai tsaye Haysam ya ce, Idan na dawo makaranta ka dinga kasa min kayan nan ina talla cikin kasuwa, idan na sayar na kawo maka ku in sai ka bani hakkina Ba Malam Zakiyyu ba hatta ma wafcinsa Malam Datti sai da ya tsaya yana kallon Haysam, gashi yaro arami da bai wuce shekara sha hu u ba amma a nutse yake, ga magana kuma irin ta masu dattako a tare da shi. Malam Zakiyyu yayi murmushi, tare da shafa kan Haysam ya ce, ALLAH yay maka albarka, amma yaro ina iyayen ka? Sannan miya baka sha'awa da yin hakan? Bayan kai an boko ne? Shiru kamar Haysam bazai ce komai ba, da alama baya son fa ar abinda ke zuciyarsa, amma kuma baya son yima Malam Zakiyyu arya, bayan ya jinjina abinda zai fa ar a zuciyarsa ya ago ya kalla Malam Zakiyyu. Baba ni mai neman ilimi ne, iyayena kuma Mammah ta ce kawai, Babanmu ya rasu. Ina son nayi wannan sana'ar dan na taimaki Mammah ne da annena suma su dinga zuwa makaranta kamar yanda nake zuwa Sosai Malam Zakiyyu ke kallonsa, idanunsa kuwa na cika da wallar tausayi, sai kuma aunar yaron ta kamashi. ALLAH yay maka albarka yaro ya sunanka? Haysam! Mammah na kirana Muhammad, Babana yace dani Zakinsa Tabbas gaskiya mahaifinka ya fa a kai zaki ne Muhammad Haysam. A ina gidan naku yake? Anan bakin kasuwa ne baya ka an, gidan kakarmu ne Inna mai Koko Malam Zayyanu daya an shiga nazari ya ce, Ko gidan su Bashir? Dan ana kiran mahaifiyarsu da Inna mai-koko Eh nan, kawuna ne ALLAH yay maka albarka Haysam, kaje gida yanzu, gobe idan ALLAH ya kaimu kazo zan fara kasa maka kaya Wannan kalma taima Haysam da i, dan kuwa a karo na farko su Malam Zayyanu suka ga murmushin sa, cike da farin ciki ya nufi gida, ya iske Mammah ta kammala wanki tana saurin shirin tafiya gidan aiki dan ta isa da wuri saboda a afa take zuwa sai ta dawo a abin hawa, wata rana ma idan babu ku in a asan take zuwa ta dawo a asa, afafunta duk sunyi fashewar faso, haka hannunta duk yaja ruwa saboda azabar wanki, amma bata damuba, yaranta dai suyi farin ciki shine matsalarta.. Kayan makaranta kawai Haysam ya cire yayi wanka ya zauna cin abinci batare daya gayama kowa ba, Inna na masa hira shi dai nashi saurare, idan kuma yaso ya bata amsa, amma amsar tafi yawa a uhhmm ko eh ko a'a. Kwatsam bayan sallar magriba saiga mahaifin su Nasiru ya shigo gidan yake sanar da Inna cewar wani ba one keson yin magana da su iya da A'isha. Abin bai ba Inna mamaki ba, dan kwana biyun nan mutane keta aikowa akan suna son A'isha da aure amma tace ita ba aure ne a gabanta ba yanzu yaranta ne. Itama Inna kuma batace mata komai ba dan tasan gaskiya ta fa a, ina zata tabar wa an nan a har takwas duk ananu?, waye kuma zai yarda taje masa da su gidansa?. Har A'isha taso in zuwa dan tasan irin masu zuwa neman auren nata ne Inna dai ta matsa mata suka fito soron. Sai dai kuma bayan sun gaisa da ba o daya kira kansa Malam Zayyanu ya bu aci a kira Haysam. A'isha da kanta ta le a ta kirashi yana tsakar gida yana sakama su Ummi da yayma wanka da kansa kaya. Koda ya fito yaga malam Zayyanu sai tsoro ya bayyana a fuskarsa, ya saci kallon A'isha ya saci kallon malam Zayyanu. Malam Zayyanu na lure da shi, sai yaron ya bashi tausayi ya kuma sake birgesa dan ya fahimci yana tsoron acin ran mahaifiyarsa. Cikin hikima ta manya sai bai fito fili ya sanar dasu yanda sukai da Haysam ba, ya nuna musu hankalinsa da nutsuwarsa ne yasa shi da kansa yake son Haysam ya dinga zuwa yana koya masa sana'ar da yake ta kayan koli da gyaran agogo. Haysam ya sauke oyayyar ajiyar zuciya, yana tsammanin Mammah zatai farin ciki sai yaji tace a'a sun gode sosai, amma Haysam karatu yake yi kuma tana son ya nutsu a karatun kawai. A firgice Haysam ya kalleta, sai kawai suka ga yazo gabanta ya dur usa yana ro on ta barshi shi dai yana so. Koda ta masa tsawa bai fasa ro on nata ba, amma A'isha ta i. Daga arshe zata tashi tabar soron ma Baban su Nasiru ya dakatar da ita. Shine yay mata nasiha da nuna mata illar abinda take son yi, ya kuma tabbatar mata yasan Malam Zayyanu shekaru da yawa, sai a lokacin Inna itama tasa baki, da yar sukaci kan A'isha ta amince. Sai dai Haysam yasha harara dan ta fahimci koma minene da saninsa. Aiko bayan wucewar Malam Zayyanu ta tirke Haysam a aki, bai iya arya ba, dan haka ya sanar da ita komai. Sai kawai ta kamashi ta rungume tana hawaye. Wannan shine mafarin fara gwagwarmayar rayuwa ga Haysam Abdul-rasheed Shehu, ko da yake arami ne, ya auki nauyi fiye da shekarunsa. Yakan tashi da asuba ya ebo ruwa ya cika ko'ina da ruwan saboda yasan Mammah zata nema na wanki, sannan yay shiri ya tafi makaranta. Dama da kayansa na gida a jaka, da'an taso daga can zai wuce kasuwa wajen Malam Zayyanu, ya canja kayansa ya auki tallar an kunne na mata da an kayan koli irin su jambaki, masilla, allura, an kunne, hoda, kwalli, madubi da sauransu. Tausayinsa kesa Malam Zayyanu saya masa fura ko abinci, amma sai ya i ci sai ya matsa masa zai tsakuri ka an ya tashi ya wuce tallarsa. Haysam da ari, cikin ikon ALLAH kafin la'asar sai dai ya dawo da tiren, ko da kaya ka an, ayi lissafi a bashi ha insa ya auki jakarsa da ku in sai gida. Idan ya tarar da Mammah ya bata, idan ta tafi wajen aiki ya bama Inna yayi shirin tafiya makarantar allo shida annensa. Ba'a nan Haysam ya tsaya ba, wani lokacin sai dare yayi su Inna sun kwanta da wuri musamman A'isha da ba doguwar hira take ba saboda wahalar kai-kawo sai ya kwaso wankin da ake kawo mata wankau ya hau yi, sai dai kawai su tashi da safe suga kaya fululu a shanye a igiya abin mamaki. Ranar farko da A'isha tai masa fa a sai Inna ta kwa eta, dole tai shiru, Ganin haka sai ya cigaba, sai dai idan Mammah ta oye kayan ne babu yanda zai yi dole ya ha ura, ita kuma tana masa haka ne saboda tasan aikin yafi arfinsa balle ma wanki, dan ma yaro ne mai juriya da ari. Ganin ga yanda ALLAH ya saka albarka a tallar tasa sai ya fara an asusu, a cikin sallamar da Malam Zayyanu ke bashi ya dinga ajiye wani abu, da suka an taru ya sai Rula, fensil, biro da ire-iren su kayan karatu ya zuba a jakar makaranta, idan yaje sai ga dinga yima yara talla a oye yace musu yana sayarwa, tun ba'a gane shi ba har aka gane yaran suna saye. Wani mugun malamin su yayi arin hanashi amma h eadmaster yace a barshi hakan abu ne mai yau, balle kowa yasan Haysam da wazo baya wasa da karatu. Ga arin zuwa makaranta akan lokaci, da wahala ka kamashi da latti ko wani laifin fa a da wani. In dai kaga yana fa a an ureshi ne gaskiya. A duk lokacin da Aisha ta kalle shi, sai ta tuna da mijinta. Tana ganin arfinsa, nutsuwarsa, da hakurinsa a cikin anta. A lokacin da wasu yara ke wasa da keke ko tsere, shi kuma yana zaune a ashin bishiya yana karatu cikin shiru ko kasuwa cikin zafin rana ko ruwan sama ko sanyi yana yawon talla, a makaranta ma bai huta ba, yazo gida kuma ya tadda hidima, dare lokacin barci amma shi arin rage mata wahalhalu yake dan ita ta huta. Sai dai babu abinda zatace da UBANGIJI sai godiya, domin kuwa da wannan neman na Haysam take hidimar karatunsa data an uwansa, na aikinta da wankau kuwa suci abinci. Ana haka su Bashir suka kammala karatunsu suma suka dawo gida, tana murna mataimaka sun aru sai labarin ya canja, dan kuwa kai tsaye Bashir yace shi aikin soja yake so, shi ko Tasi'u da batun auren wata yarinya da sukai karatu tare yazo musu. Hankalin Inna ya tashi matu a da wannan batu nasu, suka dinga lallashin su ita da A'isha amma babu wanda ya saurare su. Burin Bashir bai damesu ba, dan kuwa aikin soja ta da e tana jin labarinsa a bakin Abdul-rasheed da yanda yake burin shima Haysam ya zama soja, dan yaso ma daga primary military school kawai Haysam zai yi Secondary insa, amma burinsa bai cika ba, amma ya barshi gine a zuciyar ansa dan har yanzu babu abinda Haysam keso kamar aikin soja, na Tasi'u mai aure yafi aga hankalinsu, dan kuwa wadda yake so ar masu ku i ce,
Chapter 31 · 0% Book details