Sashe 71
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
azhar, daga nan sukai zaman cin abinci da gwamna wanda Zak-Shadow ya i cin komai a wajen. Wannan ba sabon abu bane, dan duk wanda ya sanshi yasan ba'a ko'ina ake bashi abu yaci ba. Dan komai nashi da tsari. Kai da yawansu zasu iya ratsuwar basu ta a ganin ya zauna cin abinci a gaban kowa ba. Idan zai ci abinci yakan killace kansa ne yaci a nutse. Hakan da yayi ma ya ara saka jin shakkarsa a zukatan jami'an gwamnatin da akai zaman hadda gwamnan kansa. Dan bayan barowar su Zak-Shadow gidan gwamnatin sai da sukai ar gulma akan girman kan Zak-Shadow yayi yawa. Acewarsu yana Lieutenant Colonel kawai yana wannan isar da izza inaga ya zama General watarana, ai kowama ya shiga uku. Acewarsu wannan tsaf zai iya assasa juyin mulki a asa. Oho shi baima san sunayi ba, dan daga gidan gwamnatin airport ya wuce zai wuce Abuja. Jirginsu yana gab da tashi ma. Acan ya samu Ojo na jiranshi, shi ya saka ya saya masa tickets harda shi. Bai tsara matakin auka akan Ojon ba, amma ya udira sake jansa a jikinsa fiye da da saboda wani dalili nashi. Mintina baifi goma da zuwansa airport in ba jirginsu ya aga. Tafiyar da bata gaza awa aya ba suka sauka birnin tarayya. Anan airport suka rabu da Ojo, shi ya wuce barrak shi kuma ya samu su Ma'aruff sun zo aukarshi. Cike da farin ciki suka rungumeshi kuwa. Ojo dake binsu da kallon urilla ya mi ama Ja'afar ar briefcase in Zak-Shadow in dake hannunsa. Kafin ya ame tare da sara masa. Hannu kawai ya aga masa batare daya kallesa ba, amma yana lure da kallon urillar da yake ma su Ja'afar in. Ka an ya cije lips insa, a ransa yana raya (Yaro tsaya matsayinka kada zancen an duniya ya ru e ka. Dan in kace zaka tsalla gonar zuri'ata zan yanka maka kazar wahala ne kuma sai ka figeta da sili-silin gashi). A zahiri kam bayan mota da Ma'aruff ya bu e masa ya shiga ya zauna. Suma duk gaba suka shiga Ja'afar yaja motar suka kama hanyar gida. Gaba aya sun cika masa kunne da surutu kamar wasu ananun yara, shi dai yana jinsu da kunne kawai, wani lokacin kuma yakan yi murmurshi ko girgiza kai da fa in, ALLAH ya shiryeku a ta aice. A haka suka araso gidan.... Zantukan Ojo kaf sunje kunnen oga Jush shugaban ungiyar duhu. Dan haka ya tara meeting na gaggawa ga members ungiyar. Dama dukkan motsinsu a tsakanin nan a cikin meeting in suke kala-kala. A duk sanda ya bada umarni babu mai wasa wajen amsa kiransa. Dan haka a yanzun ma cikin gaggawa suka gama hallara. Kowa da kowa yazo idan ka cire Dagger da dama ba akowane zama suke zama da shi in ba sai suna bu atar hakan saboda a wajensu sunan karen farauta kawai yake amsawa. Sa anin kowanne zama yau oga ne ya fara magana kafin ma su tambayi dalilin zaman. Sai da ya fara kunna musu recording in muryar Ojo da aka tura masa duk suka saurara. Batare da jiran cewar wani a cikinsu ba ya cigaba da fa in, Zamu rushe wasu angarori na plan c Gaba ayansu kallon kallo suka shiga yi a tsakaninsu, cikin alamar tambayar juna a yanayin kurame suke an jujjuya hannayensu. Wasu ko na age kafa a da ta e baki irin na suma basu gane ba. Oga Jush dake binsu da kallo aya bayan aya yay aramar gyaran murya daya dakatar da gungunan nasu dake tashi a akin. Tsitt sukayi gaba aya, tare da maida hankali kansa. Sai da yaja sakanni cike da shan amshi sannan ya cigaba da magana. Kamar yanda na fa a bama bu atar wasu angarori na plan c kwata-kwata saboda na fahimci wani abu a yanzu Kamar mi kenan oga? Muna bu atar su Dagger a raye. Dan haka Viper ka dakatar da plan inmu na tura masu kashesu Yanda kace haka za'ai Sir. Amma miyasa kace hakan? Bayan kasan zaman mutanen nan a raye hannun sojojin nan komai zai iya faruwa, ciki kuwa harda sanin mu su wanene. Musamman ha arin yafi girma akan Dagger da shi ya sammu. Gara ma sauran su Dagger in suka sani Tabbas zancenka a kan hanya yake kuma kana kan dai-dai Viper. Amma abinda nake son ku tuna ba ko yaushe ake iya kama tsuntsu ta baki ba, dan wani tsuntsu ba hatsi yake ci wajen oto ba ababen cikin ruwa ne abincinsa. Ba kashe Dagger ne mafita ba, yin amfani da shi wajen kama mutumin nan ta wuya shine ya dace Sake kallon kallo suka shiga yi, dan su sam basu wani fahimci komai ba. Cike da izza Mr Specter sarkin an girman kai tamkar ogan nasu ya furta, Na fahimci abinda kake nufi Oga, kuma nayi na'am da wannan tsarin. Kai tsaye ma ni har wani yawan tunani yazo min Karo na farko Oga Jush ya saki murmurshi idonsa akan Mr Specter, shiyyasa yake matu ar son shi, dan shima akwai kwanya. Yana wani jinjina kai da lumshe idanu da bu ewa a lokaci guda ya ce, Yes Mr Specter muna saurarenka, wane tunani kayi? Wani arin girman kai Mr Specter yaji, dan haka ya gyara zamansa yana ajiye atuwar sigarin hannunsa a an bowl in da yake tara tokar. Sir ina ganin wannan sabon shirin zai dace da yin jifa da karan farautarmu a jikin fatsar da zata kamo mana wannan babban kifin. Ina nufin wannan yaron Ojo, dan aikinsa na yau sosai, sai dai gaggawa zata hana masa yin doguwar tafiya dan Zak-Shadow ba sakarai bane Murmurshi mai fa i Oga Jush ya sake saki, sai kuma ya shiga tafama Mr Specter, dole suma sauran suka zama an bin yarima akasha ki a kawai. Sai da sukai na fin sakan goma sha biyar sannan suka sarara. Oga Jush ya ce, Lallai ka gane mi nake nufi a sabon shirin mu na angaren haggu. Na angaren dama kuwa lokaci yayi da tafiyarmu zata gayyato manyan babba da jaka na asar nan, hakan ne kawai zai bamu damar farauto kifin cikin ruwa dake gadarar shi ISHA'U DUTSE NA RIMI ne BAKA FARGABA, to amma a arshe shima ai yace SAI NA RUWA ko A karo na farko saura ma suka fahimci darasin Ogan nasu, dan a tare suka kece da dariyar mugunta da na hango nasara. Sun sake tattauna abinda ya dace musamman akan fara horar da sabbin yara da maye gurbin Dagger a cikin yaransa da su Zak-Shadow basu kama ba da gaggawa, sai al'amarin Ojo da shima dole su gaggauta, daga haka taron ya watse zukatansu fes..... <><><><><><><> Tun shigowarsu harabar gidan Zak-Shadow ya zubama ba uwar motar dake fake a dai-dai ofar sashensu idanu. Koda Ja'afar ya kammala parking a inda ya dace har Ma'aruff ya fita ya bu e masa sashen da yake hankalinsa nakan motar dai, a karo na farko shima Ma'aruff in ya juya ya kalla motar, sai kuma ya juyo batare da jiran tambaya ba ya ce, Dada motar Momyn su Ismat ce, jiya tazo da yamma itama Kauda idanun nasa yay daga kan motar, batare da yace komai ba ya mi ama Ma'aruff in wayoyinsa biyu. Ja'afar ma daya riga ya fito can gefen ya bu e ya auki briefcase insa. A tare suka rufe motar, sai kuma suka kalli juna suna murmushi ganin ya nufi sashen Mammah. Da sauri sukabi bayansa sun an tafa kowa ya janye hannunsa yana yarfarwa da arin danne dariya duk a lokaci guda, sai kuma akai sa'a Dadan ya juyo zai kallesu ganin basu biyo shi ba. Da sauri suka gimtse fuskoki tare da zabura inda yake. Sha iyancin Ja'afar da Ma'aruff babu wanda bai sani ba, dan haka ma ya juya abinsa ya cigaba da tafiya suna take masa baya. Sallamar su ta saka Mu'azz dirowa a kujera da gudu yayo ofa, cike da farin ciki yake fa in, Oyoyo Dada na Guntun murmushi Zak-Shadow yayi, tare da tsayawa cak har Mu'azz in ya araso inda yake ya rungumeshi. Kan yaron ya shafa, dai-dai shima Ja'afar na kai masa rankwashi da fa in, an iya kenan, wato Dadanka ma kai ka ai, ai mu ri o aka kawomu gidan naga Ai rankwashin da yafi wannan ya kamata kai masa . Cewar Ma'aruff yana harar Mu'azz shima. Baki Mu'azz ya tura yana sake ma ale Zak-Shadow, dan in dai muguntar Uncle in nasa biyu ne ya saba da ita a gidan. (Mu'azz an Aunty Ummi ne, mahaifinsa ya rasu tun yana a ciki, dan watan Aunty Ummi in bakwai da aure mijin nata ya rasu, ba kowa bane face yayan Imran, rasuwar ta gigitata dama ahalinsa da su su Zak-Shadow in, har takai ta shiga wani yanayi na ciwo dole aka dawo da ita gida, a haka ta arasa rainon cikin ta haifeshi. Ko bayan haihuwar tasa ma ansha fama da ita kafin ALLAH yasa ta koma dai-dai ta cigaba da shayar da shi, sai dai rainonsa gaba aya Mammah da Mimi ne sukayi shi, har ya kai yaye. Ta jima a gida bata sake wani auren ba kusan shekara biyar dan tama koma karatu, sai da Zak-Shadow yay mata jan ido sannan. an gidan su Imran basu ta a nuna kwace Mu'azz ba a hannunsu, sun san yana samun dukkan gata anan gidan, sai dai kuma suma hakan baya hana suyi masa nasu gatan. Dan haka Mu'azz shine jika na farko a gidan tunda har yanzu matar Dada Nabeeha bata haihu ba duk da kuwa tare akai bikinsu da Ummi in a lokacin. Gashi a gidan sabon aurenta har ta sake yara biyu). Dada! Nima kaga Mammah ta kawo min sabuwar anwa. Sunanta Nimrah . Mu'azz yay maganar yana raba jikinsa dana Dada. Bai jira amsarsa ba ya bar wajen da an gudu. Inda Nimrah take ma ure a tsakanin kujera tunda sukai sallama ta tashi ta bu a a wajen dan har yanzu bayan Mammah da Mu'azz in ta i sakin jiki da kowa a gidan. Hannunta ya kamo cike da farin ciki ya ce, Nina taso ga Dadana da nake baki labari yazo Kafa a Nimrah ta ma e alamar bazataje ba.