← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 94

Sashe 20

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

sai kuma ya du a batare da ya amsa ba ya kamo kafa unta duka da hannu biyu ya mi ar da ita. Sake rungumeta yayi sannan ya amsa mata gaisuwa. Kafin ya rufe da fa in, Mutanen Kano duk na gaisheki harda gidaje da motoci. Gaisuwar Inna da tasu Tasi'u kuwa tafi rabin buhu Cike da farin ciki ta ce, Na gode! Amma miyasa Inna bata biyoka ba dasu Tasi'u. ALLAH kullum sai nayi kuka idan na tuna su In sha ALLAHU daga yau bazan sake bari hawayen kewar su Inna su zuba ba, zan dinga share su da murmurshi da farin ciki. Su Tasi'u kuwa karki damu zasu zo, Nasiru yace zai kawo miki su. Inna ce dai ba lallai anan kusa ba, ila sai kin haihu Ba aramin kunya kalmar sai ta haihun nan ta sakata ba. Dan haka bakinta ya mutu bata sake magana ba daga nan tama zame jikinta daga nashi dake mata da i kanta a asa. Tabarmar daya akko mata ta amsa ta shimfi a masa, shiko yana faman binta da murmurshi ganin yanda take ta faman sinne fuska dan yace zata haihu. Tsaff ta shirya masa abincin a tabarmar, shima sai ya zauna yaci dan yunwa yake ji sosai. Yaci ya oshi yasha fura. Itako daya mata tayi tace ta oshi bai takurata ba. Yana kammalawa ta kauda kwanikan, shi kuma ya hau zame kaya yana fa in, Saura wanka. Bari nai amfani da ruwan drum in can ila yafi umi, tunda naga da alama amarya bata fara girki ba a gidan nan har yanzu Inna tace ba yanzu ba Ta bashi amsa kanta tsaye. ar dariya yayi da fa in, ar gatan Inna kenan, wato ba yanzu ba Eh mana, sai na ara girma tace To Inna ta shirya kayan girki kam dan yau zaki girma Sam A'isha bata wani gane mi yake nufi ba. Shima kuma bai ara cewa komai ba ya fita. Koda tace bari tazo ta kai ruwan sai yace ya hutar da ita ta zauna ta jira shi... Koda Abdul-rasheed ya fito wanka samun A'isha yayi ta ingire barci, bai tadata ba ya saka babbar riga a jikinsa ya fita a gidan, bai wani jima ba ya dawo da ledar nama tsire sai amshi yake. Tadata yayi cike da lalla awa, zata fara masa shagwa ar ya barta ita barci take ji ya dai lallasheta taje ta wanko fuska. Naman ya bata yace taci. Da farko kunya ta hanata ci saboda shi. Ganin haka yasa shi fita ya bar mata akin, sai ta samu taci kuwa sosai, ta auki sauran ta ajiye gefe. Ta fito danta kuskure baki ta ganshi zaune a waje, mi ewa yay yana tambayarta mi take so? Tace zata wanke baki ne. Bakinta ta wanke da gawayi da gishiri kamar yanda Inna ta koya mata tun a gida safe da dare idan za'a kwanta. Shima sai ya amsa yayi duk da yana da brush shi kam, itama kuma ya sayo mata. Suna komawa aki A'isha ta kama gadonta zata haye. Ri o hannunta yayi, dan haka ta juyo, suna ha a ido tai maza ta du ar da kanta asa. Barci kike ji? . Ya tambaya cike da kulawa. Kanta a asa ta jinjina masa. Ya ce, Na baki gado na ki ana yau? A'a ga nawa nima zan kwanta anan, kaima sai ka kwanta a naka Miyasa ba ya so? Saboda kowa yana da nashi Toni nazo na ana naki? Ai bazai ishemu ba To shike nan ki hau nawa sai ki bani naki . Bai jira tayi magana ba ya auketa camak ya dire a saman gadonsa bayan ya ago labulen. Wani da i ya ratsa A'isha, a ranta tace (Ashe gadon da i ne da shi haka, kai miyasa ban ta anawa da baya nan ba) shi dai dake kallonta bai san abinda take ayyanawa ba ya ce, To kwanta sai da safe . Ya zuge mata labulen mai suna zuge shige. Aiko tana ganin ya rufeta ruf ta wani baje a gadon tana murmushi, ALLAH a kwai da i, ga taushin katifa gana zanin gado. Ga filo sun zagaye gadon reras har sha biyu gwannin sha'awa, ai saiga hajjaju matar Abdul-rasheed cikin an mintina barci yayi awon gaba da ita. Duk abinda take Abdul-rasheed na kallonta ta tsakanin labulen yana danne dariya. Sai da ya bari barcin ya mata arfi yaje ya rufe gida ya dawo. Duk abinda ya dace tayi matsayin matar gida sai shine yayi. Ya kashe fitilar wan su gaba aya dan baya son kwanciya da haske shi kam sam, sai dai akwai Torchlight a kusa da shi koda yaushe. Labulen ya aga ka an ya le asata, ganin yanda ta ararraje dole ya dara ka an yanzun kam. Dan da alama dai gadon nan ya lula da matar Abdul-rasheed ba arya. A haka ya samu ya hau shima ya gyara mata kwanciya, sannan ya zuge labulen suka koma ruff. Haskata ya anyi da fitila, da gaske barcinta take hankali kwance alamar bata da wata matsala, wato babu abinda yakai uruciya da i, ita yanzu bata san mi yake ji ba, shiko tsahon watanni yana azabtuwa a kanta. Hora kan nasa kuwa ya zame masa alkairi, dan tabbas da ya ta ata kafin tafiyarsa da bazai iya sati biyu a Kano baizo Bauchi ba. Amma gashi Alhamdullah har ya cika watanni shida ciff ya dawo garinsa na haihuwa dawowa ta har abada, inma da abinda zai sake biyo baya da zai sa ya fita bazai kai kamar wanda yayi a baya ba, duk da yana da burin sake zurfafa iliminsa again. A hankali ya sauke ajiyar zuciya, tare da kashe fitilar ya ajiyeta gefe ya gyara filo da yau shima ya kai kwance.. Cikin barci A'isha ta fara jin sa anin abinda bata ta a ji ba tsayin rayuwarta. Wato hannun mutum a jikinta a firgice ta farka tare da zabura ta walla masa ara. arar data sashi saurin ora hannunsa a saman bakinta ya rufe shi ruff, tare da kamota ya ri eta a jikinsa da yar tana fisgewa. Babu shakka da ace akwai wani a gidan sai ya jita, ALLAH ya soshi su biyu ne. Da yar ya tausata ta nutsu, bayan ya maimaita mata kalmar shine da Abdul-rasheed yafi sau goma kafin ta fahimta. A hakan ma bata nutsu ba ta saka masa kukan ita ta ha ura zata koma gadonta ta kwanta. Lallashinta yake da iya iyawa da kwantar da kai amma ta i fahimta. Shi ko yana cikin wani hali, dan haka ya fara mata nasiha da son fahimtar da ita da yaren da zata gane. Ina hajjaju bata gane in ba, daga arshe dai dole ya barta ta sakko a wannan gado kuwa, dan neman shi e masa take alamar dai ta riga ta tsorata da shi. A gurguje Please >>>>> <<<<< Wasa fa farin girki tsakanin Abdul-rasheed da A'isha, dan tun yana aukar al'amarin mai sau i harya fahimci baya samuwa cikin sau i. A washe gari wasan uya ta sanya da shi. Zuwa wani daren yana fita sallar magriba ta sulale itama tabar masa gidan. Koda aka idar da salla bai dawo ba sai da akai isha'i. Nan in ma Baba yabi gida duk dan ya bata dama ta yi barci cikin salama, dan ya fahimci yinin yau gaba aya a arare take da shi ko fara'a batayi ma har yara dake shigowa. Wajen arfe tara baba yace ya tashi yaje gida dare nayi. Haka yay musu sallama shi da Inna ya taho, koda yazo gida ya shiga aki wayam babu A'isha, sai yay tunanin taje bayi ne. Zaman jiranta yayi, duk da yayi mamakin ganin tiren abinci da aka aiko daga gidansu a ofar aki, sai shine ma ya shigo da shi ciki. Shiru-shiru babu motsin Indo, dole fa ya mi e ya fito tsakar gidan da Torchlight a hannu, ya gama haske-haskensa babu alamarta, arshe dai har bayin ma ya le a nan ma babu ita. Hankalinsa ne ya tashi, babu shiri ya fito ya nufi gidansu, abinka da ba wani nisa ba, dan can hankalinsa kawai ya bashi zata iya zuwa. Inna da Baba na haramar shigewa suma su kwanta ya shigo, da mamaki suke tambayarsa lafiya?. A ru e yace, A'isha. Naje gida ban sameta ba, na zata tana bayi ne sai dana ga da ewan yayi yawa na le a babu alamarta, ashe ma ban lura bane buta na nan a aki. Sosai hankalin Baba ya tashi shima, sai dai ita Inna abinka da mace sai ta tafi tunani. Ganin suna sallallami tace, Ku dakata, nasan babu inda zataje tunda ba wani waje ta sani ba daga nan dai sai gidajen an uwanka, kuma dai duk gamu a kusa. Bari mu fara duba nan gidan kota shigo . Inna ta amshi Torchlight in baba ta fara le akuna tana haskawa. Ilai kuwa sai ga A'isha a cikin yara su Alawiyya annensa da yaran ma otansu da suke zuwa kwana gidan tana sha ar barcinta hankalinta kwance. Inna ta ce, Yau ga ja'ira, ai gata nan tsakkiyar su Nana kuwa tana barci. Bara na tasota Lokaci aya shima Baba tunaninsa ya harba, dan haka yace, Kinga barta kada ki tasheta Karimatu. A'a ya zakace kada a tasheta Malam. Miye amfanin kwanciyar anan? Barta ke dai, kai jeka sai da safe Duk da ba haka Abdul-rasheed yaso ba bazai iya musawa ba, cike da ladabi yay godiya ya tafi ransa fal mamakin A'isha. Ya fahimci yarinyar nan so take ta a masa aiki dai kawai. Ashe labarin da abokinsu ya basu akan tashi matar data dinga komawa gida ma ita ana maidota kasancewar garinsu aya suna masa dariya ashe shima tashi Shatun jiransa take. Tir ashi akwai aiki kenan dai...........
Chapter 20 · 0% Book details