Sashe 63
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Karka damu, a yanzu nafi bu atar mutuwa akan rayuwar da zata cigaba da tunamin wanene mijin aurena. Rayuwar da zata cigaba da tunamin rasa an uwa biyar da mahaifana a dalilin mijin aurena. Na godema ALLAH da ban koma gareshi ba sai da nasan wanene mijin aurena. Ba zan aibanta shi ba, amma ni da shi da armu tilo zamu ha u gaban mai rarrabe ayyuka da gaskiya. Ban samu cikar burin haihuwar a namiji da nai al awarin baka ba, amma zan dam a maka AMANAR ata aya tilo da kaf duniya dakai ka ai na yarda. Dan ALLAH ka raineta tamkar yanda nake fata rainonta, ka bata ilimin addini dana zamani. Ka raini zuciyarta da jarumta irin taka da tausayi da hidima ga al'umma. Ko da wasa kada ka sanar mata ainahin halayyar mahaifinta, dan Alhamdullah Babana ya bata rubutun mantawa da shi a zuciyarta na har abada, ina kuma ro on yay mata tasirin da bazata ta a tunashi in ba, amma ko ya cigaba da rayuwa har lokacin girmanta, ina son ta tashi da sanin shi mataccene tun tana da uruciya, ma'ana ka sanar da ita ita in marainiya ce gaba aya ta rasa uwa da uba tun tana arama. Sannan bana son tai amfani da sunansa a matsayin uba. Dan ALLAH ka ri e min AMANAR NAJA'ATU NIMRAH, na yarda da kai bazakaci amanar dukkan alfarmata ba. Ro o na arshe har abada kada ka bar wa anan mutanen suyi sukuni da walwala a wannan duniyar. Ka addabesu, ka zame musu KI A A RUWA MAI TADA HANKALIN DO...... D...... Ta kasa arasawa saboda yanda numfashinta ke fisga. Da yar ta sake jawo shi da furta, N...Nimr... Na akin Inn...nta a cikin kwalla Inn...a ta oyeta. Dan ita suka fara ne... Nema su ka..she. in... Nu nata da mukai yasa suka kashe Innata da an uwan....a. Sunyi al awarin kuma sai sun kashe ta, ina tsoron kada su cigaba da bibiyar rayuwarta dan ALLAH ka kula da it.....a AMANA Harshenta ya ri e ta kasa cigaba da maganar. Ga Captain Musa ya araso da yaran soji zasu auketa a saka cikin jirgi likita ya bata taimakon gaggawa. Amma ina wannan tafiyar mai girma ce, kuma ta har abada ce ga Umman Nimrah. Hannu Imran ya aga musu da yar, yayinda Zak-Shadow ya motsa lips insa da yar ya shiga ambato mata kalmar shahada. Idanun kan sunyi wani irin masifar juyewa jajur. Cikin aminci UBANGIJI akan lips itama ta dinga maimaita duk abinda ya ambata ganinta na juyewa zuwa ga UBANGIJI, amma kuma har lokacin Zak-Shadow in kawai take kallo. A haka idanun suka kafe alamar rai dai yayi halinsa. A mamakin kowa gefe Zak-Shadow ya maida kansa kawai. Kaudawar da kowa yafi zargin hawaye ne suka cika masa ido. Duk da kuwa kowa yasan kuka ba abi'arsa bace. Musamman idan sukai dubi da kalolin tashin hankalin da suka gani a rayuwar aikin soja da tafi wannan har a asashen etare. Komai baice ba ya mi e kawai, yayinda Imran yaja ankwalin kanta ta rufe mata fuska tare da shimfi eta a wajen. Koke-koken mata da yaran ya aru sosai, matan sun kai su goma sha bakwai, dukansu kuma matan yayyen Umma ne da anne, sai yaransu. Inda Zak-Shadow ya nufa Imran yabi da kallo, a akin da suka sami nasarar fiddo tsohon nan ne, nan ne kuma Umma tai nuni da Nimrah na'a ciki. Captain Musa ne biye da shi. Basu fi mintuna uku da shiga ba kuwa suka fito Captain Musa auke da atuwar walla irin ta mutanen da mai hoton murtala. Da alama akin da suka shigan da duhu dan harda fitila a hannunsa da suka haska. Murfin kwallar ya bu e, sai ga Nimrah a ciki da alama ma a sune take. Riga ce doguwa a jikinta ar kanti, tayi face-face da jinin Inna dan sanda suka harbi Inna in jinin ya fallatsawa Nimrah. Karon farko Zak-Shadow daya zubama cikin kwallar juyayyun idanunsa ya kauda kansa saboda isowar Imran wajen. Cikin girmamawa ya nuna matan da yaran dake wani irin kuka mai ban tausayi. Sir! Suma za'a wuce da su ne? Kansa ya jinjina masa da bin jejin da kallo. Sai kuma ya du a tare da saka hannu cikin kwallar ya akko Nimrah gaba ayanta, kafin ya furta, Alamu sun nuna basu ka ai bane. Dan yara mata ne sukafi yawa anan, mazan basu wuce shekaru uku-uku ba. Dole ne akwai wata tawagar yara mazan gidan oye a cikin jejin nan mutanen nan sun Tabbas nima ina hasashen hakan Sir. Musamman idan mukai la'akari da furucin tsohon da yace adadin jikokinsa maza sunfi matan yawa Shiru yay yana nazarin maganar Imran in. Yayinda idanunsa ke bin mata da yaran da kallo a tsanake. Sosai kukan da suke ke ta a masa asan zuciya. Amma da yake an mazan mazane na gaske babu alamar hakan a saman fuskarsa. Sai ma auke idanunsa yay cikin bada umarni yace a sakasu a mota. Sosai ihunsu da karuruwa ta ara arfi. auke kansa yay tare da yima Imran magana asa- asa. Kai Imran ya jinjina masa, shi kuma ya wuce jikin motar da yazo a kai ya saka Nimrah a baya ya kwantar. Imran dake bin matan da kallo nuni yay da yara kusan goma ya ce a fito da su. Bayan ya ra ama Captain Musa magana a kunne shima. Cikin gamsuwa Captain Musa ya matsa yayma sauran nasu magana shima. Aifa take suka aura bindigu akan yaran. Ihun iyayen ne ya sake arfi, yayinda suke ro on kar a kashe musu yara dan ALLAH. A kausashe Imran ya furta Idan har bakwa bu atar rasasu suma ku sanar mana ina sauran anku suke? Barazanar mi sukai muku suka kwashe su?!! Shiru sukai alamar matu ar jin tsoron yin magana. Dan kuwa takunkumi akai musu ta ashin asa akan idan suka fa a a bakin ransu su duka. Takaici da acin daya mamaye ma oshin Zak-Shadow ya daka musu tsawa. Yanda amon muryarsa mai matu ar saka razani ta ratsa jejin ya saka su sake shiga razani. Tuni wata tsohuwa ta fara bayani jikinta na rawa. Iya muke nan muka rage a gidan. Dan da yawan yaranmu maza suna birni neman ku i. Wasu kuma sun gudu bamu san inda suke ba Shi in jami'in tsaro ne na soji mai matu ar fi rah da kaifin basira. Yayi matu ar sanin aikinsa ta yanda ko'a furucin baki yakan iya tantance na gaskiya da akasinsa. Dan haka kai tsaye ga gane ya kuma fahimci tsohuwar a tsorace take. Batare da ta sake cewa komai ba yay nuni da a saki yaran. Ai a guje suka shiga komawa wajen iyayensu wasu har suna tintsirawa a asa suna tashi. Fitowa su Zak-Shadow sukai ofar gida, aka bar yaran sojoji kusan goma sha a ciki tare da su. Mizai faru, mintuna goma su Imran basu ulla da fitowa a gidan ba dan suna tattaunawa ne kawai sukaji tarwatsawar abu mai arfi ta yanda su kansu sai da suka zabura gefe dukansu. Innalillahi wa-inna ilaihiraji'un, ashe duk wannan abun dake faruwa bomb ne aure a jikin aya daga matan gidan, shiyyasa suka kasa fa ar inda sauran yaransu dasu Dagger suka iba a jiyan suke. Gaba aya kuma ya tarwatsa gidan da matan, da yaran, da sojojin da aka barsu da su su wajen ashirin. Wannan da shine tashin hankali ba'a sanya maka rana. Dan ba gidan ba hatta gidajen makwaftansu dake lafe a gida hankula a tashe tako wace kusurwa sun tarwatse. Sai dai kaga mutum yay sama an dawo da shi asa a tarwatse, wasu ma sasan jikin duk a rarrabe. Wannan abu ya zafafi Zak-Shadow da fusatashi, dan kuwa tunda ya dam a Nimrah a hannun Imran sai kawai yay sabuwar ammarar aiki da kansa ba umarni ba. Ya i da karan kansa ba jiran yara ba. Hankalin su Captain Musa ya tashi ganin yay wani hatsabibin tsalle ya shige motar ya i mai zazzage ma iya da gurneti suka san ran an maza ya aci. Aiko da gasken ya acin, kuma ranar yaran Dagger sun tabbatar ya acin. Dan da karfin ikon ALLAH a maimakon Captains shi da kansa ya jagoranci runduna guda a cikin jejin suka dinga za ulo yaran daga. Wani mahaukacin kisa yake musu mai cike da fushi da ba in ciki. Gaba aya wannan yinin Zak-Shadow baiyi tsayuwar awa aya ba da sunan hutu. Ga sojoji an sake aro masa. Lungu da sa o ya dinga za ulosu, dan kuwa bai gushe ba zai da ya gano sabon wajen ha ar ma'adanan daya sashi fahimtar dan su aka haddasa wannan sabon tashin hankalin na kwanakin nan. A take ya saka sojojinsa suka rufe wajen haba aya... Zakusha mamaki idan nace muku duk wannan abun da ake munafukin nan bai gaji da aukar video a wayarsa ba, dan cikin aljihun riga ta gaba ta sakata cike da dabara, duk kuma inda Zak-Shadow ya sanya afa yana biye, hasalima shine auke da wayar sadarwa a baya da jakar harsasai yana urama Zak-Shadow a bindiga... <<<<<>>>>>> Kwanaki hu u cir su Zak-Shadow na ya i a wannan yanki. Sun ci nasarar zubar da yaran su Dagger zubarwa mai muni, a arshe kuma Zak-Shadow ya kama Dagger da hannunsa kamar yanda yay al awarin cikin awanni ari da yardar ALLAH. Sai ko UBANGIJIN ya yarje masa ya kuma tallafa masa kafin cikar a wannan ya cafke Dagger in.. Ta ko ina asa ta auki labari akan kama Dagger da Zak-Shadow yayi da hannunsa. Da yanda ya jagoranci wannan ya i na tsawon kwanaki shida da kansa ba zaman bada umarni ba shi da Major Imran. Ta ko'ina gidajen tv dana rediyo zance su kawai kake ji. Dan kuwa sun nuna matu ar jarumta da mazantaka na mur ushe ungiyar duhu da an barandan data tara irinsu Dagger. Sai dai abinda Zak-Shadow da al'ummar asa basu sani ba. Mur ushe su Dagger kashe maciji ne kawai batare da dare kansa ba. Saboda su Dagger sunan karnukan farauta kawai suke amsawa, manyan mafarutan na gefe suna kallon komai dake faruwa suma. Duk da hankulan shugabannin ungiyar duhu a tashe yake da kama Dagger in da da