← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 89

Sashe 9

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nasir yace eh shine yace kada tai abinci da kanta sai dai ayi a bata sbd aikin g'idan da yawa ba lallane ta'iya ba' shikuma bayaso ta wahala.

"Shiru Aisha tai.

"Nasir yace ni zantafi saina sake dawowa.

"Aisha tace to shikenan' komawa tai ta shiga toilet tai wanka h'ade da alwala tazo ta fara sallah.

"Nasir yana fita dakin Fatima ya shiga ya sameta zaune akan sallaya tana lazumi' duk da shigowar da taga yayi besa ta yanke ba cin gaba da lazuminta tai.

"gani h'aka Nasir yace ni dai zantafi Fatima' a lokacin ne ta shafe addu'a snn tace yanxu dan Allah alhj abinda kakeyi ya dace kenan? girma fa kakeyi ba komawa baya ba' k'uma abinda kake aikatawa baka tsoron wataran a aikatawa yar'uwa?

"Nasir yace Fatima kenan yanxu sbd Allah me k'uma na aikata? ke kullum baki rabuwa da zargi' idan kina tunanin wani abu na kawo mata wlh ina shiga g'idan nan d'akin kine na fara shiga snn naje d'akin ta....

"shigawar yarane yasa takasa meda masa mgn' rungumeshi sukeyi suna baba oyoyo baba' baba ina katafi bamu ganka ba bb?

"murmushi Nasir yai snn yace doughter kenan wani aiyukane suka shami kai amma in Allah ya yarda nakusa kammalawa ina kammalawa zandawo mu zauna tare kinji ko...

"kafin ta b'ude baki tai mgn Fatima tace ke fita kinaba gun.

"Nasir yace nima tafiya ne zanyi saena sake dawowa.

"Banza dashi Fatima ta mike h'ade da tada kabbarar sallah taci gaba da sallarta' shima dayaga h'aka fita yai yai tafiyarsa.

"Itako Aisha tana idar da sallah alkur'ani ta dauko tafara karantawa' saida ta dade tana karantawa snn ta'eje tafara kwararowa mijinta addu'a h'ade da iyayenta snn ta shafe addu'a komawa tai gado ta kwanta amma ba bcc takeyi ba.

"Tunanin iyayenta ne ya f'ado mata a zuciya'ita kanta batasan lokacin da tasaki wani kuka ba' cikin kukan ta dauko wayarta ta duba ko akwai kudi a ciki' tana duba gani tai babu ko sisi' medawa tai ta eje kai da gwiwa ta h'aka taci gaba da kuka.

"Misalin 10AM Fatima na zaune a parlour taji shigowar mutani g'idan' da sauri ta mike d'an mekawa taga ko su waye.

"Tana lekawa wasu mutani ta gani turkaka duk mazaje ne su biyar' salati tai ta sanarwa ubangiji' kafin tarufe baki har su shigo cikin g'idan.

"Titsiye Fatima sukai a parlour h'ade da tambayar ina maigidanki? Cikin rawar jiki Fatima tace bayanan.

"Daya daga cikin su yace ina d'akin sa yake? Da hannu Fatima ta nuna masu' sukace da'ita muje' suna gaba tana baya suka shiga d'akin' suyi bincike iya bincikensu amma basuga komai ba' sukace muje naki d'akin a nan ne sukaga sarkokin zinare da sauran kaddarorin da baza'a rasa ba.

"bayan sun gama kwashewa suka koma d'akin Aisha' Aisha na gani sun shigo tace innalallahi'wainna'ilaihim'rahu'un' snn tace daga ina k'uma? ID Card d'an E. F. C. C. Suka nuna mata daga snn bata sake cewa komai ba.

"Suma suka fara seaching d'akin a d'akin ta kam basu sami komai ba' sbd tariga tabawa Nasir ya wuce dasu' sunyi bincike iya bincikensu amma basuga komai ba' ita ko Aisha tana gefe inba kuka ba babu abinda takeyi' Gani basuga abinda suke bukata ba yasasu fita subar g'idan.

"Suna fita Aisha ta fashe da kuka sbd yadda suka walakanta mata d'aki' itako Fatima bala'i tasa tana f'adin wlh sisi bazaiyi ciwon kai ba' idan sai anbiyani.

"Su iyayen sai faman nimanta sukeyi amma basu samuta k'uma koda sun kira wayar maigidanta shima baya shiga h'akan yasa hankalinsu ya tashi sosae' amma sai bbnta yace tunda anji shiru lfy ne' sbd lfy ne ke buya inda ba lfy da tuni anji.

"umma tace h'aka ne alhj' Allah ya tsare ita a duk inda take' alhj yace amin' komai menene tunda AURE NE insha Allahu bazata tagaiyara ba ' himm kawai umma tace.

"Bayan zuwan E. F. C. C. g'idan Nasir da sati daya misalin 12AM dai dai sai gashi ya shigo kamar daga sama' komada ya tabi kofa yaji a kulle yake gam da key'gani h'aka sai ya zaga ta dai dai window Fatima yana kwada mata kira' a gigice ta falka' jin muryar Nasir yasa taja dogon tsuki ta koma ta kwata taci gaba da bccn ta.

"Gani h'aka yasashi komawa gun window Aisha kira daya ta mike Nasir yace nine Aisha da sauri ta mike taje ta b'ude masa kofa ya shigo cikin d'aki' bayan ya zauna ne ta b'ude frg ta dauko ruwa ta bashi h'ade da cup' koda ta xuba masa ruwan a cup k'adin kawai yasha snn ya'ije cup din.

"Har kasa Aisha ta duka ta gaidashi' amsawa yai babu yabo babu fallasa snn ta zauna' karewa d'akin kallo yai snn yace ya naga d'akin kamar a birkice.

"A lokacin ne Aisha ta sanar dashi mutani da sukazo bincike' Nasir yace nasan za'ayi h'aka amma ni dai banida abinda zance sai Allah ya kyauta.

"Aisha tace amin' ni inda zasu kwashe komai su barmin kai wlh zanfi kowa murnar h'aka amma sbd Allah wanga wacce irin rayuwane h'aka' mutum da g'idan sa da iyalinsa amma ya gagaresa zama.

"murmushin yake yai h'ade da cewa Aisha har yanxu ke yarinya ce' ko zan kwana ina maki bayani ba lallane ki gani ba' amma Allah ya naganki wani iri kodai bakijin dadin zama da Fatima ne? Ko k'uma wani abu take maki.

"Aisha na hawaye tace babu komai'kewarka kawai ke damuna'da k'uma kewar su yar'uwa na.

"Nasir yace shiyasa nace bilyaminu ya medaki garinku idan komai ya lafa ni da kaina zanzo na daukeki.

"Da sauri Aisha tace a'a ni babu inda zani na barka' ni nafiso na zauna dakai' Nasir yace to ai yanxu ba tare muke ba' sai lokacin dana samu hanya nake zuwa inda kike' Aisha tace eh na yarda a h'aka inda har zaka rinka zuwa lokaci - lokaci ina ganika.

"Shiru Nasir yai na dan wani lokaci snn yace Aisha kina sona?

"Kai kawai ta daga masa alamar eh.

"Nasir yace gobe duk yadda zanyi sai nayi na nimi kudin mota da zai kaiki garinku' ki shirya kayanki da safe cikin dare daidai wanga lokacin zanzo na daukeki mutafi na saki a mota kafin safe insha Allahu nasan kin isa garinku.

"A sbd yasa zansaki a motar haya sbd duk wasu yaran aikina da kika sani yanxu da h'aka babu kowa' kowa ya kama kansa sbd nima yanxu da haka ta kaina nake dan mafaka nake nima.

"shiyasa zan saki a motar haya ki tafi gida.....

"Cikin kuka Aisha tace ni babu inda zani' zan zauna a h'aka idan har zaka rinka lekowa ina ganika.

"Gani irin kukan da takeyi yasa Nasir dagota yai ta zauna akan cinyarsa snn yace waya kukan ya'isa h'aka banaso na sake gani wanga hawayen' hannu yasa ya share mata tass snn yaci gaba da cewa yanxu Aisha kin zabi ki zauna h'aka? Aisha baki tausayamin kada hakki yai min yawa Aisha.

"Aisha manna kai tai a kirjunsa tana ejiyar zuciya' shima rungumeta yai a jikinsa kamar yaramar yarinya' snn yaci gaba da cewa ni dama ba wani abu nake dubawa ba illa zamanki ke kadai gani nai kamar baki saki jiki a g'idan nan bane shiyasa' duk da nasan ko waye Fatima bazata cutar dake ba' amma kinsan halinku mata banlema ace kishiya dole wataran sai a hankali' k'uma kinga ba zaune nake a cikin ku ba banle idan naga wani abu zai shiga tsakaninku na kwaba yanxu duk da haka kin amince zaki zauna?

"Aisha tace eh.

"Nasir yace to shikenan' da haka ya lallaba yai ta bayan bukatarsa.

"itako Fatima gani 2AM yayi mikewa tai taje tai alwala tazo tafara jera nafiffilinta kamar yadda tasaba.

"Nasir yana tare da Aisha gani 4AM ya mike h'ade da dauko towel ya daura yashige wanka' bayan ya fitone yana meda wandosa ya mika mata towel din ta daura snn tashiga wanka.

"bayan ta fitone daga wanka ne tasa kayanta Nasir yace Aisha ni zantafi' shiru Aisha tai kanta na kasa' sbd tanaso ta tambayesa amma kuma takasa' Nasir yace yan'mata na yah! dai?

"A sanyaye Aisha tace dan Allah kanada dari biyu kabani? Nasir yace Aisha me zakiyi dashi? Aisha tace ummata nakeso na kira sbd munyi kwana biyu bamuyi waya dasu ba.

"Nasir yace Ayya wlh gashi dagani sai naira dari k'uma idan nabar nan bayanki dashine zanyi amfani na hau napep na karisa' Aisha tace dan Allah Yallabai ina kasamu gun fakewa? Murmushi kawai Nasir snn yace kada kisamu yan'mata na kimin ko.

"yanxu ga darin idan yaso ni saina hakura' da sauri Aisha tace a'a katafi dashi kawai ni na hakura.

"Nasir yace Allah kuwa ki karba' sbd bansan mgnr da kikeso kuyi dasu ba.

"Tace a'a ba komai bane dama gaisawane kawai zamuyi dasu' tunda hakane babu damuwa wani lokaci sai muyi.

"Nasir yace to shikenan Aisha nagode Allah yai maki albarka yasa kici gaba da wanga hali naki ta gari.

"Murmushi kawai Aisha tai masa' Nasir yace ni zantafi saina sake dawowa.
"Aisha tace Allah ya tsareka ya kareka aduk inda kake.

"Nasir yace amin mugode snn yafita d'akin Fatima yaje koda yashiga ganita yai tana sallah ' hakan yasa betsaya bata lokaci ba yai tafi yarda' har yakai bakin kofar parlour zai fita saiga Fatima tasha gaba na h'ade da hankadeshi ya koma da baya.

"Nasir yace Fatima menene h'aka k'uma? Fatima tace ina sarkokina da katuro aka amsawa? Da mmki Nasir yace sarkoki k'uma Fatima wasu sarkoki kike mgn akai? Fatima tace kafi kowa sani' kuma wlh bari kaji sisina bazaiyi ciwon kai ba' tunda ba kai kasiyemin ba ubana ne yasiyemin' idan haka kafitomi dasu kawai.

"Nasir yace Fatima kanki daya kowa?

"cikin tsawa Fatima tace kaina biyu ne ba daya ba.

"Nasir yace ubanwa kike ma tsawa? Wlh idan kikai wasa saina maki dukan masifa kafin nabar g'idan nan.

"Fatima tace bance bazan dukuba amma wlh in har kadukeni saina rama' Nasir yace ok ba kinada karfi ba?

"Fatima tace kada ban'iya ramawa da kaina ba wlh sai kudina ya ciremin ta kaici' domin wlh biya zanyi a ramami.

"Nasir yace ok bari na dukekidin k'uma kafin nabar g'idan nan inaso naga wanda zasu rama maki.
Chapter 9 · 0% Book details