← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 44 OF 89

Sashe 44

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

" zahradee yana shiga yasama kofa key'zainab na gani shigowarsa ta juya masa baya tai kamar me bcc' daidai cinyarta yasamu ya watsa mata mari' a birkice ta mike muguwa alguguma manafuka tashi".

"yanzu menayi k'uma sbd Allah?"

"Ina zakisan abinda kikeyi' Ashe dama duk wata shiga da fitata ido kike sami ko?".

"Eh d'in nasa ido d'in sai me".

"h'aka kikace ko?".

"eh h'aka nace".

" wlh zainab bantaba tsanarki ba irin yau, natsaneki banasonki zainab k'uma bana kaunar ganiki".

"sai me? wlh zhrdee da mgnr ka yakai zci danafi kowa murnar h'aka".

" kamar yaya?"

"kamar yadda ka dauka'.

" zainab ki kiyayeni fa".

"ko k'uma kai ka kiyayeni ba".

"wlh zainab inda badan su Hjy ba wlh dana nada maki dukan dasai kinkasa tashi".

" zhrdee kenan su Hjyn me a tunanina babu abinda su Hjy da Abba suka isa su hanaka' sbd bajin mgnrsu kakeyi ba".

"wahh! kike fadiwa h'aka?'.

" kai dakai nakeyi".

"kadai sann wanda zaka duka amma baniba".

"Dan karami tsaki yai h'ade da kwafa snn ya kwata".

" da safe kafin Abba yafita kasuwa sbd yasan halin Hjy f'ada yai mata sosae akan koda wasane kada tasake taiwa Aisha mgnr jiya tarabu da'ita kawai".

*"itama Hjy bata musa masa ba' shima kansa zhrdee yarage satar kwana ba kamar dah! ba' amma fa har gobe koda wasa besake taraiya da zainab ba".

"yau zainab ce da girki bayan ya gama cin abinci yazo kwanciya tace zhrdee".

" meye ne?".

"Dan Allah inaso na rokeka wani abu".

"batare daya kalleta ba yace ina jinki".

"Dan Allah g'ida nakeso naje gaida su ummata".

" babu inda zaki".

"Allah fa nace maka".

" sai fa kiyi ".

" zhrdee ya karisa mata mgnr ne da juya mata baya' tun daga snn bata sake cewa komai ba' itama kwanciya tai".

"da safe lkcn zainab tashiga gaida Hjy' dama dasafe dukkansu suna shiga gaidata' bayan sun gaisa zama zainab tai taki tashi' Hjy tace zainab lfy kuwa?"

"eh dama dan Allah inaso kisami bakine da zhrdee".

" lfy wani abu yafaru".

"a'a babu komai".

" to menene?".

"dama so nake naje g'ida gaidasu ummata'".

" shine kawai".

"eh shikenan".

" to shikenan yanzu jeki ki karisa aikin ki k'uma ki shirya cikin lkc sbd saiya daukeki a g'ida snn yakarisa kasuwa".

"to ngd Hjy".

"cikin murna zainab ta mike zuwa d'akin ta' tana shiga daidai lkcn zhrdee yana shirin shiga wanka' toilet ta shida ta h''ada masa ruwan wanka snn tafito' tana fitowa shikuma ya shige toilet d'in gani ruwa a h'ade kafa yasa ya ture ruwan ya zube akas snn ya h'ada wani yai wanka".

" kafin ya fito tun zainab taje kitchen ya h'ada masa abin karyawa duk da tasan ba lallane yaci ba' tunda bacin abincinta yakeyi ba amma be hanata dafa masa' gani Aisha a kitchen tai duk da batasan me takeyi ba amma tasan baya wuce abin breakfast take hadawa".

"suna h'ada ido Aisha ina kwana".

"shiru Aisha tai babu amsa".

" Aisha take fa nakeyi ina kwana".

"lfy klau' Aisha na f'adin lfy klau daga snn bata sake mgn ba saima juya baya da tai".

" itako zainab taci gaba da aikinta tana gamawa ta kwashe zuwa daki' snn zhrdee shima yafito kenan daure da towel gaban mirrow ya tsaya yana kallon kansa a madubi".

"tana ije tre d'in taje ta bayansa ji kawai ya anrrungumesa ta baya h'ade da cewa bari na shafawa mijina mai' duk da ba tsayine da'ita ba amma be hanata kwanciya masa a baya ba h'ade da kewaya hannayenta tana shageshi".

"doguwar tsaki yaja h'ade da cewa wlh idan baki sakeniba saina tureki' zainab najin h'aka ta kara lafewa a jikinsa".

"badake nakeyi bako".

" Dan Allah ma baka goge antabaka bama".

"na godime mara kunya".

" wlh zainab inda badan cikin dake jikinki bako himm".

"karisa mana'da saikayi me".

" wlh duka zanmaki' amma ko yanzu idan kika kureni saina farfasa maki baki".

"tsayuwa zainab tai h'ade da tokare kafa daya ta dauki hannu ta rike kugunta tana karkade jiki tana f'adin Allah ko' to bismillh".

" dawa kikeyi zainab?"

"da kai nakeyi".

" ni ko?'.

"Eh" kai d'in".

"ni ko?".

"Eh" kai ".

" kikace eh' a guje yabinta' yana cewa ai da kintsaya' ita k'uma tai parlour snn ya dawo ciki".

"tana fita tafara gyara parlour saida ta goge duk inda ya kamata snn tai shara tazo ta shige wanka'shima zhrdee dayake yai yai ra'ayin ci sosae yaci abinda bayan ya gamane yashiga d'akin Hjy sallamarta zaifita kasuwa".

" da sallama ya shiga har kasa ya duka ya gaidata h'ade da sallamarta zaifita kasuwa' Allah yabada sa'a yabaku abinda kuke nima nace alkairi duniya da lahira yai maku Albarka dukkanku".

"amin Hjy ngd'".

" har ya mike yawwa zhrdee ga zainab nan idan Allah inaso ka'ijeta a g'ida' idan kataso kasuwa sai kabiya ka dauketa kudawo tare".

"can kasa da murya yace to naji' k'uma dan Allah kadan samu abinda zaka bata kai tsaraba g'ida".

" naji kawai yace yafice' yana fita d'akin Abba yashiga suka gaisa snn yaje Aisha gimbiyarsa da sallama yashiga' Aisha na ganisa da sauri ta juya baya".

"Aisha kenan har yanzu fushi kikeyi dani? to ina kwana' kin tashi lfy?"

"tsaki tasake yimasa".

" Aisha ni zanfita nace saina dawo ko kina bukatar wani abu".

"still babu amsa' juyawa yai yafice zuwa d'akin zainab' yana shiga yatarar ta shirya tsaf' to manafuka alguguma kin fadiwa Hjy kinji dadi ko? sai ki tashi guje".

" batare data tanka masa ba' ta dauki mafiya suka fita yana gaba tana baya har sun wuce d'akin Aisha sai zainab ta dawo da baya da sallama tashiga Aisha na zaune tana buga mage a wayarta zainab tace Aisha".

'kai kawai ta daga mata amma babu mgn".

"zantafi uguwa nida maigidan namu bazamu dawoba sai yamma shine nace bari na sanar dake kada kiji shiru' sai mu dawo".

" juyawa kawai zainab tai tasa kai batare da ta tsaya sauraran abinda Aisha zata ceba tafice".

"da zcy ya diba Aisha batasan lkcn data kwada wayarta a bango ba wayar ta tarwatse wasu kwallane suka zubo mata gado ta h'au taci gaba da kuka".

"zainab na fita ta shige mota zahradee ya jasu' b'akin wani kanti ya tsaya bayan yai parking snn yafita zuwa cikin kanti siyayya yai sosae sabulai wanki dana wanka chocolate biscuits cake sweet dai sauransu yazo ya b'ude bayan motar ya zuba sukaci gaba da tafiya' ko kallon inda zainab ke zaune bayayi har suka isa' saida ya shiga cikin haraban g'idan snn yai parking suka fita b'ude baya yai ya dauko ledar tsaraban' gani zainab tai gaba da sauri yace ki tsaya".

" tsayawa tai ta jirasa snn suka shige tare' har parlour suka shiga da sallama lkcn duk kannin zainab na parlour a guje sukazo suka rungumeta suna f'adin Anty oyoyo zainab na murmushi zhrdee ma h'aka' yar'utansu me suna maryam tazo ta rungume zhrdee gani h'aka yasa shima daukanta".

"guje me d'an wayon cikinsu tashiga ta sanarwa inna Hulaira ga Anty tazo' saida inna tasa hijab snn suka fito tare' ganita yasa zhrdee mikewa tsaye bayan ta zauna ne shima ya zauna a ladabce ya gaidata h'ade da tambyar su Hjy da Abba".

" duk suna lfy sucema a gaidaku".

"ayya muna amsawa".

" mikewa inna tai taje d'akin Mmn zainab ta sheda mata zuwan su zainab snn tafita kitchen taje ta dauko ruwa da juice tabawa mame kanwar zainab takai masu parlour".

"shiru da taji alamar Hjy bataje gun su zhrdee ba sake binta tai d'akin dadina da yaya sanyi jiki wlh na f'adi maki sirikina yazo kifita Ku gaisa amma abu ya gagara".

"nifa kada ku dameni da wani sirikin nan kubarni na kare aikina tuku".

"Dan Allah yaya tashi kije idan kin dawo kya karisa".

"ke!! kifita daga idona daga ke har surikinki ba'a kanku akafara ba".

" abu ma harda gori' babu damuwa nidai Dan Allah aje a ganomi siriki".

"inna ta karisa mgnr NE h'ade da fisge zani da Hjy ke nikewa snn ta mike h'ade dasa hijab suka fita tare' ita tai parlour inda zhrdee yake' ita k'uma inna tai d'akin ta".

"tana isa zhrdee yasake mikewa taida ta zauna snn ya duka suka gaisa' suna gama gaisawa Hjy ta mike takoma d'akin ta' shima mikawa yai batare dayace mata komai ba yakami hanyar fita zainab na gani h'aka da sauri ta mike ta bishi har bakin mota' yana shiga mota ya tayar gani zai tafi yasa zainab cewa sweety dawani lkc zaka dawo".

" banza da'ita yai yaja motarsa yafice' itama be dameta ba sbd idan da sabo tasaba' juyawa tai takoma ciki gani yabar ledar da suka shiga dashi yasata tunanin kodai mantuwa yai dashi' hannu tasa ta b'ude gani sabulai ne dasu sweet yasace cewa kilan tsaraba ne' daukawa tai ta shiga dashi d'akin inna".

"tana ije kayan ta shiga d'akin mmn ta gaisheta snn ta dawo d'akin inna' kallo daya inna tai mata tagano cikine da ita' farfesun kayan ciki ta dibo mata h'ade da lemo kwakwa tanaci suna hira har tagama inna tace mame ta dauki plate d'in takai kitchen' bayan fita mame inna ke tambyarta yadda zamasu yake a g'idan su Hjy".

"nan zainab ta kwashe komai ta fadiwa inmarta harda kuka' gashi nafi Aisha kyautata masa amma baya gani kullum cikin gefenta yake ko a dakina yake baya hanashi mgnr Aisha bayan ma batasan yanayi ba' Dan ko kyatata masa batayi yanzu da h'aka ma sufi sati uku bata mgn dashi k'uma koda shine yai mata bata tankashi amma duk begani ba"..

" harda kece baku mgn?".

"a'a' bandani".

" to ai me sauki ne' kedai duk rintsi duk wiya duk abinda zaiyi naki ido' k'uma koda yai maki abinda bata maki rai Dan Allah ki daure' banda yawan fushi banle yakai ga gaba' koda laifine yai maki ki daure kinjiko?".

"naji inna".

" to kinadai gani yadda mukeyi da abbanku'".

"babu ruwan ki da'ita koda tana fushi kiyi banza da'ita kikama mijinki' mijine babu kunya a tsakaniku koda fushi yakeyi dake kada h'akan ya dameki kamashi ki rungume ki jashi da wasa har yasake ya biyeki".
Chapter 44 · 0% Book details