← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 94

Sashe 43

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 2 min read

sake fahimtar rayuwa ta canja ga mahaifiyarsa, ta tabbata dai bata tare da sabon mijinta. Sai dai yanzun ma bai tambaya ba saboda girmamawa har sai da Mammah ta sanar masa komai a wannan karon da bakinta. Tabbas zuciyarsa ta hasala matu a, amma bai ce komai ba dai a zahiri. Itama Mammah data fahimci yanayin nasa sai tai masa nasiha da garga insa akan kar taji wani abu daga garesa. An riga anyi ya wuce sai a tari gaba. Badan yaso ba yay shiru kamar yanda ta garga e san. A cikin wannan hutu ya samu damar bibiyar karatun anensa, har zuciyarsa kuwa ya gamsu da yanda komai ke tafiya Alhamdullah. Musamman ma su Ja'afar an Secondary. Ya ji da in kuma ganin yanda kasuwar Mammah tai tasiri a gida. Ya ziyarci Malam Zayyanu da abokinsa Malam Datti. Sun masa addu'a sosai da nuna jin da in nasarar da ya samu a NDA. Duk da yana cikin hutu bai daina yin motsa jiki da safe da yamma ba, kamar yadda suke yi a NDA. Wani lokacin idan yana fama Mammah har fa a take masa ya huta. Yakan yi murmurshi ne kawai ya ce, Mammah idan banyi ba jikina zai yi ciwo ne Haka dole ta yaleshi har hutunsu ya are, kamar kuma yanda yay al awari yaje Bauchi tare da su Ma'aruff cikin weekend. Sun ziyarci kabarin mahaifinsu da Umma har ma da kakaninsu su Malam. Babu wanda yasan yaje a an uwan mahaifinsu sai kawunsu Jamilu kawai, dan basu kwana ba a ranar suka juyo Kano. A watan Agusta ya koma Jaji, domin yin Young Officers Course, inda ya sake ha ewa da Imran, a wannan karon ma a aki aya suka zauna, dan sai da sukai duk yanda zasuyi aka ha asu cikin amincewar UBANGIJI. Alhamdullahi sun kamalla course in su a farkon shekarar 1999, daga nan kowa aka turashi inda zai fara aiki. sai dai an samu matsala dan anyi posting insu waje daban-daban shi da Imran, amma da yake suna da oganni tuni suka nema oga Adetunji suka sanar masa damuwarsu. Shine yay ta kai kawo har aka ha asu waje aya yanda suke fata, antura su aiki zuwa 82 Division Enugu, inda suka fara rayuwar soja ta zahiri. A can suka gane cewa aikin soja ba na jarumtaka ka ai ba ne, aikin zuciya da sadaukarwa ne.
Chapter 43 · 0% Book details