← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 89

Sashe 26

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Kwanan Aisha bakwas a hospital safe da yamma sae an wanke mata kurajan' duk lkcn da za'a wanke mata idan har su umma da Abba suna gun' tashi sukeyi suyi nisa da gun sbd ihun da takeyi su k'uma hankalinsu tashi yakeyi.

"gani ciwo yaki ci yaki cinyewa yasa Abba zuwa office d'in doctor bayan sun gaisa ne Abba yace a gskya doctor be'raina da yinkaba amma dan Allah inason zanyiwa Aisha canji hospital sbd banga wani progress da ake samu anan ba.

"mirmushi doctor yai snn yace Alhj kenan laluran Aisha be d'anganci rashin kwarewar aikin mu' tunda kana gani kamar laifinmune to bari na f'adi maka gskya laluran Aisha ba karamin lalura bane' dama inason kashigo nai maka bayani sae gashi Allah ya kawoka.

"a gskya Aisha tana bukatar kyakykyawar kulawa sbd wani cutar ba'iya waje ya tsaya ba can cikin jikinta yake shiyasa sae ammata gwaje gwaje sosae snn musan irin magani da zamu dorata akai.

"to doctor yanzu me kake gani za'iya?.

"abinyi yana gunka.

"kamar yaya?.

"to a gskya irin wnn lalura ba karamin kudi yake ciba' ba nan ba duk hospital da zaka kaita mgnr dae kenan.

"yanzu kamar nawa kake gani zataci?.

"A yanzu kam bazan iya f'adi ba sae yadda muka gani' abin nufi sae mufara mugano wacce irin lalurane snn k'uma mu abinda magani daya dace tai amfani dashi'zamuyi kokarin bata kyakykyawar kulawa wajan gani cutar besake dawowa ba.

"to doct babu damuwa nidae fatana Allah yabata lfy.

"Amin Alhj'.

AFTER 2 DAYS

"dict ya h'ada takardun duk wata gwaje gwajen da yaiwa Aisha da k'uma results d'in da yabayar' da Abba yazo kai tsaye office d'in doct ya nufa baya su gaisa sae da dotc ya gyara zama snn yace to Alhj gskya a iya binciken da mukai akan Aisha result na farko da yafara bamu shine a gskya dae Aisha tasamu matsala a mahaifarta wanda ba lalla bane ta mahaihu.

"na biyu k'uma shine tana bukatar kyakykyawar treatment sbd cutar da take dauke dashi..

"A gigice Abba yace badae HIV bane doct?.

"murmushi doct yai snn yace a'a Alhj.

"ba HIV bane' wnn wani irin cutane wanda k'uma ina kyautata zaton tasamune a gun maigidanta sbd a iyan tambayoyin da nai mata da k'uma gwajin da mukai ya nuna mana cewa adah batadashi sae bayan auren ta.

"to ni k'uma a Iya sanina da Aisha ba maza takebi ba banle nace daukowa tai gun biyebiyen maza.

"ita k'uma irin wnn cuta daukarta akeyi.

"maybe yana niman matan banza ko k'uma auri sakine sanadiyar h'aka ya dauki wnn cutar wanda har itama tasamu.

"da alama shima kansa besan yana dauke dashi ba' sbd duk wanda yake dauke da irin wann cutar dole ya samu nakasu a harkokin lfyrsa' ma'ana ta hanyarne yake iya harbawa wani.

"Amma zamuyi iya kokarinmu akan Aisha mgnr haihuwa k'uma maybe maybe zata iya samu nan gaba' amma dae anya kuwa" himmm!!.

"to nidae doct abinda yafi damuna shine naga Aisha tasamu lfy' shine babban matsala ta.

"karka damu Alhj insha Allahu zata samu lfy nan bada dadewa ba' tunda yanzu mugano cutar da take dauke dashi.

"to nagode doct.

"nima nagode".

"tun daga lkcn aka canzawa Aisha maguguna' mgnr kaikayi da zafi da suke hanata bcc duk tafara samu saukinsu shiyasa yanzu h'aka koda doct yazo wanke mata gun batajin zafi kamar yadda da takeji' sbd doct yana shigowa da kanta take b'ude masa gababta ya wanke snn ya shafa mata magani'.

"In day!! ne kuwa sae yazo da masu riketa' duk da h'aka be hana Aisha ihu da shure shure' hatta makwabtanta sae sun san ana wanke mata ciwo sbd ihu.

"tuni zahradee yaji labarin Aisha tadawo g'ida' tun kafin Nasir ya aiko mata da saki tun anriga ansanarwa zahradee da cewa Aisha batada aure' da k'uma sanar masa halin da take ciki na rashin lfy.

"Zahradee yai matukar tosaya masa amma a yadda yakeji a zcyrsa ba zai'iya zuwa gaidata ba.

"sae dae a matsayinsa na masiyinta zaitayata da addu'ar samu sauki.

"Cikin hukunci ubangiji a hnkli Aisha tafara samu sauki' yanzu har zama tanayi k'uma tana iya tashi ta d'an zaga d'akin.

"Abba da umma suji dadi gani 'year"su tafara samu sauki.

"Yau ma da ubaida tazo dubata har waje suka fita can wajan wani gidin bishiya suka zauna' ubaida tace niko Aisha kinsanarwa Nasir kamar bakida lfy?

"a'a ubaida bansanar masa ba' niso na nasar masa amma wayar bata hanuna' tun ranar da Abba ya amshi wayar yace zaije g'ida yasamu caji shine besake dawomin dashi' koda na tambayesa cewa yai ina ta kainane ko inata waya.

"ni k'uma tun daga lkcn besake tambayarsa ba.

"To Allah ya kyauta' amma ai yakamata ki sanar dashi koda bazaizo ba' tunda zamansa kikeyi yanada'kyau yasani.

"Eh" nima nayi tunani h'akan ubaida amma babu yadda zanyine.

"Abinda yafi damunama shine besan halin da yake ciki ba' sbd nasan inda lfy klau ne Nasir bazai barni na zauna a g'ida har tsawon wnn lkcn ba.

"kowani haline yake ciki oho Allah ne masani.

"Aisha na mgnr ne tana kwalla.

"To Aisha Allah ne masanin komai' duk ma halin da yake ciki dae addu'a ne naki insha Allahu Allah zaikawo masa mafita.

"Amin ubaida ngd.

"sun jima suna hira ubaida natabawa Aisha hkr da cewa Nasir yananan zuwa gateta insha Allahu' da h'aka har yamma yai snn ubaida ta tafi g'ida.

"Sae da Aisha ta shafe wata daya da kwanaki snn suka koma g'ida mgnr sauki kam ba'a mgn sae dae ramar datai.

"da h'aka Aisha taci gaba da kula da kanta'shima Abba kusan kullum idan yana dawowa daga kasuwa saeya siye mata kayan marmari h'ade dasu frue a hankali Aisha tafara maida jikinta.

"mgnr waya kuwa kusan kullum sae tayi amma Abba yaki bata k'uma yacewa umma kada tabari Aisha tai amfani da wayarta wajan kiran Nasir.

'"mmki ya kama umma'umma tayi tayi da Abba akan ya sanar da'ita dalilin h'akan yaki.

"shiyasa tun tana mgn har tagaji ta hakura' da mgnr' h'akna yasa tai tunanin zuwa g'idan ubaida sbd tai amfani da wayarta takira Nasir idan a yanzu da h'aka kewar Nasir takeji.

"tana matukar son gsnisa koda bazai mata komai ba' amma k'uma kash!!!.
sae tai rashin sa'a koda ta tambayi umma' umma kin yarda tai a cewarta wai abbansu yace kada abari tarinka fita ko nan da kofar gida ne.

"babu yadda Aisha zatayi dole yasa ta hkr.

"Tunda Aisha taji tasamu sauki tasawa iyayenta kuka ita zata koma g'idan mijinta' duk yadda umma takai ga lallashinta amma Aisha taki hkr h'akan yasa da yamma bayan Abba yadawo daga kasuwa umma ta sanar masa.

"Abba yace ta kira masa aishan' mikewa tai taje dakinta ta kirata sukazo tare.

"Da sallama Aisha ta shigo dakin bayan sun gaisa snn tace Abba gani' Abba yace Aisha.

"na'am Abba".

"naji sakonki a gun ummanku' h'akane?.

"jiki a sanyaye tace eh'Abba.

"Amma ke Aisha meyasa kikason komawa g'idan Nasir baki gani akwai tutarwa a zamanku? yanzu sbd Allah me sonka tsakani da Allah kenan zai turoki g'ida tsawon wata hudu babu ko waiwaiye? yadda sbd Allah kina gani yai maki adalci kenan?.

" h'akace nima nasan be kyauta ba amma Dan Allah Abba kuyi hkr' babu mmki wasu uziririkane suka shamasa kai da yazo amma Dan Allah kayi masa hkr Abba.

"Aisha kenan bafa ba mgnr hkr nakeyi ba.

"eh"to Abba inaso na koma.

"ina Aisha?".

"Aisha kiyi hkr babu inda zaki..

"kuka Aisha tasa tana f'adin Dan Allah Abba kayi hkr.

"Aisha kiyi hkr Nasir baya sonki' ni k'uma bazanso 'yanta taje inda ba'a sonta ba'.

"a'a Abba wlh baka fahimcesa bane yasa.

"himm" Aisha kenan".

"Aisha kinfi kowa sani kukalai keda kaniki Allah yabani a rayuwata Dan h'aka bazanso naga abinda zai tabamin Ku na kyaleba.

"ko aurenki da maigidanki Allah ne kawai yai da k'uma namu gudumuwar na rashin bincike sbd a lkcn dukkanmu idanumu ya rufe' Aisha a gskya kinban mmki sbd a rayuwata da k'uma irin tarbiyan dana baki banta tunanin zakimin h'aka ba.

"bayan aurenki da Nasir labari yazomi duk irin rashin mutunci da rashin adalci irin naki dan Allah ma shedane banmaki irin wnn tarbiya ba' shine bika juyawa zahradee baya' ke a ganiki kinmasa adalci kenan?.

"Allah ya gani bankasa da komai a g'ida naba banle ace rashine yasa yai maki duk irin hidimomin da yai maki' amma ni nasan so da kauna ne yajashi ga h'aka.

"Aisha nasan ba rokonsa kikai ba' amma kodan darajar soyayyar da yake maki wlh be kamata ki masa haka ba.

"tunda Abba yafara mgn jikin sisha yai sanyi" kukanma da takeyi ya gagara.

"Abba yaci gaba da cewa bazan boye maki ba Aisha tun bayan tafiyar wlh kasa h'ada ido da Alhj Kailani nayi sbd bansan da wani ido zan kallesa ba.

"duk da shima bezo yaimin bayani ba amma banyi blimey nashiba sbd tun bayan tafiyarki zahradee yashiga matsanaciyar hali na rashin lfy wanda dakar mahaifinsa yasamu gano kan d'an sa.

"duk halin da suke ciki lbr yana zuwamin naso naje amma matsalar shine bansan da wani ido zan kallesu ba.

"yanzu dae koma menene Aisha gashi nan kin gilbi kayanki' rashin hakkinkine da bandashi shiyasa' sbd kin nimi kibani kujya a idon duniya ki zubarmi da mutunci k'uma ki hakani f'ada da jama'a to ta Allah bataki ba' sbd yanzu da h'aka ina me tabbatar maki Nasir ya aika maki da sako tun ba yau ba'ga salon nan.

"mika mata wayarta yai snn yace b'ude ki karanta sakon.

"jikin Aisha har rawa yakeyi wajan budewa.

"koda Aisha ta bude bata karisa karantawaba ta sulale ta sume.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.

MMN USWAN

2⃣5⃣

"Umma na gani Aisha ta sume tasa ihu h'ade da kuka' Abdul dake zaune a gefensu a guje yaje ya d'ibo ruwa' yana dawowa jikin umma na rawa ta amsa ta yayyafa mata.

"duk abinda sukeyi Abba na kallonsu amma be tanka masu ba" duk da shima d'in ya razana amma ya matse yanuna ko a jikinsa.

"umma ta kuka h'ade da kiran suna Aisha.

"Aisha na farfadowa h'ade da sauke wani irin ajiyar zcy.

"daga umma har Abdul sae faman sannu suke cewa Aisha.
Chapter 26 · 0% Book details