Sashe 59
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
a gefe dake nuna alamar na gardawane da kufan fitsari da akayi, awon wai da akaci da sauran sigari da akasha. Nimrah na cin dabinonta ta nuna wani waje tana kallon Zak-Shadow. Baba an sanda, kuma anan naga wani mai irin kayan Babana zaune shima ya rufe fuskarsa saboda tsoron fatalwoyin Babanki? Eh mana . ta fa a cikin shiririta tana cin dabinonta. Kallon kallo akai tsakanin Zak-Shadow da Imran. Imran ya maida hankalinsa kan Nimrah, cike da wayo ya ce, Shine kuma baki masa magana ba? Ai tsoro naji na fatalwoyin, kuma ya rufe fuska fa, shima kaga ai tsoron su yake ji ko baba an sanda? Miyasa baki fa ama mamanki ba? Na fa a mata ita da Inna sukace na cika surutu, shine na gayawa su Fatsima sukace arya nake, niko na rakosu harnan fatalwoyin kuma har sun gudu Wani irin cije baki Zak-Shadow yayi, zuciyarsa na hasaso masa tabbas akwai oyayyen al'amari akan mahaifin yarinyar nan. Barin wajen sukai suka koma can gidan su Nimrah. A karo na farko Zak-Shadow ya bu aci zama da Umma dake cikin tashin hankali tunda suka fita da Nimrah, sai dai ganin sun dawo ta shiga sauke ajiyar zuciya a jajjere. Dan haka ma koda Zak-Shadow in ya nema suyi magana bata musa ba. Tabarma ta akko ta kawo ashin inuwar ce iya dake a sashen nata. Dan haka kawai take jin girman mutumin nan a ranta tun randa suka fara ha uwa shekarun baya. Bai musa ba ya zauna shi da Imran. Ita kuma zata zauna asa yace ta akko wata tabarmar. aki ta koma ta akko tabarma ta shinfi a itama ta zauna. Shiru wajen ya auka kafin ta motsa baki cike da arfin hali ta ce, Kayi ha uri da abinda nayi ranar, ban san kuskure bane ba. Wlhy farin ciki ne kawai ya kamani na ganinka saboda tun wancan shekarun da muka ha u nai maka al awarin baka abinda na haifa sai nake yawaita mafarkinku a barci na. Kullum kuma cikin addu'ar ganin ba haifi namijin da zan baka ba nake, amma har yanzu ALLAH bai cika min burina na ba Karo na farko Zak-Shadow ya kalleta, kai tsaye ya furta, Ina abinda kika haifa wancan karon? Cikin sauke ajiyar zuciya ta kalla Nimrah dake wasa da asa gefensu ka an, Itace waccan da kuka fita da ita azun Daga shi har Imran kallon Nimrah sukai suma. Imran dake murmushi ya ce, Masha ALLAH, ALLAH ya albarkaci rayuwarta. Minene sunanta? Naja'atu, amma muna kiranta Nimrah saboda sunan mahaifiyar maigidana ce. an huci Zak-Shadow yayi ka an, asa- asa ya ce, ALLAH ya rayata . Sai kuma ya cigaba da fa in, Ranar tace miki taga fatalwa a bayan gida, miyasa baki saurareta ba? Nimrah nada surutu sosai, shiyasa nakan eta da irin wa an nan abubuwan saboda tarbiyyarta matsayinta na mace Hakan ba laifi bane, amma yana da yau idan yaranmu sukazo mana da maganar abinda ba kasafai ake zancen sa a cikin al'umma ba mu basu lokacinmu, idan na gyara ne mu gyara musu, ko muyi musu arin bayani ta yanda zasu fahimci abin a yanda yake. Idan ba haka ba zasuje su fa a a inda bai dace su fa in ba, maybe ya cutar da su, ko kuma ya zama na cutarwa ga kowa. Yanzu kamar ita zancen fatalwa data kawo miki mutanen da sukai muku arna da ibar yaranku ta gani a wannan ranar, da kin saurareta da kin fahimci abinda take magana akai, koda bazaki iya aukar mataki ba zaki iya fa awa maigari, kinga kin taimaki garinki da al'ummar garin. Sa anin haka kuma kinga sakamakon daya kawo. Ba aramin tashi hankalin Umma yay da bayanin Imran ba. Ta zubama Nimrah ido da har yanzu ke wasa hawaye na silalo mata. Imran ya sake katseta da fa in, Minene sana'ar mahaifinta? Manomi ne kamar sauran mazan garin, sai sana'ar kifi da yake yi kuma anye? Eh, harda soyayye, a can yara yake zama, duk zagayen auyukan nan shi ka ai ne ke wannan sana'ar shiyasa yake samun ku i sosai dan wajensa ake zuwa a saya auye- auye dake kusa damu arfe nawa yake fita da kayan sana'ar tasa? Sai da yamma bayan la'asar. Dan haka yake jimawa bai shigo gida ba sai irin sha biyu haka, wani lokacin kuma baya kaiwa musamman idan Tanimu aninsa na gari, dan yakan amsheshi shi kuma ya dawo gida Shi Tanimun miye sana'arsa? Shima yana noman ne, amma yana fita balaguro cikin birni. Yaro ne mai ari sosai, dan kusan cigaban dake yankin auyukan nan namu duk da taimakonsa da tsayawarsa aka samesu. Kamar mi da mi? Kamar makarantu, asibiti, wutar lantarki. Shi ne yayta wayar da kammu har muka saka yara a makaranta musamman mata da muka i da farko. Idan yaje birni yakan da e ne? Baya wuce wata uku yake zuwa gida yay kamar sati biyu ko uku sai ya koma Shida mijinki waye yafi wani ku To bana ce ba, dan shi samun namiji ba kai tsaye mu muke iya ganewa ba anan. Amma su duka kowa na samu gwargwadon iko, sai dai shi Tanimu mutum ne mai hidima ga an uwansa gaskiya. Shi ko mai gidana in banda mu da Innarsa babu nauyin kowa a kansa A wannan zuwan da Tanimu yayi gida kwanansa nawa a garin? Bai wuce sati aya ba Yana taya maigidanki zama wajen kifinsa kamar yanda ya saba? Eh yana taya shi Kwana hu u da suka wuce ina maigidanki ya je? Yaje Gangare aurin auren ar wani abokinsa arfe nawa ya dawo? Da daddare ne sosai gaskiya dan har munyi barci ma? Tunda kika aureshi, kin ta a kama shi da wani laifi? A'a gaskiya, shi mutum ne mai ha uri da rashin son magana. Tun a rayuwar samartaka ma ban ta a jin ance ga abokin fa ansa ba. Koni aka atawa rai na tashi da nufin yin fa a ko ramawa yakan zauna yayta bani ha uri da hanani. Kasancewar sana'ar dare yake yi yana zama a gida tare da ku ya yini? A'a gaskiya, yin haka zai iya zama abin magana mu anan balle gidan yawa, yakan fita kamar kowa amma yana shigowa gida musamman lokacin cin umame da kuma in an gama abincin rana Zamu iya ganin kayan sakawarsa? an shiru tayi a karo na farko ta kasa amsa Imran a wannan karon, sai da Zak-Shadow ya ce, Karki damu ba wani abu bane Ajiyar zuciya ta an sauke. Kafin ya mi e ta shiga aki, babu jimawa ta fito da akwatin arfe babba. A gabansu ta ajiye sa, Imran ya ce ta bu e da kanta. Bu ewar tayi tana fiddo kayan aya bayan aya, gaba ayansu basufi kala bakwai ba, duk yadi ne irin na mai aramin arfi. Bayan ta gama gaba aya yace ta maida, ta kawo masu datti suma. Haka ta mi e ta ebo su, suna aure a cikin zaninta, harda nata dana Nimrah. Nashi suka saka ta ware, nata ma haka, sai na Nimrah da sukafi duk nasun yawa. Zaki iya lissafa min ranakun da duk kuka saka wa an nan kayan? Da yake basu da yawa sai tace zata iya. Da nata ta fara, sai nashi. Ta akko kala na hu u tai an shiru tana kallon kayan, a karo na farko ta kallesu, sai kuma tai arin ajiye kayan batare da tayi magana ba Miyasa zaki ajiye? Na manta ranar daya saka wa an nan gaskiya, shiyyasa zan ajiye gefe kozan tuna kafin na gama Ya yi cigaba Cigaba da lissafa sauran kala ukun da suka rage tayi. Imran zai yi magana Zak-Shadow ya katsesa ta hanyar yi mata nunin ta auki kayan ta koma da su. arin kwasa tai harda wanda ya ware in nan yace ta barsu. Haka ta barsu ya kwashe sauran. Tana barin wajen Zak-Shadow yay kiran Nimrah. Da gudu kuwa tazo, ya kama hannunta ya zaunar a kusa da shi, sai kuma ya jawo kayan baban nata gabansu ya ajiye. Kalla wannan kayan na waye? Cikin wasa tace, Babana Yaushe ya saka su a jikinsa? Na manta Tuna dai, kamar na ranar da kikaga fatalwoyi ne a bayan gida fa Kayan ta zubama ido kamar mai son tuno haka. Sai kuma ta kalli Zak-Shadow. Eh-eh irinsu ne wanda ya rufe fuska ya saka Dami ya rufe fuskar? Bansan sunan abin ba, amma Babana na saka irin shi shima Jeki akko min na gani Da gudu ta tashi zuwa akinsu. Umma dake tsaye tana kallon su hankalinta ya fara tashi, zata bi bayan Nimrah Imran ya hanata. Kusan mintuna uku kuwa sai ga Nimrah da hiramin Babanta ta dawo. Kar a Imran yayi, ya ce, Kin tabbatar shine wannan? Kai ta jinjina musu kawai. Imran ya kalla Zak-Shadow, kai ya jinjina masa. Shima sai ya jinjina nashi yana aukar kayan ya fara bincikar aljihunnan jikin wando da rigar. Ana farko ya ciro ku ari biyar bandir biyu sabbi, ayan ya ciro wata takarda arama a nanna e. Gaban Zak-Shadow ya ajiye ku in, sannan ya warware takardar......... _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ _Chapter 45_ __________________ https://chat.whatsapp.com/GCVmfFguMEf49AFrOjSiMt Link na grp 07077532253 https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1 link. N dm https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90R3y3tCP5z&_r=1 tiktok IMZEEDVENTURE Duniyar kayan kitchen an yayi dake maida mata walisa a gidajensu. Shin kuna Neman in da zaku samu luxury kayan kitchen masu kayatarwa? Kayan yara masu kyau unique na yan gayu? To shiga link din grp na