← Book details Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 94

Sashe 26

Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

ku, ku danna wannan link din domin yin magana da ita kai tsaye. Ko ku neme ta a number wayar ta da take asan rubutun nan._ INSTAGRAM https://www.instagram.com/leemars_delicious?igsh=MWRzZWtnYXM4ZHB2dw%3D%3D&utm_source=qr CALL/WHATSAPP wa.me/2349030398006 TIKTOK https://www.tiktok.com/@leemars_delicious?_t=ZS-90ZQJ2mNJKc&_r=1 Kar ku sake a baku labari, siyan na gari mai da ku i gida. __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ........Sakanni sun zama mintuna, mintuna sun koma awoyi, awoyi sun riki e zuwa kwanaki, kwanaki sun ha u sun zama sati, satittika sun dun ule zuwa wata, wattani suka ha a shekara. Shekaru sun cigaba da shu awa. Har amarya Yakura ta cika shekara uku a gidan Abdul-rasheed. Bata samu ciki ba har yanzu, hakama A'isha tunda ta yaye Haysam shekara biyu kenan bata samu wani cikin ba. Abdul-rasheed kuwa nata sake samun aukaka a wajen aiki da kasuwancinsa na inki, dan zuwa yanzu ya koyar da yara da yawa aikin tela, kuma Alhamdullah suma suna cin gashin kansu, ga shagon saida kayan inki ya bu e duk sati Nasiru na aiko masa da kaya daga kano. Wani lokacin kuma yaje da kansa yayo daga nan yayo zumunci ya siyama Inna kayan abinci ya dawo. Zuwa yanzu kusan duk awainiyar zuri'arsa ta dawo kansa ne. Yayima su Baba yayima yayunsa da annensa, yayi ma dangin mahaifiyarsa, yayima dangin matansa. Sannan ya sauke hakkin gidansa. Haysam yaro an shekaru hu u a duniya, ya tasa abinsa masha ALLAH, kyakkyawa mai lafiyar jiki ga gatan iyaye dana kakanni, ya tashi yaro mai shiru, mai son karatu da tambaya. Wayonsa ya girmi shekarunsa, damma baida surutu ne. Yana da shekara biyar a duniya kwatsam a an tsakanin sai ga A'isha da ciki, ya salam zo kaga murna wajen Abdul-rasheed da Yakura dama su Baba, cikin A'isha nada wata biyu itama Yakura ta fara nata laulayin, ya rabbi, rasa ina Abdul-rasheed zai saka kansa yayi dan farin ciki, dan harga ALLAH yana matu ar son yara. Kamar yanda A'isha ta fara samun ciki itace ta fara haihuwa, santalelen yaro namiji a wannan karon ma, mai kammani da Abdul-rasheed shima. Ansha shagali yaro yaci suna Ja'afar. Ja'afar nada wata biyu da kwanaki itama Yakura ta sauka, itama dai ta santalo nata namijin mai kama da Abdul-rasheed, shima dai yaci suna Ma'aruff. Haysam cike yake da farin cikin samun anne da suka tashi tamkar tagwaye, dan kuwa ma tagwayen ake kiransu. Su Ja'afar nada shekara aya aka saka Haysam makaranta, dan kuwa ya cika shekaru shida a duniya cif. Duk da kuwa kafin ma sakashi makarantar tuni ya fara aukar karatu a wajen mahaifinsa da ma A'isha da Yakura. Dan Abdul-rasheed tsaye yake akan tarbiyyar Haysam, sannan akwai sha uwa a tsakaninsu mai girman gaske. Akoda yaushe zaka sameshi zaune a gefen mahaifinsa yana sauraron karatun Al ani ko labaran tarihi na Annabawa da jarumai. Hakama sauran litattafai dai-dai fahimtar yaro mai irin shekarunsa. Duk lokacin da mahaifinsa ya karanta masa tarihin jarumtar Annabawa data sahabban MANZON ALLAH (S.A.W) irinsu Abubakar As-Siddiq (RA). Abokin ANNABI mafi kusa kuma khalifa na farko, mai ha uri da sanyin hali Umar Ibn Khattab (RA). Khalifa na biyu, adalin shugaba jarumi kaifi aya. Usman ibn Affan (RA). Khalifa na uku, ya tattara Al-Qur ani cikin littafi, mai yawan yauta kuma mai sadaukarwa ga bayin ALLAH mabu ata. Aliyu ibn Abi Talib (RA). Khalifa na hu u, kuma uwan ANNABI, jarumi da baya tsoro sai dai kafirai suji tsoronsa, dan ya basu wuta iya wuta a filin daga, Mijin Nana Fateema ar MANZON ALLAH (S.A.W). Ga su Abdulr-rahaman ibn Awf (RA). Irinsu Sa'ad ibn Abi Waqqas (RA). Talha ibn Ubaidullah (RA). Zubair ibn Al-Awwam (RA) an uwan Ummul Muminin Khadija. Bilal ibn Rabah (RA), mai kiran salla na farko jarumi na gaske. Salmanul-farisi (RA) da ire-iren su da yawa da in lissafosu zamuyi da irin rawar da suka taka a musulunci da tsayawa kusa da MANZON ALLAH mu kammu mun san jarumai ne abin koyi da ba Haysam kawai ba anmu ma ya kamata ace muna basu tarihinsu domin su tashi da burin koyi da su ba zindi an wannan zamanin ba da yaranmu ke koyi da su koyi mara amfani da amfanarwa. A angaren hikayoyi yana bashi irin nasu Iliya an Mai arfi, Jatau an Mariya, Sarkin Zamani, da makamantansu. Dan a wancan lokacin, ana ya asu a gidajen rediyo kamar su rediyo Nigeria da jaridu irinsu Gaskiya tafi Kwabo da sauransu. Irin wa an nan tarihi da hikayoyi sunyi tasiri matu a a zuciyar Haysam, dan har yana ji a ransa yana son yayi koyi da su wajen hidimtawa addini. Sai dai abinda ke saka lissafinsa ru ewa shine zamanin da yake sa anin nasu ne, tunda shi bai zo zamanin ya e-ya e ba. Dan haka sai yayta jerama Babansa tambaya. Abdul-rasheed kuwa baya gajiya da bashi amsa, tare da kawo masa misalai akan idan su anyi ya e-ya e a zamaninsu shi kuma zai iya zama an sanda, ko SOJA ko wani dai aikin kaki domin bama asarsa gudummawa. Ba wani fahimta Haysam yake da yau ba, amma hakan na sashi jin eh lallai zai iya hakan. A haka ya fara makaranta sai abubuwansa suka sake fa a. Bayan yaye annensa Ja'afar da Ma'aruff iyayensa sun sake samun ciki kusan a tare, amma Yakura ma ta riga A'isha a wannan karon, dan haka ta rigata haihuwar a namiji mai kama da an uwansa. Shima dai yaci suna Bilal, bayan wata uku da kwanaki itama A'isha ta haihu mace. A karo na farko Abdul-rasheed ya samu mace, dan haka taci suna Halimatu mahaifiyarsa Iya kenan suna mata alkunya da (Ummie). Itama dai akasha shagalin sunanta. A wannan lokacin ma Yakura ta sa sake yin gwanne kuma, dan Bilal nada shekara aya ta sake samun ciki, dole A'isha ta cigaba da shayar da Bilal da Ummie a tare, aka bar Yakura da laulayin sabon cikinta har ALLAH ya kaishi haihuwa ta haifi mace itama da taci sunan Inna wato Karimatu suna mata alkunya da (Mommy). Bayan haihuwar Mommy babu jimawa UBANGIJI ya amshi ran Baba, jiyyar kwanaki biyu rak. Wannan rasuwa ta girgiza wannan zuri'a, barema Inna data koma kamar ta ru e. Haka dai akasha kuka da kai-kawo kowa ya ha ura a arshe. Ashe wata na tafe, dan Inna na cikin takaba itama dai ciwo yay mata tsanani, ta matu ar sakama kanta damuwar rashin baba, ashe itama ciwo ne na tafiya, itama dai a cikar wata na shida da rasa baba tabi bayansa. Su Abdul-rasheed suka sake gigicewa da anta. Nan ma akasha kuka kowa kuma ya ha ura, shike nan gida ya fa i, an bar su Abdul-rasheed daga su sai dangi. A lokacin Haysam nada shekara goma sha aya a duniya. Yana primary 5, yana shirin gamawa kenan ma, tunda aji 5 ce a lokacin 1983. An gama kukan rasuwar su Baba da Inna babu jimawa itama mahaifiyar Yakura ta rasu, haka suka kwasa sai Maiduguri. Satinsu guda suka dawo ko muce A'isha da Abdul-rasheed suka dawo tare da yara. Yakura sai data ara kusan sati biyu ma sannan ya dawo. A lokacin A'isha ta sake samun ciki, cikin daya dinga bata matu ar wahala, daga arshe ma ta haifeshi a bakwaini, har sai da aka sakashi cikin kwalba na wasu watanni, ita kuma tasha jiyya tamkar bazata rayu ba, mafi yawan mutane idan suka je dubata gani suke kafin su araso gida za'ace A'isha ta rasu. Abin birgewa kuma Yakura ke jiyyarta kai bakace kishi bace ba sam. Haka dai tasha fama tsahon watanni kafin ALLAH ya bata lafiya ta mi e tamkar ba'ayi ba, dan kafin cikar wata biyu jikinta ya murje sarai harta fara dawo da ibarta. Kamar jira sai ita kuma Yakura ta shiga nata sabon laulayin cikin. A yanzu dai Abdul-rasheed nada a bakwai a duniya. Haysam, Ja'afar, Ma'aruff, Bilal, Ummie, Mommy, sai autan A'isha Ammar. Family ya ha u sai dai Alhamdullah. Ga ku e Abdul-rasheed na samu na ban mamaki, sai dai baya tarawa kullum cikin hidimar an uwa yake da ansu, kai hatta ma wafta da abokai cin arzi insa suke yi, dan mutum ne mai yauta da hidima. Ga dai ku i ana wasa da su, amma idan ka cire gidan da yake rayuwa bai ajiye kaddarar komai ba. Hakan kuma bai ta a damunsa ba bai ta a kuma damun matansa ba. Ba shi kawai ba su kansu sun koya daga alkairinsa, ko baya kusa sukan yi a madadinsa da an abinda yake basu da sana'o'in su duk da kuwa ananu ne. Abdul-rasheed bai ta a sayen kaddara koda ta fili ya ajiye ba balle gona idan ka cire ta mahaifinsu da yake nomawa, bayan rasuwarsa kuma aka raba musu gado, daya tashi sai ya barma annensa da suke aki aya ma kason sa. Dan a lokacin ne autan akinsu ke shirin yin aure, shima dai ya gado Abdul-rasheed duk tsawon lokacin nan yana yawon karatu ne, daga arshe dai zaiyi aure a yanzu cikin wannan satin. Auren daya taka rawar gani mai ban tsoro da razanin zuciya a zukatan zuri'ar Abdul-rasheed Shehu Isa Kobi dama al'ummar anguwa, kai harma duk wanda yasan wannan sunan wannan aure ya kawo masa tarihin da bazai manta da shi ba......... Shin miya faru ne a wannan aure daya zame ma wannan zuri'a tambari da bazasu manta ba? Wane ajiyayyen tarihi wannan aure zai bari haka? . Kudai kumuje zuwa dan har yanzu a shinfi a muke. Cakwakiyar da shagulgula na gaba _Zaku sameshi a wa an nan manhajar guda uku in sha ALLAHU._ *_NIGER - (500 CFA) (Telegram vip 1000 CFA)_* *_+227 98 94 12 81_* *_My NITA_* *_Zaku iya kuma tura katin Airtel na asar NIGER shima 500 CFA ko vip telegram 1000 CFA_* _Shaidar biya *_Whatsapp number_* *_+227 98 94 12 81_* *_TELEGRAM VIP 1000 (1K)_* *9032345899* *_Moniepoint MFB_* *_BILKISU MUSA IBRAHIM_* *_KATI MTN (1k)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya: *_Telegram Number 09032345899_* *_AREWABOOKS (Vvip)_* *_Chapters & Audio_* @BilynAbdull *_WHATSAPP (500)_* *1487616276* *_Access Bank_* *_Bilkisa Ibrahim Musa_* *_Kati MTN:- (500)_* *_09032345899_* *_Shaidar biya:-_* *_Whatsapp Number +234 805 568 7449_* *_MASU SON A TALLATA MUSU KAYANSU SUMA_* *_WhatsApp Number *+234 805 568 7449* *_Telegram Number *+234 903 234 5899* *_ALLAH ka gafartama iyayenmu *_Typing A A RUWA.....!! *_Bilyn Abdull ce
Chapter 26 · 0% Book details