← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 94

Sashe 84

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kusan bakwai Zak-Shadow da bai san abinda ke faruwa ba ya shigo. Dan rashin samun isasshen barci a daren jiya shima yau makara yay ko sallar asuba a gida yayi ta. Dan haka sai yanzu yake fitowa daga sashensa, batare da ya ko kalla hanyar akin Nabeeha ba, hasalima yayi zaton basa gidan, dan tunda suka dawo asibiti jiya baiga kowa ba tsakanin ita da uwar tasu da annen nata, sai Jiddah ce ma da daddare ita da mijinta suka zo duba su tanata kuka da bashi ha uri akan abinda ar uwar tata tayi. Tun shigowarsa falon yake jin kukan Nimrah. Kai tsaye akin Mammahn ya nufa shima, inda ya tadda duk annensa a ciki. Kowa kuma arin lallashin Nimrah dake kwance jikin Mammah yake yi, amma yarinyar nan ta i sauraren kowa sai kwarara ihu take yi. Babu wanda yaji sallamarsa sai da amshin turarensa ya shiga hancinansu da gyaran muryar da yayi sannan duk suka juyo, idonsa akan afar Nimrah ya amsa gaisuwarsu, suko hankulansu na'a kan hannunsa shima. Cikin girmamawa da tsantseni ya gaida Mammah shima, tare da tambayarta jikin Nimrah data an sassauta kukanta. Alhamdulillah, sai dai inaga dole mu koma asibiti yanzu dan tunda asuba take kukan afar, inaga tana mata ciwo ne, kaima yaya naka hannun? Hannun nasa ya an kalla, sai kuma ya kalla afar Nimrah in itama. Ni kam babu wani damuwa Mammah, itama harda rigima dai Rigima kam ai dole ce, dan tana da hujjar yinta. Wannan ciwon ba arami bane ga babba ma bare ita. Babbar damuwar ma ta i cin komai ga tea nan har ya huce ta i sha Hannu ya mi ama Biebah dake ri e da kofin batare da yace komai ba, ganin haka sai kawai Mammah ta mi e tana fa in, To Biebah tashi ki nema na mutane abincin kari. Mu'azz tashi kaima muje kai shirin makaranta. Kamar zai yi kuka ya ce, Mammah ni bazanje ba, zan zauna tare da Nina Kallon da Zak-Shadow ya watso masa ya sashi sauka a gadon da sauri, sai dai idanunsa cike da walla. Murmurshi kawai Mammah tayi ta kama hannunsa suka fice. Caraf Nimrah ta ce, Mammah ni dai ki dawo naki nake so.... Mammah na arin juyowa Zak-Shadow ya watsama Nimrah harara, sai ta sake ta e baki zatai kuka. Kika bari wannan hawayen suka zubo zaneki zanyi. Maza kar a kisha. Kin zauna kinama mutane kukan banza amma bakinki baya mutuwa Ni dai dan ALLAH ka bita a hankali Muhammad, idan bazaka iya ba na dawo na bata aramin murmushi yayi. Shike nan Mammah zan bata Suma su Bilal duk murmushin sukayi dan sunji da in ganin murmushin nashi. Shima zamansa ya gyara ya fara kai mata kofin bakinta, sai ko ta fara amsa babu musu. Sha kamar uku ta yatsine fuska tana kallonsa, ta ce, Dada Uhhhm Ya amsa mata a ma oshi. Kaima ar dabar ce ta jimaka ciwo a hannu? Da mamaki ya zuba mata ido, a zuciyarsa yana ayyana (sai shegen surutu). Suko su Ja'afar dariya zancen nata ya basu, jira suke suji amsar da Dadan zai bata amma yayi shiru. Cikin kasa ha uri Ammar ya ce, Nimrah ar daba kuma? Eh Uncle Ammar . Ta fa a kamar yanda taji Mu'azz na kiran kowansu da Uncle in. Batare da jiran cewar kowa ba ta cigaba da fa in, Ummana tace an daba ke ri e wu a da yanka mutane ai. Kaga itama ta ri e wu a ta yankamu ni da Dada, Dada kaima kayi kuka data yanka ka? Ta are maganar tana tsatstsareshi da idanu. Rasama abin cewa yay, sai kawai ya samu kansa da girgiza mata kai. Idanu ta waro masa sosai, sai kuma ta yamutsa fuska alamar motsin da tai taji zafi. Amma bata ha ura ba sake cewa, Kenan kai baka yi kuka ba? Kuma baya maka zafi kamar nawa? Nan ma kai kawai ya jinjina mata yana kai mata kofin shayin a baki dan ta yaleshi da wannan surutun nata, gashi ta wani tsatstsareshi da idannunta. Kauda kanta tai gefe, dan in surutu nacin Nimrah itafa sai ta fetsar take jin da i, dan yanzu ma kai tsaye ta ce, Dada jira na gama. Kai miyasa baka jin zafin ko kaima an daba ne? Dan Lawwali yace min suna an daba dake yankar mutum idan aka yanke su basa jin zafi kuma basa yin kuka Anya shi kam ya ta a gamuwa da magananniyar yarinya irin wannan? A zuciyarsa yake ayyanawa, yayinda su Ma'aruff ke unshe dariyar dake cinsu. Dai-dai Nimrah ta kai hannu tana ta a hannun Zak-Shadow dake kallonta kawai Momyn Nabeeha tai sallama, kafin su amsa ta shigo Nabeeha biye da ita sai su Ismat a arshe, dan ita da kanta ta tattaro su wai su duba Nimrah su bama su Mammah ha uri. Ai a bazata Nimrah tai wani uban tsalle ta haye jikin Zak-Shadow ta amesa tana fasa ihu da fa in, Wayyo Dada ar daba ta sake zuwa, oyeni kada ta yankamu. Wayyo Dada wayyo zata ara yankamu shike nan ar daba mai wu Idan kunji ana sumar tsaye to ita Nabeeha da uwarta sukayi. Dan har tsakiyar kai kalmar ( ar daba) in nan ta dakesu. Yayinda su Bilal suka kasa ha uri shi da Ammar suka shiga kwasar dariya. Suko su Amima yanda Nimrah tai uban tsalle ne da firgita ya basu dariya. Ita ko baiwar ALLAH da gaske tsorata tayi, dan tai bala'in shigewa cikin jikinsa, arshe ma rigarsa ta aga ta tura kanta ciki ta du une, ALLAH ya sota ma tun a daka tsallen farko ya ri afar tata mai ciwo a hannunsa, da ba aramin fami zatayi ba kam, maybe ma inkin ya farke tunda jikin ba wani wari gareshi ba fatar uruciya. Ihun Nimrah ya shigo da Mammah da Biebah, sai Mu'azz da har an masa shirin makaranta. A tsorace Mammah ta ce, Wai mike faruwa? Da arfi Nimrah dake cikin rigar Zak-Shadow ta ce, ar daba ce mai wu a Mammah ta dawo zata yankamu ni da Dada, ku yankata Mammah kuma ku yayyankata kamar akuya Duk yanda Yaya Ma'aruff da Yays Ja'afar ke dauriya a wannan ga ar suma sai da suka dara. Sai Mu'azz ne abinka da yarinta ya hau gadon yana kamo hannunta da fa in, Ke Nina bafa ar daba bace su Aunty ne fa Cikin kuka Nimrah ta ce, arya kakeyi ar daba ce, ranar ita ta yankamu ni da Dada, kuma tace saita kasheni bata sona. Muguwa! Muguwa in ALLAH ya yarda sai kin mutu yau kin ha u da fatalwar kabari da walakiri mai aton sanda Cikin matsanancin acin rai da kishin ganin yanda Nimrah ta shige rigar Dada, shi kuma ya wani zauna kamar gunki yana ri e da afarta kawai sai zuciya ta tokare irjin Nabeeha. A zafafe ta ce, Ubanki ne mugu an daba shegiyar yarinya mayya, Momy ga abinda nake gaya miki nan kin i yarda kina wani muzo mu ganta... tai maganar tana kai hannu zata dam afar Nimrah dake hannun Dada. Abinda kuwa bata ta a zato bane ya faru, dan kuwa caraf aka ri e hannun nata, tana arin fisgewa cikin rufewar idanu Mammah ta auke fuskarta da mari. Lokaci guda akin yay tsitt, dan bama ita data ago a birkice taga Mammah ce mai marin ba hatta Zak-Shadow kansa ya girgiza, dan kowa yasan wacece Mammah akan kawaici.... Katse tunaninsu Mammah tayi, cikin fa a ta ce, Shin haka kike dama Nabeeha ko yanzu ne wannan halayyar banzar take neman shigarki? Wane shirme ne wannan kike yi akan yarinya arama ar cikin ki, wadda da ALLAH ya baku haihuwa kin haifi wadda ma ta fita...... Hannun Nabeeha Momynta ta kwace daga wajen Mammah, itama a fusace ta ce, Haba Hajiya A'isha yada haka da girmanki? Bakiga laifin Haysam shi da ya auri ar cikinsa ba sai laifinta, kishiya ko jaririyace ai yin kishinta ba haramun bane balle wannan hatsabibiyar yarinyar mai kama da an haifeta a tsakiyar tasha..... K! Ya isheki haka Malama!! Ma'aruff ya fa a a zafafe tamkar zai kaima Momy duka. Cikin zazzaro idanu dan shima akwai zuciya kamar Dada ya cigaba da fa in. K har kina da bakin cema wata ar tasha bayan ga ar tasha nan kin haifa mai yankar mutane da wu a, ai gaskiya Nimrah ta fa ar daba kika haifa, sannan Wlhy mahaifiyarmu ta fita cikin idanunki idan ba haka ba kuma zaki sha mamaki, dan akan Mammah da Dada komai zamu iya yi ciki harda koya muku tarbiyya dan naga tayi aranci anan. Ku mi yasa baku san kawaici bane ba, idan badan Mammah in ba wlhy da tun jiya mun yagalgala ku sai buzinku. Iyeee!!! Ma'aruff ni zakama rashin kunya? Anyi miki in, in har zaki ta a mana uwa duka ma zaki iya ci a hannunmu. Anata muku kawaici amma bakwa ganewa, damma kin samu ana gayawa ar taki gaskiya da gyara tarbiyyarta tunda ke kin kasa. Nimrah kuma ta zama matar Dada sai dai duk mai mutuwa ya mutu da ba in ciki babu canji, wani wasan ma sai nan da shekarun girma..... Hannun Ma'aruff Mammah ta ri o dan yi yake kamar zai kwashe Momyn Nabeeha da mari. Ya isa haka . Cewar Mammah tana janye Ma'aruff baya. Kafin ta maida dubanta gasu Nabeeha, babu alamar wasa ko sassauci a tare da ita ta nuna musu hanyar fita, Ga hanya Hajiya Hasiba, idan kuma kuka kaini bango to zan barku da Muhammad, kun san kuma abin bazaiyi yau ba. Dan na fara gajiya da tausarsa akan wannan haukar na Nabeeha. Dan ALLAH ku barmu muji da abinda ya dame mu. Cikin acin rai itama Momyn ta bu e baki zatai magana Mammah ta sake aga mata hannu tana girgiza kanta.... Idan bazasu fita da arzi i ba Mammah ki barmu mu fitar da su, dan mu nan munma ishesu Dada yafi arfinsu, su in banza ya tanka haukarsu Yanzun kam Ja'afar ne mai maganar. Jiki a sanyaye Ismat tazo ta kama hannun Momynsu dana Nabeeha, shiyyasa tacema Momy kada aje bada ha urin nan yanzu dan tasan nacin Nabeeha da mitar tsiya, sun kuma san wanene Dada a
Chapter 84 · 0% Book details