← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 94

Sashe 36

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

kiran Yes, Sir! da karfin murya, kowanne cadet ya fara jin cewa jikinsa na canzawa, kamar yanda rayuwa take canjawa daga barin uruciya zuwa sabon alubale mai banbanta kai da sauran jama'ar gari. Ba su da lokacin tunani na zahiri, amma kowannensu ya fara fahimtar cewa a cikin NDA duk suna amsa sunan masu daraja aya ne da fuskantar alulabe aya a ashin oki, zumu i da burin zama soja... >>>>>>>> <<<<<<<< Yau kwanakin mako cif da shigowar su Haysam NDA, a satin gaba aya rayuwa mai sau i ce da cigaba da morar uruciya da arasa zazzage sauran wautar data rage a ga an jiki irin ta masu shekarunsu. Domin kuwa satin gaba aya babu wani abin kuzo mu gani dake nuna musu ma an fara wasan, shiyasa wasu a cikinsu suka fara shagala da maida hankali a nisha i da ulla abota kawai a tsakani. anin Haysam yaro mara kwaramniya da yawan magana. Ba ruwansa da kowa sai Imran, komai nasa a nutse, akoda yaushe yana gefe nesa da hayaniya da nisha in sauran. Sai dai a duk inda yake Imran sabon aboki sabon an uwa na manne da shi. Da yake shima Imran in baida hayaniya sosai sai abotar tasu tai dai-dai. Sai dai shi yanada surutu, dan a kwanakin kaf har ya kammala bama Haysam labarin an gidansu A to Z. Yayin da shi kuma Haysam bai iya gaya masa komai ba bayan sunansa da garinsu Bauchi da Kano da suke a yanzun. Kamar yanzu ma suna can daga bayan hall in kwanan nasu ne suna hira ko nace Imran na zuba masa surutu kiran da akema su sabbin alibai ya riskesu. A tare suka mi e suka zagayo ta gaba, batare da neman ba'asi ba suka bi ayarin saura dake tafiya amsa kiran suma a babban filin taro. Bayan sun gama hallara kaf kowa yana daga tsaye a nutse babban Officer ya tsaya a gaban su da takarda mai auke da jerin sunaye ya fara jawabi kamar haka.. Today, you will be assigned to your permanent Companies. Once your name is called, move to your Company s block. That will be your new home. A tare suka amsa da kalmar, Yes Sir! An fara kiran sunaye akunan da sunayen wanda zasu kasance a cikinsu aya bayan aya. Duk wanda aka kira zai amsa ya nufi inda aka nuna masa. Kowane aki da iya adadin mutanen da ake bu ata. Kasancewar ana binsu a jere ne a kiran sunayen har aka zo kan H, Haysam na cikin H arshe, cikin sa'a kuma Imran na cikin I in farko. Kamar yanda ake kiran kowa aka kira sunan, Haysam Abdul-rasheed Shehu. Cike da nutsuwarsa ya amsa yana mai mi ewa tsaye, Yes, Sir! , ya fa a yana nufar inda aka nuna masa an rubuta Alpha room. Kamar abin almara sai ya sake jin an furta, Imran Abbas. Haysam ya juyo cikin mamaki, Imran ma yana kallonsa cike da farin ciki har murmushi na arin bayyana kansa akan fuskarsa. Shi kansa Haysam sai da aramin murmushi ya bayyana ka an a saman tashi fuskar. Dan bayan anensa Imran shine na biyu daya ji yana so tamkar jininsa. Gashi dai suna matsayin sa'anni ne a shekaru, amma raunin Imran dake a bayyane yasa yana jinsa kamar aninsa daya kamata ya bama garkuwa. Badan Imran ya bashi labarin shine yake son aikin soja da kansa ba da ya ce an tilasta masa ne da tsiya saboda yanda yake a raunane. An aro mutum biyu cikinsu, dan kowanne aki na aukar mutane hu u ne. Gado biyu ne sama da asa. Biyu a sama biyu a asa. Sai lockers da sauran abin amfani kowa da nashi da ma sunansa a jiki. Kowane group an ha a su da Officer in da zai kula da su. Bayan sun shigo nasu akin wanda ya jagorancesu ya nuna musu akin da fa in, Each room, four cadets! You are brothers now. You eat together, you fight together, you win together. Yes Sir Sunan Haysam ya fara kira yana nuna masa nashi gadon. Haysam Abdul-rasheed Shehu bunk na asa, Imran Abbas kuma gadon saman Haysam. Da wani irin farin ciki Haysam da Imran suka kalli juna suna murmushi kamar azun, wannan lokacin ya tabbatar musu cewa rayuwarsu zata ci gaba da tafiya a tare kenan, abotar da aka ulla batare da tabbacin rayuwar waje aya ba bisa rahamar UBANGIJI da dubin zuciya ta tabbata.. Suma sauran kowa an bashi nashi. Basu zauna ba suka fara shirya abubuwansu a inda ya dace da yanda suke bu ata. Musamman ma abokai biyu da farin cikinsu ya kasa oyuwa. Da daddare bayan kowa ya kwanta, sai Imran ya an le o daga sama, yana magana a hankali da kallon fuskar Haysam da yay kwanciyar rigingine a gadonsa yay filo da hannayensa duk biyu. Zak... kana jin kamar rayuwa ta canza ko? e idanun Haysam yayi a hankali ya sauke su kan fuskar Imran daya le o ta sama. Wani an guntun murmushi yay masa. Kamar bazai ce komai ba sai kuma a ciki ya furta, Imran!. Tabbas rayuwa ta canza, canjawar data nisanta mu da ahalinmu da su ka ai muka sani a rayuwar jiyanmu. Amma da kai tare a nan sai ta zama mai ebe kewa da koyar da sabon darasi ar dariya Imran ya yi cike da jin da in kalaman sabon abokinsa Haysam. Hankali kwance kuma kai tsaye cikin son fidda abinda ke zuciya ya ce, Ni ma haka nake ji My Zak-Shadow, kamar kai ne garkuwata, an uwana jinin jikina da ya uya sai yanzu ne ya bayyana min kansa Hannu Haysam ya mi a masa, shima Imran ya mi o nashi suka ri e juna. Cike da tabbatarwa ya ce, Ni kuma ba zan bar ka ka fa i ba in sha ALLAHU Imran. Ba'a nan kawai ba, a ko inama. Ka sani kana cikin lagona da in har aka hareni ta hanyarka tabbas zan fa i, fa uwa irin ta kwanciyar da babu juyi a ciki. Ka ri e al awari, ka ri e amana, ka tuna wannan koda anan gaba A hankali hawayen da suka cika idon Imran suka gangaro suna iga a fuskar Haysam. Bai share ba, bai sakar masa hannu ba kuma har wani lokaci. A wannan daren kafin su rufe idonsu, sautin bugun tambarin al awarin ri e amanar juna ya gama zagaye zuciyoyinsu. Rayuwar soja ta gaske ta fara a cikin walensu, sun yarda su biyu sun riga sun zama abokai, aminai, kuma an uwan juna a cikin akin Alpha dake wannan makaranta ta NDA. arfe 4:30 na asuba aka busa ararrawa mai arfi. Duk da har yanzu duhu ne muryar aya daga cikin senior cadets ta farkar da su Haysam kamar sauran an uwansu sabbin alibai. Wake up, gentlemen! You ve got 5 minutes! Imran sarkin tsoro kuwa ya zabura yana neman fa owa a gadon, jikinsa sai rawa yake saboda tsoro. Haysam kuwa ya tashi da natsuwa kamar yanda ya saba a gida idan Mammah ta tashe sa. Gadon ya dafa cikin sanyi da muryar wanda ya tashi a barci ya furta, Ka nutsu Imran, ka sauka a hankali. Ka tsaya a gefe na, ka koyi komai a hankali da nutsuwa, gaggawa ta iye mutum take daga cimma burin nasara, haka Abiy na ke gaya min sanda ina yaro . Ya are maganar yana kama hannun Imran ya taimaka masa ya sauko a hankali. Suna fita daga akin iska mai sanyi ta bugi fuskokinsu, sai arar afafun alibai kake ji a kan asa. Wani senior mai arfin jiki ya tsaya a gaban su da fitilar hannu yana ta faman haskesu cikin ido da fa in, Down for push-ups! Let me see soldiers, not boys! Gudu suka fara iya arfi kamar yanda aka basu umarni. Tun ba'ai rabin filin ba wasu suka fara kukan gajiya. Imran kam da ba arfin zuciya yana neman kaiwa asa ne ma, amma Haysam ya matsa kusa da shi, yana fa in, Ka cigaba, kada ka tsaya Imran. Ka kalle ni kaji. Idan ka fa i ka sani nima zan fa Wannan magana ta arfafa shi sosai har ya yi mamakin kansa, an daga nan yaji kawai ya ara aimi har suna tafiya a jere da Haysam, Alhamdullah cikin nasara suka kammala round in farko. Koda aka an huta aka koma kuma nan ma bai sare ba sam. Dama shi oga kwata-kwata ko'a jikinsa. Komai Haysam na yinsa ne da arfin jiki da zafin nama kasancewar zuwa yanzu ya saba da wahalar rayuwa, to tallar da yake yi in nan zagaye kasuwa ai ba wasa ba. Wankau in Mammah, ibar ruwa. Hatta daka idan ta amsa tare sukeyi in dai yana gida. Wannan wahalhalu sun taka rawar gani a rayuwarsa warai da gaske har yake jin wannan warin gwiwar a yanzu da son arfafa irin su Imran masu rauni da gata yasa basu saba da wahala ba. Bayan an gama sunyi sallar asuba, suka dawo wajen rarraba breakfast packs. Imran yana jin kamar afarsa bata motsi da yau, sai Haysam ya kar i nasa kwanon ya ri e masa zuwa wajen zama. Sannan ya taimaka masa ya zauna yana jera masa sannu. A gefe aya, wasu senior cadets suna kallon Haysam cikin mamaki, sauran an uwansa duk a galabaice, amma shi a tsayensa yake kamar ma baiyi komai ba yana a nutsuwarsa da karfin hali, ga kuma yana da tausayi fiye da kowane sabo a cikin su. Wani daga cikinsu ya ce, Wato wannan yaron akwai wani abu daban a idanunsa, ku kula sam bashi da tsoro ko fargaba balle jin karaya kamar yanda sauran suka nuna Wanda ke kusa da shi ya ce, aryar banza, yo mi aka fara da mazan. Yau kawai kake masa wannan yabon. Ka bari suci watan farko dan Babansa wlhy sai ya rusuna wannan zafin kan nasa yabi iska Dariya suka sanya suna mai tafawa cike da sha iyanci. Duk abinda suke fa a kuwa a kunnen Haysam, amma ya basar kamar ba jinsu yake ba yana maida hankalinsa ga Imran dake shan ruwan zafi a wahale. Koda Imran ya kallesa sai ya sakar masa murmurshi, baki Imran ya an tura tare da fa in,
Chapter 36 · 0% Book details