Sashe 18
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
tasa hannu da sauri ta kare. Sai ya saki dariya, itama murmushi tayi mai cike da kunya. Zuciyarta na fa a mata abin da bakinta bai iya fa a, cewa sabuwar rayuwa ta fara a garesu kamar yanda Inna ta fa a mata, kuma shi mutum ne da nutsuwarsa ke girmama kwarjininsa a idanun kowa a bayyane. Kin tafi tunanin miye kuma Matar Abdul-rasheed? Kai tsaye ta ce, Tunanin ka Masha ALLAH akan mi? Babu kwalo-kwalo ta zayyane masa kalaman Innar tata. Ya an tsaya kawai yana kallonta da murmushi. Kafin ya cigaba da cin abincinsa yana jin girma da kimar Inna na aruwa a ransa. Haka dai suka karya, ya taimaka mata suka gyara wajen, ta kwashi kwanikan zuwa waje danta wanke a gaban rijiya. Shi kuma sai ya auki botikin arfe ya fara jawo mata ruwan wanke-wanken, sannan ya fara iba a botikin yana kaiwa randunan ruwansu aya bayan aya. A haka suka kammala aikin yace zai yi wanka. Ita da kanta ta auki ruwan takai masa bayi tare da kwandon soson wanka. Ta dawo akin ta saka turaren wuta ta share. A lokacin ne kuma yaro yay sallama cikin gidan auke da kwanika akan ture. Bata yayi tare da mata bayanin cewa Inna ce tace ya kawo. Bata san wacece Innar ba, amma taji a ranta daga gidan su Abdul-rasheed in ne. Godiya tayi da sannu, dan haka yaron bai zauna ba ya juya ya koma. Fitarsa babu jimawa Abdul-rasheed ya shigo. Ya ce, Sallamar wa nake ji ne kamar Amadu? Wani yaro ne dai, ban sani ba ko sunansa kenan, abinci ne ya kawo yace inji Inna Oh daga gidanmu ne. To ki zauna sai ki karya Idannunta a an ware ta ce, Ba yanzu muka gama karyawa ba? Na oshi ALLAH To Alhamdullahi, ki ajiye sai zuwa anjima. Amma kije kema kiyi wanka kada mutane su fara shigowa suna ganinki da kaya tun na jiya Babu ko musu, sai ma amsa masa da tai cike da ladabi, daga haka ta iba ruwan itama ta wuce bayi. Lokacin data fito harya shirya, dan haka bai zauna ba yay mata sallama ya fice dan har yara sun fara shigowa gidan. Aiko itama A'isha a gurguje ta kammala saka kaya, ta zauna tai kwalliya gwargwadon iyakarta kuma dai-dai da lokacinsa. Daga nan ta fiddo ma yaran da suka fara taruwa a gidan tabarmin karauni, sai kuma ta kwaso shantu duk ta zube dan harda ammata. Ai daga nan suka kafa shiriritar ki an shantu da ammata sa'anninta a tsakar gidan nan suna raira wa in ga a. Kafin kace mi gidan ya cika da yara. Manya dake shigowa ganin akin amarya kota kansu basa bi ma, sai dai su shiga su gano su saka albarka su fice abinsu batare da sun damu ba, dan wannan ba komai bane daga amaren wannan zamanin nasu saboda uruciya da arancin shekaru.. Amarya A'isha bata sake tunawa da batun Abdul-rasheed ba har yamma ta samu abokan shargalle, abincin rana da aka sake kawowa ma daga gidansu, dana safen duk sun cinye ita da awayen nata. Sai gab da magriba an kawo mata tuwon dare mai kawowar data kasance anwar Abdul-rasheed ce Khadijah da bata koma Maiduguri ba ta kora yaran duka, sannan ta saka A'isha yin wankan dole ita kuma ta rufo gidan ta hau gyara tsakar gidan da sukama kaca-kaca. akin dai da yake ba zama sukai ba a ciki da haskensa, sai an ganin aki da ke shiga. Amma duk da haka shima sai da Khadijah ta sake sharo mata shi ta kunna turaren wuta, zata kunna fitila taga babu kalanzir. Dole ta auki kalbar da aka aje dan sayen kalanzir in ta fita samun yaro ya bada a suyo sukaci karo da Abdul-rasheed ya dawo. Koda ya tambayeta ina zata haka ta sanar masa sai shi ya amshi kwalbar yace ta koma shi bari ya say o. Haka kuwa akayi, dan haka a gurguje Khadijah ta taya A'isha shiryawa. Sai gata ta fito tsaff kamar ba itace tai bu u-bu u ba. Ta bajeta da turare. Sai ga ango ya dawo. A tare suka masa sannu suka gaisheshi, Khadijah ta amshi kalanzir in tana zubawa a fitila shiko yana satar kallon A'isha datai masa yau a cikin jojin da Khadijah ta sakata sakawa. Yasan wannan kwalliya haka sai da taimakon Khadijan, dan ta fita wayo kuma ta girmeta. Khadijah na gama kunna musu fitilar tai musu sallama zata wuce. Amma ya tsaidata kan ta zauna har ya dawo massalaci dan kar A'isha taji tsoro. Haka dole ta zauna sukai salla tare, shi ko yay alwala da ruwan da A'ishan ta kawo masa a butar karfe ya fice massalacin........... _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce _Da s nan Allah, Mai rahama, Mai jin ai._ _Chapter 14_ __________________ https://chat.whatsapp.com/Kf6jd57OsXHCG7cODNAje6 *_Kowace mace na matu ar son taga ta gyara kitchen inta kodan ta kalla itama taji da *_Dun ule ku in ki saya ne ke miki wahala hajiyata?_* *_Ko tarasu a hannunki ke baki wahala saboda kokin fara sai ki kasa ki kashe?_* *_To kwantar min da hankalinka awata, IMZEED VENTURE ta gama shirya miki komai ta yanda kema zaki mallaki naki cikin sau i da rahusa._* _Ta bu e adashin gata wanda yafi bashi kwanciyar hankali da da i, akan farashi mai sau i, kaya an zamani, gasu ingattatu. Za'a kai miki a duk inda kike. Kedai naki kawai yin zubi akan lokaci._ *_Za'a fara zubi 25th October in sha ALLAH 20k monthly kayan 100k 10k monthly kayan 50k *_Arha tafi bashi, hakama adashe yafi bashi. Ga sau i abaka tamkar yauta __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ .........Abdul-rasheed bai dawo ba sai bayan sallar isha'i. Yana shigowa Khadijah tai musu sallama ta wuce. Shi kuma ya zauna yana zolayar A'isha akan yau dami-dami tayi da baya nan?. Sai da ta ajiye masa abincin da aka kawo daga gidansu gabanshi sannan ta zauna tana bashi labari cike da farin cikin tabbacin yau in ya mata da i. Shima sai yaji nashi farin cikin ya sake girma, da jin damuwar yanda zai tafi ya barta nan da kwanaki ka an dan zai koma Kano makaranta. Dole dai ya ture tunanin a arshe ya lalla ata sukaci abincin tare, daga nan suna hira yaga ta fara hamma yace taje ta kwanta. Shi kuma ya akko kayan karatunsa ya fara nazari. Daga baya shima ya kwanta a nashi gado batare da yau ma yama A'isha komai ba. Kwanakin da suka biyo baya sun cigaba da gudana ne cike da sha uwa a tsakanin Abdul-rasheed da A'isha. Domin kuwa cikin hikima irin ta masu ilimi yanata jan ra'ayinta da janta a jiki kamar aboki tana sake sakin jiki da shi. Gayyar yaranta kuwa na anguwa kullum tare da su take yini, a haka suka cika kwanaki goma Abdul-rasheed ya shirya komawa Kano dan kwanakin hutunsa sun are. Gashi yana arshen zango baya bu atar wasa da karatunsa. A'isha taci kuka sosai har ya dinga jin kamar shima ya tayata, daga arshe dai da yar ya lallasheta ya tafi ya barta zukatansu cike da aci. A'isha ta koma sukuku da ita, kuma yanzu tana yini ne kawai a gidanta, amma da daddare can gidan su Abdul-rasheed take zuwa ta kwana. Da safe sai ta dawo gidanta sai kuma dare taje can. Tun tana tsangwamar kanta harta saki jiki saboda annensa biyu da suke kusan sa'anni ammata. Ga Inna ba ruwanta, fa anta kawai dai idan anyi ba daidai ba. Sosai A'isha take saka hannu suyi aikin gida tare da su Alawiyya, idan zasu fita ne dai Inna ke hanata binsu, ko in zasu tafi makarantar allo. Tun abin na sakata kuka harta fahimci hakan fa shine a'ida da doka, tunda sauran matan yayunsa bataga suna fita ko'ina ba sai da dalili, dan haka sai ta saki jiki. Tun A'isha na irga kwanakin tafiyar Abdul-rasheed harta bari, kwanci tashi sai gashi da watanni har hu u. A lokacin ne Baba ya aika masa wasi ar tunatarwar yazo gida ko kwana biyu yayi, koya manta yana da iyali ne yanzu. Ya kamata ya dinga sara yana duban bakin gatari. Wasi a ta isa ga Abdul-rasheed. Kuma ya gamsu da tunatarwar Baba, sai dai baya son zuwa gida ne saboda kaucewa abinda zuciyarsa da gangar jikinsa ke raya masa akan A'isha. Yana son ya bata damar ara fahimtar kanta har ga ar kammala karatunsa daya rage watanni biyu rak. Dan haka ya maida sa on wasi ar baba da amsar ban ha uri data neman uzirin bashi damar kaiwa zuwa watannin da suka rage masa. Acewarsa karatunsu ya auki zafi a yanzu kuma suna gab da fara jarabawa. Bayan an kawo wa baba amsar Abdul-rasheed dole ya ha ura ya bishi da addu'a, dan ya fahimci manufarshi kai tsaye. Haka kuwa aka ci gaba da rarrafawa har watanni biyun Abdul-rasheed na karatu suka cika. A lokacin ya shirya baro Kanon dabo zuwa Bauchin Yakubu gida. Sun sha kuka sun sha ru ani shi da amini kuma an uwa Nasiru da ogansa Yaya Zubairu. Daga arshe dai dole suka sallamawa tunda mai rabawa ta raba, sai dai ance sabo turken wawa ne, a wannan ga ar wannan turke ne kafe da zukatan su Abdul-rasheed. Yaje yayma Innar A'isha sallama, dan dama yana zuwa duk kwanakin mako da yake yi a anguwar kullum safiya gaisheta, hakan yasa abincinsa daga gidansu A'isha kullum kwano ukun nan babu fashi a kwanakin arshen makon. Shiko baya