← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 32 OF 89

Sashe 32

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"can gefe ta hango kular Aisha' batai ta kansaba sbd dama ba cin abincinta takeyi ba' su Amatullah ne da Amatulrahaman sukeci.

"sumadin ba kullum ba sbd gaba dayansu ba yara bane'dan a yanzu da h'aka Amatullah tana three hudreen ne ita k'uma Amatulrahaman tana two hudreen ne a tabawa balewa university dake bauchi.

"toilet Hjy tashiga tai wanka hade da alwala bayan ta idar da sallane ta bude abincin da Aisha takawo mata' gani leda dayane yasata meda murfin ta rufe bata sake bi takansa ba k'uma.

"zahradee yana dawowa daga kasuwa kai tsaye bangare su Hjy yanufa shida Abba' dama dabi'ar zahradee ne duk lkcn daya dawo kasuwa saiya fara zuwa gun Hjy su gaisa sann zaije bangarenshi.

"da sallama ya shiga Hjy na zaune kan sallaya tana lazumi a ladabce zahradee ya gaidata.

"da fara'arta ta amsa hade da tambayar kasuwa".

"alhamdllh".

"hannu yasa ya ciro bandir din two hudreen naira note yabata h'ade da cewa Hjy ga wnn kyasiye goro.

"Hjy tai murna hade da samasa Albarka.

"zahradee na duke sai faman cewa amin yakeyi.

"mikewa da zaiyi hannu tasa ta jawo kular Aisha tace gashi kakaiwa matarka.

"to kawai yace snn ya amsa.

"yana amsa ya fita' bagarensa yanufa' yana shiga Aisha ta taresa da murna tana f'adin sannu da dawowa.

"yawwa sannu.

"mike mata kular yai yace Hjy ce tace na kawo maki.

"kakawo k'uma?" dazufa na kaimata abincin a ciki' kodai har sugama dashi ne?".

"kibude ki gani mana.

"to"

"koda Aisha ta b'ude yadda takai ko taba ba'ayi ba aka dawo dashi.

"shirutai tazubawa kular ido.

"yah dai Aisha?".

"kagafa yadda nakai abincin h'aka aka dawo dashi".

"kamar yya?".

"gashi kagani fa".

"dama iya kacin abinda kika zuwa kenan ko yafi h'aka?".

"a'a" iya kacinsa kenan".

"sbd Allah Aisha wani irin abinci kenan kamar za'abawa mage' dubafa kigani' fushi kenan tai k'uma ko nine h'akan zanyi.

"idan banda rainin wayo wani irin abincine wnn sbd Allah' yau koda bakisanta ba kya dauki wann figigin abincin kibata.

"amma"..

"amma me?".

"gani nayi ranar da nayi da yawa fada tai sosae wai albazaranci ne.

"eh kema kanki ranar kinsan baki kyauta ba.

"sbd h'aka idan har kinaso mu shirya kije kibata hkr kawai.

"hkr k'uma?".

"Eh" kifita kawai kije tun kafin tabiyomu nan ta hadamu gaba daya.

"to kawai Aisha tace duk idanuta sun cika da kwalla' hijab tasa tafita.

"haka kawai kizo ki jamin wani mgn agun Hjy bayan kisan ba kyalemu zatayi ba dagani har ke.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITERS F. O.W.☘.

MMN USWAN

3⃣0⃣

"sallamu'alaikum"

"ami'waalaiki salam'waye?".

"nice Aisha.

"dama Aisha ce tatsaya tana doka wata uwar sallama kamar bakuwa.

"a sanyaye Aisha ta kariso ciki".

"lfy?"

"lfy klau Hjy" dama rokonki nazoyi' Dan Allah kiyi hkri.

"wani abune ya faru?".

"a'a" mgnr abinci ne".

"zahradee ne yadawo da abincin dana samaki yace kekikace a dawo dashi' sbd kinyi fushi.

"shidin yace nayi fushi?".

"Eh shiyasa yace nazo na baki hkr".

"shidin ko?".

"OK tashi kije ki kirashi k'uma kuzo tare.

"to Hjy".

"mikewa tai yaje kiran zahradee din.

"tana fits Hjy tace duk zakuci ubanku dani.

"zahradee na zaune a bakin gado yana jiran Aisha' tana shigowa yace kinbata hakurin?".

"Eh"Amma tace kaje".

"naje k'uma?".

"Eh" wai muje tare".

"to muje' zahrdeee yana gaba Aisha na baya suka shiga dakin' duk dukawa sukai a gabanta snn yace gani Hjy.

"Hjy gani".

"basai kacemi gaka ba'naga zuwanka' tunda ba makauniya nake ba.

"kacewa matarka tazo tabani hkr sbd nayi fushi ko" kayi shiru kamar ba dakai nakeba.

"Eh"h'aka ne".

nice nace maka nayi fushi?".

"a'a".

kaga zahradee banason mananu maganganu daga kai har matarka baku isheni' abincine k'uma ba dole bane sai kunbani' kafi kowa sani bacin sbincinta nakeyi ba'kosu Amatullah dinma su ba kowani lkc sukeciba shiyasa tun farko nace a'a kubar kayanku kace a'a to ga irinta kenan.

"Eh" Hjy nine nace arinka sawa koda bazakici".

"zahradee Kaine bazan boye maka ba' kane kakeso bani abincinka amma matarka bataso...

"da sauri Aisha tace a'a Hjy wlh ba h'aka bane' gani nayi kwanaki da nake sawa da yawa bakwaci shine na rage hannu sbd kada yazama albazaranci.

"eh' kinada gskya shugaban'yar tattali tunda daga g'idanku ake kawo abincin ba.

"ooo!!!! In Laila abin mmki baya karewa nine yau za'a koyamin yadda ake tatta.

"to bari kiji tunda badaga gidan ku ake kawo abincin ba' baki isa kice zaki kawomi wani kauli da ba''adi ba.

"dakawa zahradee tsawa tai h'ade da cewa ashe dama duk abinda makeyi da sanika....

"a'a" Hjy wlh bansani ba' kenan kinsan inda na sani bazan kyaleta ba Hjy.

"shiru Aisha tai kanta na kasa tana hawaye.

"to bari kiji daga yau na kashe kawomi abincinku' k'uma kada kiyi tunanin abinda kikeyine yasa 'a'a ra'ayi nane kawai sbd koda shakeni zakiyi bansan tast din abincinki.

"zahradee dake duke inba hkr da yakebawa Hjy ba babu abinda yakeyi.

"itako Aisha kuka kawai takeyi.

"Hjy taci gaba da cewa yarinya tun kafin kisan zakizo duniya nake girki banle zuwanki jiya-jiya kice abincinki zai tsolemi ido.

"suna cikin h'aka ne Abba yai sallama ya shigo da sauri Aisha ta mike tabar dakin' zahradee dake duke Abba yace son yaya akai ne?".

"da sauri zahradee ya dago yana me cewa Abba.....

"kae tashi kafita.

"mikewa yai yafita.

"bayan fitarsa ne Abba yace Hjy yaya akaine?".

"da fara'arta tace name fa Alhj?".

"ganisu nai anan".

"babu komai".

"washe gari da safe bayan su zahradee da Abba sufita kasuwa' batai aikin komai ba sbd bcc da takeji sakamakon rashin bcc zahradee ya hanatayi da dare.

"har bcc ya fara daukarta taji ana knocking da farko batai niyar tashi ta bude kofar ba'amma jin knocking yaki karewa yasata mikewa tazo ta bude.

"gani Hjy ne yasata dukawa tace ina kwana Hjy.

"ba gaisuwarne damuwata ba' me yasami idon naki sukai jazirrr h'aka?".

"babu komai bcc ne kawai nakeji.

"bcc?".

"Eh".

"ke kika sani' wann damuwarki ne' me aikin bece ya gaji ba'saike da kike kwance akeyi maki' tashi muje kimin.

"mikewa tai tabita' Hjy na gaba Aisha na baya suka shiga kitchen Hjy ta nununawa Aisha lugu da sake na kitchen din snn tace tana bukatar da goge mata ko'ina harda su gas kuka da electric tace duk ta gogesu tas baya tagama k'uma tai mata wanke-wanke.

"to kawai Aisha tace Hjy na fita Aisha na binta da kallo.

"tunda Aisha tafara aiki bata gama ba sai bayan azahar snn takare.

"zuwa dakin Hjy tai ta sheda mata cewa takare'da fara'arta tace ngd Allah yai maki albarkw".

"amin Aisha tace snn takoma bangarenta.

"tana shiga bakin gado ta zauna tai shiru h'ade da uban tagumi tana tunanin abubuwa kala-kala' itadai tasan tsakaninta da zahradee batada matsala h'aka yayyinsa da kanninsa h'ade da Abba matsslarta dayane shine Hjy.

"me nayi mata da bata sona?" idan akan mgnr haihuwane Ai ba'ita yakamata ta damuba zahradee yakamata ya nuna damuwa amma bedamu ba sai Hjy?"

"to kodai kiyayyane?".

"wani zcy yace aa Aisha Hjy bata kinki.

"tunda mafi yawanci lkc idan Abba yaiwa su Amatullah da Amatulrahman kamar su kayan kwalliya zannuwa turaruka da dai sauransu sai Hjy ta cirewa Aisha tabata batare da zahradee ya sani ba' shima Abba da yaga h'aka idan har zaimasu siyayya saiya hada da Aisha.

"shiru tai taci gaba da tunanin dalilin dayasa Hjy take mata h'aka.

"gani la'asar yayi ta mike zuwa toilet tai wnka hade da alwala' tana idar da sallah tashige kitchen dan dora sanwa. tanayi tana wanke-wanke da h'aka har tagama tasawa Hjy tana.

"bata kaiba daki ta koma taje tasha kwalliyarta cikin doguwar rigan shadda snn taje ta dauki kular abincin takai dakin Hjy.

"da sallama ta shiga lkcn Hjy na sallah Amatullahi ne zaune a kan cushion saida suka gaisa snn Aisha ta ije abincin'har ta mike Amatullah tace ina zaki k'uma.

"daki zani".

"daki? me zakiyi a dakin?.

"idan Dan nine akai wnn kwalliyar to kizoki zauna kusa dani.

"murmushi kawai Aisha tai tafice batare da ta tanka mata ba.

"bayan Hjy ta idar da sallah ne tacewa Amatullah ta dauki ahbincin ta medawa Aisha.

"haba Hjy me k'uma tai' Dan Allah kiyi hkr mana.

"ni bataimi komai ba' cine kawai bazan yiba.

"to mu zamuci' ko sister?".

"eh"

"to shikenan gaku gashi ai.

"bayan zahradee ya gama cin abinci ne yaje dakin Hjy gaisheta' yana shiga su amatullah suka muke hade da cewa sannu yya da dawowa.

"yawwa snnuku.

dukawa yai ya gaida Hjy' bayan su gama ne Hjy tace zahradee".

"na'am Hjy".

"yanzu kakai wata nawa da aure?".

"lahhh Hjy har kinmance?" biyar kenan fa".

"alhamdullh gara da Allah yasa kana sane' yanzu yaya mgnr alkawarinmu?".

"alkawari k'uma Hjy?".

"eh" alkawari".

"gskya Hjy ni babu wani aure da zankara' tunda babu abinda Aisha ta rageni dashi...

"kafin zahradee ya kare Hjy ta daukesa da mari' har yaushe kazama h'aka zahradee ashe fitsaran naka yakai h'aka?" wato kai kaji dadi mace to wlh baka isa ba' idan ubanka aure k'uma babu fashi.

"wlh Hjy hkr zaki dani wlh babu wani auren da zanyi' da sauri zahradee ya mike yabar daki.

"salati kawai Hjy keyi h'ade da mmkin zahradee.

"zahradee yana fita dakin Abba ya nufa' yana shiga Abba yace son yaya akai ne na ganka h'aka.

"abba kaji Hjy fa wai dole saina kara aure.

"aure k'uma?".

"Eh" h'aka Hjy tace".

"to kai me kagani?".

"nidae gskya Abba bazan kara kowani aure ba'sbd duk abinda nakeso Aisha tana nai min.

"to son mgnr haihuwa k'uma fa?".

"haihuwar me Abba? Dan Allah abar mgnr haihuwarnan h'aka tunda na samu Aisha ta.

"lalla son har yanzu kai yarone' to wlh bari kaji mgnr aure ba fashi Dan a gskya inaso naga yaranka kafi ba koma ga ubangiji.

"kae Abba harda kae?".

"kwarai da gske son.

"bayan fitar zahradee ne Hjy ta shigo da sallama Abba yace madam yaya akai.

"murmushi Hjy tai sann tace yanzu sbd Allah Alhj h'aka zamu zubawa zahradee ido?".

"na me fa?".

"mgnr aure mana".
Chapter 32 · 0% Book details