Sashe 40
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 3 min read
kuma yarda nai zamana anan shi zai dinga zuwa. Karo na farko Haysam ya ago yana kallonta, idanun nan sun ka e jazur. Cikin acin murya ya ce, Kuma kin yarda Mammah? Rasama mi zatace masa tayi, dan gaba aya ya juye mata tamkar Abdul-rasheed a gabanta. Sai kawai ta girgiza masa kai. A'a ban amince ba Ajiyar zuciya Haysam ya saki tare da furzar da huci, harma abin yaso mata dariya amma ta gimtse. Daga ranar bata yarda ta sake masa batun auren nan ba, har hutunsa ya are ya shirya ya koma ya sake barinsu da kewa. Ya wuce da sati biyu aka aura mata aure da Alhaji Nura. Harga ALLAH ba son auren nan A'isha take ba, amma haka ta daure ganin Alhaji Nura mutumin kirki ne, baida damuwa bai da hayaniya kuma. Kamar yanda yay al awari kuma ya ri e mata marayu kamar ansa. Bai rabata da sana'arta ba ya kuma shiga gyara mata gida. Matsalar abinci babu ita, haka ma ya shirya Malam Sulaiman ya rakashi har Kaduna ya duba Haysam. Shi Haysam bai fahimci komai ba, a tunaninsa abokin Malam Sulaiman ne kawai. Dan haka ya gaishesa da girmamawa tare da sakin jiki yana amsa masa tambayoyin daya dinga masa. Rayuwa ta cigaba da shu awa Mammah ta sake samun kwanciyar hankali da mijinta. Tayi yau yaranta sunyi yau suma sunata karatunsu. Duk da dai su Ja'afar da farko basu saki jiki da Alhaji Nura ba suma sai da Mammah ta dinga musu fa a da nasiha. A haka Haysam ya sake zuwa hutu ya tarar da abinda bai masa ba. Amma da yake ya kwankwa i tarbiyya ya oshi haka ya danne a ransa bai ko nunama Mammah ba har hutunsa ya are ya koma. Tafiyarsa babu jimawa ciki ya bayyana a jikinta. Sosai Alhaji Nura ya nuna farin ciki mai tsanani da wannan ciki, dan matansa biyu babu wadda ta ta a ko atan wata shekaru fin goma-goma yana tare da su kuma sai Mammah a yanzu. Aifa kafin kace mi zance ya zagaye ko'ina, Mammah na samun gata iya gata a wajen mijinta kamar zai lasheta da wannan ciki, in dai kaga bata samu abu ba sai dai in batace tana so ba. Haka aka cigaba da rainon wannan ciki. Cikin Mammah nada wata bakwai abubuwa suka fara canjawa a yanda suke. Hidimar Alhaji Nura ta fara raguwa, hakama okin wannan ciki, kai takai yanzu sai yay sati bai le o gidanta ba. Tun mutane basa fahimta har aka fara fahimta, wasu suka fara fa in bai san haihuwa ne ai dama, wasu suce matansa ne sukai masa asiri, dan yaje ya tare a gidansu sai hidima yake musu. Al'amarin kamar wasa aramar magana ta fara zama babba, takai Mammah tayi wata guda bata saka Alhaji Nura a idonta ba. Su Ammar da suka bu i ido da shi suna kallonsa matsayin mahaifi sunci kukan har sun gaji sun ha ura. Inda ta godema ALLAH yanzu sana'arta ta zauna da afafunta, dan tunda ta samu ya ara mata jari ta sake mi ewa da afafunta. Ganin haihuwa ta kusa zuwa mata ta samu kawunta da batun abinda ke faruwa duk da tasan ya sani. uri ya bata da mata nasiha, ya tabbatar mata subi komai a hankali Alhaji Nura baya cikin hayyacinsa ne, dan al'amarin nasa akwai amshin gaskiya game da asirin da ake fa a matansa sun masa. Amma dai zai sameshi yaji mike faruwa. Jiki a sanyaye tace to ta koma gida. ________