Sashe 60
Kida A Ruwa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Imzeedventure Kisha mamaki idan baki da kudin siyan kayan Yaro sabo to zaki iya yin order na kayan gonjo dinta mai Kama da sabo! Idan kuma kayan kitchen ne baki da kudin siyan nan take to har adashi GATA tanayi IMZEEDVENTURE wata sabuwar duniyar yale- yale ce da ayatarwa da mata sukafi bu ata musamman walisa da son gwangwaje kawunansu harma da iyalansu. Gaji ya kori ji, garzaya ki shiga wannan link in namu dai domin ganema idanunki. https://wa.me/message/TFJVQFKRUBGBJ1. Koki tuntu emu ta wannan layin *_+234 707 753 2253_* Muna da account aTikTok@imzeed _venture. https://www.tiktok.com/@imzeedventures?_t=ZS-90A6JG1PvXe&_r=1 Karku bari ayi babu ku, Nima Bilyn Abdull tuni na antaya __________________ *_TELEGRAM GROUP_* https://t.me/+erpSeN2ssqgwYTdk *_WHATSAPP CHANNEL_* https://whatsapp.com/channel/0029VbBMI7RLY6d9zU893c1F *_TIKTOK_* https://vt.tiktok.com/ZSDkPqMm1/ *_INSTAGRAM_* https://www.instagram.com/invites/contact/?i=fc2g6shv1k6u&utm_content=p17zzzv ______________________ ........Layukan waya ne a ciki har hu u. Suma ajiyesu Imran yayi, sai kuma ya juya yana kallon Umman Nimrah dake kallon ku in da mamaki, dan ita kam bata san da su ba sam, kai kayan ma ta kasa tuna randa mijin nata ya sakasu a jikinsa.... Ko zamu iya ganin wayarki? Ajiyar zuciya ta an sauke na katsewar tunaninta, ta girgiza masa kanta. Banda waya Mijinki fa? Shima baida ita, sai dai ranar yake cemin yana son ya saya mana ni da shi, zai ba Tanimu aninsa idan zai dawo sai yazo mana da ita. To ban sani ba ko ya ba Tanimu sautin a randa zai tafi Kota wani baki ta a gani a hannunsa ba? Eh to sai ta matar Tanimu, itama kuma sai in Tanimun ya kira dan suyi magana take kawo mana, ta kuma kaima Inna. Daga ba wannan ba ban ta a ganinsa data kowa ba, kai gidan nan ma duka daga Tanimu sai matarsa keda salula Zaki iya fa a mana abokan mijinki da kike yawan ganinsu tare, har suke zuwa gidan nan Abashe ne kawai abokinsa. Kuma ALLAH yay masa rasuwa watanni goma sha aya kenan. Kowa da shi kawai ya sanshi tun yana saurayi Ina ne gidan Abashen? Da nan makwaftanmu ne, amma yayi sabon gida sun koma can farkon gari shekara uku kenan? Kai kawai Imran ya jinjina mata, sai kuma ya juya yana kallon Zak-Shadow da duk ke nazartar tambayoyin da Imran kema Umman Nimrah da amsar da take bashi. Canja harshe Zak-Shadow yayi, cikin harshen turanci yace, Dole a sake sabon bincike a gidan nan. Kayi kiran Captain Musa yanzun nan . Daga haka ya mi e ya fita yana latsa wayar hannunsa alamar zai yi magana da wuni... Kandala matar Tanimu dake la e tun shigowar su Zak-Shadow a bayan katangarta data raba sashensu dana su Umman Nimrah na ganin su Imran sun fita itama tabar wajen sa af-sa af. Sai faman tafa hannaye take da ri e ha a irin na gulma. Magana ce ke tsikarar mata uwawu gashi babu damar fita kai gulma ma wafta, ta gagara zaune ta gagara tsaiwa. Zuwa can dabara ta fa o mata, wata ar dusa data shanya akan rumfar dabbobinta ta auka ta juye a roba. Sashen ayar facalarsu da mijinta da su Tanimu ke uba aya ta nufa. Tun daga farkon shiga ta ce, Ramma ga dusa, naji kina jaje azun na gagara tashi ne na mi o muki ita tun azun ina fama da ciwon kai Ramma da tasan batai jajen dusa ba ita dai ta bu e baki zatai magana. Da sauri Kande ta yafta mata ido alamar tai shiru. Sai ko ta wayance itama ta ce, Kai aiko na gode. Tun azun dabbobina ke kuka na rasa tudun dafawa asa- asa Kande tace, Ramma akwai matsalafa a gidan nan Matsala ai dama cikinta muke Kande. Yau kwana biyu mazanmu na can a hannun sojoji Ai inaga gaskiya ta kusa bayyana, ALLAH ya kusa wato mana su. Tun azun wannan bahagon sojan da kallon fuskarsa kawai tashin hankali ce yazo gidan nan. Naga ya auki waccan yarinyar ar gori ya fita da ita, tunda kuma suka dawo suka tsare uwarta da tambayoyi tana basu amsa, har kayan sakawar Yaya mai kifin aka sakata ta akko suka zazzage, naga sun fiddo ku i sabbi fil ari biyar, da layin waya. Kin kuma san bashi da waya ai. Gashi can sun sake fita dai.... Ramma dake zazzare ido ta ce, Mun shiga uku Kande, kar dai ana zaton wuta a ma era a ganta a masa To aiko da alama can in take. Yo ai biri yayi kama da mutum, ki kula a kwanakin nan basa shan koko kullum sai shayi da burodi, ranar ar naba su Laminu labari wai sunci tsire da daddare babanta ya sayo. Ke dama ki kiyayi mutum sumu-sumu wlhy abin tsoro ne. Randa Tanimu zaiyi tafiyar nan da daddare yake gaya min ya ranci ku i a wajensa har dubu arba'in, naita mamaki har ina jin haushi, ashe-ashe ku in bana ALLAH bane Kande ni abinda ban gane ba anan. Kenan dai shine ya kawo mana wannan masifar da aka samu shekaran jiya cikin gidan nan? A to ke da mi kike tunani, shine mana. Dan bala'i ya rasa inda zaije ya ajiye sai akin tsohuwarsa, yanzu da wannan abun daya kashe mutane a Gangare ne a ciki tunda ance fashewa yake shi ai kinga shike nan ya kasheta ko yama iyanta asara. Maganinta itama, badai tafi sonshi da arsa ba kamar shi ka ai ta haifa, mai mata wahala daban wanda take riritawa daban Salati kawai Ramma take tana arawa, dan maganar ta girgizata matu a. Kasancewar ita babu wani jin haushin su Umman Nimrah a ranta ita tausayinta ne ma ya kamata wlhy. Ka da e baka haihu da mutum ba sanda kuma ALLAH ya fara baku ace ga wannan masifa mutum nayi, ga yarinya mace, idan wannan magana ta fita wazai aureta a wannan garin basu da ba'a manta abin gori.... <<<<< >>>>> angaren su Imran mintuna talatin ba'ai ba Captain Musa ya iso da wata tawagar soji, da karnuka. Sai da suka mi a gaisuwa ga Zak-Shadow dake a ofar gida har yanzu yana waya sannan suka shiga cikin gidan. Kamar yanda ya bada umarni haka sojojin nan keyi, bincike ake mai zafi da yafi na farko har a jikin bango da ramin eraye ba'a bari ba. Kai saida takai hatta ledar asan akin Umman Nimrah sai da aka kwaye gaba aya, da ledar sama da akai kamar silin. Cikin filos ba'a bari ba. A ayan akinsu da take ajiye-ajiyen kayan aiki da icce sai randunan ruwa sai da aka fidda komai. Wani guri ne ya nuna kamar an tona aka maida asa aka rufe Zak-Shadow yace a tone shi shima. Haka suka shiga tonawa kuwa, abin mamaki sai ga tunkunyar asa, ana bu e murfinta sai ga ku i masu yawa a ciki kusan cike. Nan fa aka shiga fiddosu bandir-bandir sabbi Hakama a cikin akin Umma an ara samo ku i cikin katifar rimi ta gadon da yake kwana, harda wayoyi har biyu. ALLAH sarki Umma zuwa yanzu kuka take sosai, hakama Inna sai surutai take kamar wadda ta zautu. Tana son baban Nimrah sosai fiye da sauran yaranta musamman yanda bashi da yara sosai in nan. Duk da kuwa Tanimu yafi yautata mata da yi mata hidima a rayuwa, shi ba in halin matarsa ne yasa bata sakewa da shi, itako Umman Nimrah tana mata abu kamar arta. Idan ma ta nema abu Baban Nimrah in bai mata ba ita takanyi a madadinsa batare da Innar tasan ba shine yayi in ba. Bincike na biyu shine gidan abokinsa mai rasuwa Abashe, inda su Zak-Shadow suka gane shine gidan matar nan mai yara marayu da suka fara samun abubuwa tace ita kuma bata san da su ba. Ashe kuwa da gaske bata sani in ba. Dan sai yanzu ne da zance ya kai ya kawo akan lamarin Baban Nimrah in ta tuna ya kawo musu hatsi kusan sati aya kenan, da yake tunda mijinta ya rasu haka yaketa awainiya da ita da yaran babu gajiyawa, randa ya kawo hatsin yace babban yaronta da yaci sunansa suke kira da Aboki yaje ya amso musu kifi. Tabbas taga yaron nata da bako bayan ledar kifi, koda ta tambayesa sai yace mata Baba ne ya bashi ajiya yace zai amsa ranar kasuwar Gamau. Itako bata maida hankalin sanin minene a ciki ba yaron ya shiga da bakko akinta ya ajiye. Bako ta sake tunawa ba sai yanzu ma. Gari fa ya auki sabon tashin hankali. Dan duk wanda keda ala a da Baban Nimrah sai da aka kamashi a wannan yinin, hatta wajen kifinsa da inda yake zuwa sari a can cikin local government insu sai da aka bibiya. Zuwa dare sai ga an uwansa na nan gidansu duk an sakko, sai dai banda Tanimu dan basu gama bincike a kansa ba. ALLAH sarki Umman Nimrah idan ka ganta abin tausayi, wuni aya duk ta susuce ta fita a hayyacinta. Dan zuwa dare ma zance ya gama baje gari dan ma akwai sojoji da sukai musu takunkumin hana yawo barkatai an uwanta sukazo suka tafi da ita harda Nimrah bisa umarnin mahaifinta dattijon arzi i, babban malami ne a yankin ma ba garin kawai ba, dan bazasu so abin kunyar da mijinta ya aikata ya shafeta ba, musamman da matan gidan suka fara mata habaice-habaice da yada magana a kai-kai ce bisa jagorancin Kande matar Tanimu data fara ya a maganar, dan ma dawowar mazan gidan ya sata komawa tai la was ganin babu nata mijin itama.... >>>>>><<<<<<< A sansanin su Zak-Shadow cikin tantin Imran da bai cika zama ba ake tsare da su Baban Nimrah, zuwa safiya ake son fita da su daga jejin zuwa birni, ana ara tantance wanda basu da ala a da al'amarin ne musamman wa anda aka tattaro yau da rana. Kwanaki na uku kenan bayin ALLAHn nan su Zak-Shadow basuyi barcin rabin awa ba. Yaransu da manyansu tsaye suke akan afafunsu. Kai ko abincin kirki basa ci sai an itatuwa. Duk mai imani ya gansu sai ya tausaya musu. Amma a haka muda muke kwance a gidajenmu muci mu oshi mu kunna tv muyi kallo, mu hau gado muyi barci har muke iya zagin jami'anmu da kallonsu muce basa aiki. Musani ganin jami'an dake ofisoshi zaune, da wanda ke yawo akan hanya suna nuna wasu