Sashe 6
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
kai masa dawar daya zubama tsuntsaye ya fahimci akwai damuwa a tare da shi, dan haka ya la e yana nazartar shi, sai kuma akai sa'a aka kira wayarsa a lokacin, dan haka duk wayar da yayi acikin kunnensa take, duk da ba wani surutu ya zuba ba, amma da yake yana ankare da sai ya saka ma komai alamar tambaya. Sai kuma gashi da za'ayi sallar magriba yaga Major Imran Abbas ne yaja sallar, dan haka zuciyarsa ta bashi Lieutenant Colonel na shirin barin jejin kamar yanda ya saba fitar adda sawu da tunanin basa fahimta. Eh tabbas basa fahimtar, dan a duk sanda suka daina ganin gilmawarsa kawai abinda zuciyarsu ke basu yana zagayen sauran sansanin ne ko meeting da sauran jagororin sansanin wato Captains, dan yakan yi hakan akai-akai. Dan kuwa runduna guda ce a ashinsa dake rarrabe a cikin jejin da suka kai a dadin dubu aya da wani abu, kuma shine Boss gaba aya da suke ashin umarninsa, Major Imran Executive Officer, sai Captains da su na asa, duk da dai suma yaran hawa-hawa ne, kamar shi yana cikin Lieutenants. Akwai Sergeants na asansu, akwai kuma Soldiers (rank-and-file). Tun asali tun fari shi dama ya shiga aikin soja ne badan kishin asa ba, dan kamar an ireshi ne saboda manufar da yake akai a yanzu, kafin ma ya shigo aikin an bashi horo na musamman ta yanda yake iya duk wani aikin munafunci da le en asiri cike da wayo, musamman akan Zak-Shadow a yanzu, kuma yana da tabbacin akwai ire-iren sa ma dan bashi aya bane kuma suna tare da Zak-Shadow in kusa sosai dama wasu manyan jami'ai irin Zak-Shadow ko na sama da shi harma dana asa da shi batare da su sun sani ba. Koda yake kwanaki an ta a kama ire-iren nasu aka kuma hukunta shi da hukunci mai girma, dan amanar gidan soja ta wuce tunanin mai tunani, su kansu a lokuta da dama suna wannan she ancin ne a tsorace, matu ar tsoron gudun randa zata tashi musu. Amma ma udan ku in da ake biyansu da shi na tunzurasu da assasa gur ataccen tunaninsu da jagorancin shai an. Balle shi dake a ashin babban ZAKI, dan bafa a banza aka saka ma *_ZAK-SHADOW_* in wannan sunan ba a gidan Soja, Zakin ne na gasken gaske da ya ciyo sunan tunma a asalin sunan yankan sa. Maybe shiyasa ma sunan ke da tasiri sosai a rayuwarsa da abi'arsa. (ALLAH ya ara kare ku jami'anmu a duk inda kuke . Kai mutane na ku ba MAZAJEN FAMA jinjinar ban girma mana , a ha a musu da kirari na musamman kuma, arshe a sara musu Waya ya zaro daga jikinsa, arama irar nokia, ya dannama wata number kira. Ba'a aga ba sai da ta kusa tsinkewa. Murya asa- asa ya furta, Good evening Sir! Amsa masa da akai daga can ya sashi cigaba da magana cikin tsantseni da risinar da kai tamkar yana a gaban wancan Sir! Yau in nan ya fita. Dan sanda na kai masa dawar da yake zubama tsuntsaye bayan nabar wajen sai na la e, naji yana waya da matarsa kamar..... Sai kuma yay an jimm alamar saurare. Kafin cikin ya ini da son a yarda da shi ya cigaba da fa in, Tabbas na tabbatar baya jejin nan, dan yau ba shine yaja sallar magriba da isha'i ba. Na duba inda ake ajiye mashin insa kuma babu shi, na le a tantinsu oga Imran ne kawai a ciki, kuma in dai ba ana kan aiki ba baka raba su. Duk da haka na bincika dukkan sauran sansanin kuma an tabbatar min bai je ba Sai kuma yayi shiru. Zuwa can ya sake cewa, Yes Sir! . Daga haka ya cire wayar a kunensa yana murmurshi, yasan yau account insa sai yayi rawar girgiza kwankwaso saboda manyan kayan da zasu shigo cikinsa akan wannan albishir in. Sakkowa yay a bishiyar ya koma cikin an uwansa, koda abokinsa da bai san ainahin shi munafuki bane ya tambayesa daga ina yake sai ya nuna ya zagaya ne yin uzuri, dan haka babu wanda ya kula suka cigaba da hirar su...... _____________ A can angaren wanda ya kira kuwa yana yanke kiran wata number ya lalubo ya danna mata kira shima. Ana agawa ko gaisuwa bai tsaya yi ba ya fara magana kai tsaye. Congratulations Aboki, yau dai mun samu damar da muka da e muna fako tun a watan jiya, dan na samu tabbacin barin yaron nan jejin yanzun nan Daga can aka furta, Woow Zak-Shadow!, damar da aka da e ana jira kace ta samu. Lallai yau rana ce ta musamman a garemu, dan kuwa na tabbatar zamuja kaya iya kaya akan wannan albishir. Ba damuwa yanzu zan sanar da oga kuwa ai ba zancen wasa faka-faka kawai Aboki Dariya yayi irin ta nasara shima, sai kuma ya ce, Okay hakan yayi, amma abokina kadai tabbar babu matsala ko? Karfa mutanen nan su ci amanar mu. Bayan mun saida asarmu sun sami biyan butarsu su zubar damu a banza batare da mun mori komai ba sai dukiya. Kasan fa halin an Adam na wannan zamanin da wayo da iya cin amana, sannan mutanen nan a ankare suke komai nasu a tsare yake. Yaron nan yaron asarmu ne na amana da kowa ke da hope a kan jarumtarsa, ba gidan soji da shugabanni ka ai ba hatta al'ummar asar nan aukarsa suke kamar wani WALIYYIN SOJA Mtsoww!! Wato abokina wataran sai naji kana bani haushi. Wai miye damuwarka da batun wata asa can, asar data kasa gamsar da kai koda da albashin wahalar aikinka, su su minene ma kace duk basu suka so mu kasance a wannan hanyar ba, eh su suka so mana, tunda ai basai sunce muje mu aikata ba, sun gama tattare komai daga su sai ansu da matansu dake asashen waje. Muko an barmu da umama kujera basir duk ya gama cinyemu Dariya sosai wancan ya kwashe da ita, tare da fa in, Wlhy baka da dama, aiko bamace muna cikin masu umama kujerar nan ba, dan mumafa tun farko karka manta munja kayan nan gwargwadon iko a gwamnati ta hanyar fakewa da ayyukan mu, kai dai a rufe rufau kawai. Ba lokaci faka-faka ka sanar dasu, kasan Yaron nan shegen kansa ne akwai wayo, komai a ankare yake yinsa Tabbas hakane. Ka bani 5minuts kawai, aikinka ya kammala a wannan ga ar zakaji alert tare dana yaron shima