← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 89

Sashe 19

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Aisha tace kekika sawa ranki shiyasa nidae babu abinda yadameni dasu tunda Ina sonsa.

"Ni barima natafi sbd banga zansamu mafita a gunki ba.

"Ubaida tace lalla kam.

"Fita Aisha tai babu ko sallama.

"Mmkin Aisha yakama ubaida sosae.

"Da yamma saega Nasir yakirata ta wayarta' lokacin umma na parlour Abba h'aka yasa Aisha samu hanyar fita.

"Da sallama ta'isa gusa' shima yana ganita da fara'arsa ya tareta cikin girmamawa ta gaidashi' shima ya amsa.

"Bayan sun gama gaisawane yace Aisha nazo jin sakamako nane'ina fatan Allah ya amsami addu'ata.

"Cikin jin kunya Aisha tace babu komai na amince.

"Nasir yace alhamdullh Allah na gode maka.

"To yanzu yaushe zanzo naga Abba? Idan gaskiya a shirye nake.

"Shiru Aisha tai snn tace kabani kwana biyu.

"Nasir yace to shikenan.

"Aisha tace zanshige sae anjima.

"Batare daya tankataba hannu yasa cikin aljihu ya dauko bandir d'in five five hundred naira note yamika mata.

"Aisha tace a'a kabarshi kawai.

"Nasir yace idan ba rainawa kikai ba to ki amsa.

"Hannu biyu tasa ta amsa hade da godiya' snn sukai sallama.

"Aisha na shiga daga lungu tsayawa tai ta boye boye kudin snn ta karisa daga ciki'kai tsaye d'akinsu ta shiga da sauri sbd umma batasan da fitataba dama.

"Tana shiga d'akinsu kyakykyawar buya taima kudin snn tafito.

"Da dare zahradee yaso zuwa gun Aisha amma yanayin yadda yakeji ya hanasa zuwa'sbd ji yake kamar kirjinsa zai b'ude sbd azaba.

"D'akinsu ya shiga ya kwanta snn ya dauko wayarsa dama number Aisha yana dialled call ne kawai d'an nawa yai' a lokacin na kwance tana f'aman tunani ta'ina zata fara? Kawai taji wayarta yana ringing.

"Koda ta duba taga number zahradee ne tsaki kawai tai h'ade da juyawa wayar baya.

"Zahradee yai kira yakai sau'biyu amma Aisha bata daga ba.

"Gani bata daga ba yasa ransa sake baci' zubawa wayar ido kawai yai yana kallonsa' can wata zuciya yace me zaihana karubuta mata text message ka tambayeta ko akwai wani laifin da kai mata k'uma tanajin kunyarka bazata iya f'adi maka ba.

"Amma ta text tunda ba ganika takeyiba maybe ta'iya f'adi kama.

"Mikewa zaune yai ya jingina da bango snn yafara da.

**** ***** *****
Dear Aisha, The reason I write this letter to you I don't known what I did to you, If I call you, you did use to pick my cell, that is the reason I write this letter to ask you what I did to you? Pls tell me.
**** ***** *****

"Snn yai sending d'insa.

"Aisha najin shigowa text da sauri tadaga wayar' tana dagawa taga suna zahradee budewa tai ta karanta bayan ta kare tsaki tasakeyi snn tai hurgi da wayar.

"Shiru shiru zahradee zaiga reply yaji shiru.

"Sake rubuta mata yai yace Aisha I'm waiting for your reply.

"Koda tasake karantawa kamar jiya'dan batada niyar meda masa da reply d'in' kawai bude data tai taci gaba da chat d'inta.

"Shima da yaga tunani yana nima yimasa yawa hawa online yai' nan suka h'adu da Aisha.

"Yace Aisha"shiru' Aisha'shiru.
Bata tanka masa ba.

"U don't want to telk to me ba? Himm Allah ya kyau.

"A lokacin ne ta bude'gani sakonsa ta meda masa da cewa ba h'aka bane.

"To menene?.

"Kawai dae.

"Kawai dae me?.

"Look nifa ba yaro bane kada kinimi rainami hankali.

"Idan kinsan da wani abu a zuciyar gara ki sanar dani.

Aisha U don't care about me.

"Haba zahradee' wani irin tunani kakeyi h'aka?

"Aisha idan damuki nakeyi' Is better I should stop disturbing you.

"H'aba zahradee meyasa kai a rayuwa bakayiwa mutum uzirine.

"Babu wani uziri da zanmaki Aisha wlh akwai abinda kike kunlawa Aisha.

"H'aba zahradee meyasa kace bandamu dakai ba zahradee...

"Hakane mana Aisha' If you care about me let me see.

Zahradee banida lokacin ka.

"Iya kacin amsar da Aisha ta turawa zahradee kenan ta sauka' tana kashe data Nasir yana kira.

"Sbd bugun da zcyr zahradee yakeyi mikewa yai yashiga toilet yai alwala yazo yafara nafila yanakai kukasan gun ubangiji.

"Dan shine mekowa me komai me ikon yida hanawa.

Allah yasa mudace' mufi karfin zcyr mu.

"Zahradee yana sallah hawaye kawai suke kara kaina a fuskansa.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

MMN USWAN

Zanyi amfani wann damar wajan mika godiya ta ga masu backing din na nagode sosae Allah yabar kauna da zuminci. Kada kudamu ba komai bane gazawane kesa ka ka dauki fasaha wani ka juya' idan har kasan kai perfect basai kayi amfani da hikimar wani. Dan haka ina rokon dan Allah duk meyi yabari pls👏

1⃣8⃣

"Bayan zahradee ya'idar da sallah yai tahhiya h'ade da sallama' snn ya dauko carbonsa yai subhanallalahi wabihamdihi, adadi khalkihi, wa rida nafsihi, wa maidada kalimatihi, wa zinati arshihi, guda 100.

"Snn yai Subhanallai, walhahamdul lilla Allahu Akbar. sai salatin Annabi manzon (S.A.W.) guda 100. Snn ya karanta fatiha, Ayatul kursiyu, Amanar rasulu, Lakadja'akum. Snn ya daga hannayensa sama yana mai kaskantar da kansa da k'uma tawali'u ga Ubangijin rahma maijin kan bayijsa.

"Duk a likacin hawaye basu daena zuwa daga i'donsa ba.

"Yace Ya Allah ina mai tawassali da salatin manzon ka fiyayyen halitta Annabin rahma sallallahu alaihi wa sallam, tsira da aminci sukara tabbaba ga shugabanmu Annaba Muhammad (S.A.W.) da k'uma kyawawan sunayenka guda cassa'in da tara".

H'aka zahradee yaita jero su tun daga Allahu har Assaburu. Snn yace " Ya Allah ubangijin sammai bakwai, ubangijin kowa da komai mamallaki mulki ga wanda yaso, kai ne kashen annabawa wanda bawani bayanka.

"Allah kai ka halitceni ka halitfi Aisha, k'uma kai ka jarabceni da sonta ya Allah, Allah kafini sani abinda yake cikin zuciyarta Allah idan wani abu take shirin kunlawa a kaina ya Allah kada kabari ta cutar dani Allah,

"Idan Aisha alkairine a gareni Allah ka mallakamin ita a matsayin matata, idan k'uma ba alkairi bace Allah kaimin zabi mafi alkari.

"Ya Allah Kaine masani sirin dake boye' bansan abinda Aisha take nufi dani na' Allah kafi kowa sani yadda nakeji da Aisha a zcyta Allah, idan Aisha ba rabona bace Allah kada kabari sonta ya halakar dani har yakai ga sabamaka, Allah ka sanyamin sanyi a zcyta kamar yadda kasanyawa Annabi Ibrahim sanyi a lokacin da yake cikin wuta.

"Allah kai nabarwa zabi kaimin zabi mafi alkairi a tsakanina da Aisha.

"Bayan ya shafane ya dauki alkur'ani mai girma' ya b'ude Suratul Yasin ya karanta snn ya b'ude Suratul Rayman, da Waki'a snn ya rufe da Suratul Mulki.

"Snn ya bude Suratul Ali- imran (Sura 3 Aya ta 59) INNA MATHALA "ISAA "INDALLAAAHI KA MATHALI ADAM (A') KHALAQAHU MIN TURAABIN THUMMA QAALA LAHU KUN FA YAKUUN(U).

"Lalle ne misalin Isa a wurin Allah kamar misalin Adam ne, (Allah) ya halitta shi daga turbaya sa'annan kuma yace masa"Kasance" Sai ya kasance.

"Yana da'kyau kowani musulmi yazama yasan wayanga SURORIN' badan komai ba kodan biyan bukatarka a gun ubangijinka.

"Surorin suna cikin ( Suratul Ali-imran sura ta 3 aya ta 59)

"( suratul mu'min' sura 40 aya ta 68)

"Suratul yasin' sura ta 36 aya ta 82)

Allah yasa mudace.

"Yana shafewa wani irin sanyi yaji a zcyrsa' amm duk da h'aka bedae na ambato Allah a bakin sa ba' haka yaita tasbihi da f'adin Alhadumllah har 100' snn ya shafa yasamu gun ya kwanta.

"Tun daga lokacin zahradee yaji sauki a zcyrsa' duk da saukin da yaji a zcyrsa amma da zaran zai kira Aisha sae yaji abin yadawo masa sabo a zcyrsa.

"Duk kiran da zahradee zaiwa Aisha tana gani amma bazata daga ba har ya tsinke sai dae idan yagaji da kira dan kansa ya hakuri' h'aka k'uma koda sun h'adu a whApp zaiyi mgn har yagaji tana gani amma bazata tanka masa ba.

"Shima tunda yaga walakancin yana niman yai yawa yasashi hakura da kiranta'kodan bacin ran da yake kamashi idan yakirata shiyasa ya hakura.

"Duk da halin da yake ciki h'aka ya boye besanarwa iyayensa ba' yabarwa zcyrsa shikadae' gani baya zuwa yasa Aisha tai amfani da wann damar tabawa Nasir damar zuwa' daedae lokacin da zahradee yake zuwa ta medawa Nasir lokacin.

"H'akan yasa iyayenta basu luraba' mafi yawanci lokuta umma ce take tambayar zahradee'sae Aisha tace aikine yai masa yawa shiyasa becika zuwa ba.

"Umma tace dama hakane Ai idan aski yazo baki goshi yafi zafi' mudae fatanmu Allah ya tabbabar mana da alkairi yasa ayi a sa'a. Nidae a matsayina na mahaifiyarki Aisha bazan gaji da yimaki nasiha ba' Dan Allah Aisha kiwa mijinki biyayya kibar gani yana mutuwa maki babu yadda Allah baya juya al'amarinsa' biyayya da kwantar dakae nasa mijinki ya kara sonki fiye da yadda kike tsammani.

"K'uma ki rike iyayen mijinki tamkar sune suka haifeki.

"Hakan zaisa mijinki yaji ya kara sonki SBD kina wa iyayensa biyayya.

"Aisha kizamo mace ta gari mai koyi da shugsban matan aljanna' Aisha inaso a lokacin da aka kaiki dakin ki' inaso ki natsu da'kyau ki lura da abinda mijinki yakeso kuma ki lura da abinda mijinki bayaso' kirinka kwantar masa da hankali a lkcn da yake cikin damuwa' hakan yakesa kiji ance mace ta mallake mijinta' wlh aisha babu boka babu Malam ladabi da biyayya ma kawai sun isheki Aisha' kinjiko.

"Naji umma k'uma ngd.

"Umma tace Allah yai maki albarka yabaku zaman lfy.

"Shiru Aisha tai bata tanka ba.

"Yau sauran seven week biki duk g'ida biyu shirye shirye sukeyi' da safe kafin su Alhj da zahradee sufita kasuwa Hjy mmn zahradee tabi Alhj har d'akinsa lkcn yafito wanka yana yana Shafa mai' b'akin g'ado ta zauna' cikin raha Alhj yace gimbiyata yaya akaine?

"Murmushi hjy tai alamar nuna jin dadin mgnr da yai mata' snn tace dama mgnr kai kaya g'idan su iyayen yarinyar gane' shine nace bari nazo na tambayeka SBD naga mako daya ne yarage.

"Murmushi Alhj yai h'ade da cewa h'aka ne' amma kiramin son tuku.

"Babu musu tamike zuwa part d'in zahradee taje ta sanar dashi abbansa na kiransa.

"Batare da bata lkc ba ya biyota sukaje tare' da sallama suka shiga d'akin' bakin gado ta zauna kusa da maigidanta'shikuma zahradee dukawa yayi a gefe yace Abba gani.

"Alhj yace dama mgnr kai kayane g'idan su Aisha' kamar yau she kake gani yafi dacewa akai kaya?.
Chapter 19 · 0% Book details