← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 89

Sashe 59

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"tsayawa tai gefe tana kwashe zhrdee da harara' shiko bema san tana yiba"

"badake nakeyi ba?"

"snn aisha ta dawo ta zauna' tana zama abbanta yai sallama ya shigo"

"gani zhrdee yasashi karisowa da fara'arsa' juyawa zhrdee yai suka gaisa snn Abba yace lfy ko?"

"Abba yai tambyarne sbd bashi a g'ida Aisha tazo lkcn yana kasuwa' ummace ta zayyana masa abinda ke faruwa"

"Abba yace duk subisa parlour sa' bayan su shiga kowa ya zauna Abba yasake tambyar zhrdee gskyar lamari"

"wlh Abba duk da nasan tsotsayine amma harda laifin Aisha'...

"laifina k'uma?"

"kwarai laifine Aisha"

"to meye nawa a ciki dan yaronka ya kone' ko k'uma sharri kazo kai?"...

" kafin takare tuni umma ta buge mata baki "

"Abba yace ina sauraranka"

"wlh Abba yaro na kuka naje d'akin mmnsa na daukesa zuwa d'akin Aisha' inda tasan bataso na rinka shiga mata daki da yaron wlh da bazan shiga mata dashi dakinta"

"idan na dorasa akan gadonta ta saukesa kasa'ni. kuma na do rasa ne sbd rarrafe yakeyi kada yaje yai mata barna' ita k'uma tana zuwa ta saukesa kasa wai sbd zaibata mata gado' harfa wasa nake mata cewa idan yabata gadon zansiye mata wani' amma besa Aisha ta kyalemi yaroba ta saukeshi yaje yajawo plast ya kone yanzu h'aka yananan gaba daya yasalbe"

"dukkansu subiyu salati sukasa"

"zhrdee yaci gaba da cewa koda nazo inayi mata mgn sai tarigani da fushi ni da haushi ya kamani na duketa"...

"umma tace ni wlh banji dadi bama inda so samune da kai mata wanda yafi h'aka' wawiyan yarinya kawai' wanda batasan me sonta ba"

"kuka Aisha tasa' gani h'aka yasa umma dauketa da mari ta h'au dukanta' zhrdee na kallonsu amma beyi kokarin hana umma ba"

"Abba dake zaune yace Hafsat kyaleta h'aka' umma na cire hannu daga jikin Aisha' Abba yace zhrdee"

"na'am Abba"

"Dan Allah Dan annabi kayi hkr' badan inaso na goyi bayan Aisha ba a'a sai dan bamu da wani kalmar da zamuyi amfani dashine wajan baku hakuri' amma ga Aisha nan ka dauketa ku tafi duk hukuncin da kaga yadace kai mata' sbd koda nine taiwa h'aka bazan yarda ba' jikin zhrdee yai sanyi"

"Aisha najin h'aka tasa wani sabon kuka' abbanta yace wlh na rantse idan kika bari na tashi sai kinyi nadamar zuwanki g'idan nan"

"Aisha najin h'aka da sauri ta mike tabar d'akin hijab dinta ta dauko babu wanda ta sallama tafice'. zhrdee na gani fitarta ya sallami su Abba snn ya mike"

"Abba yakara bashi hakuri h'ade da alkawarin zuwa ya duba me jiki"

"babu komai Abba basai kazo bama"

"ina ya yuwu' kai dai sai muzo kawai"

"to shikenan Abba ngd"

"muke da godiya' Allah ya kara lfy"

"amin"

"zhrdee yana fita yaje ya samu Aisha a gefe kusa da mota ta tsaya' batare daya tanka mata ba yabude mota ya shiga' Aisha dake tsaye batazo ta shiga ba' shiru2 da yaga batada niya shiga ta glass ya leko wlh idan bakizo kin shiga ba' sai nazo da mota na nikeki a gu"

"tsaya tai kamar bada ita yakeyi ba"

"tada mota yai a guje yai kanta' gani h'aka yasa Aisha tsalle snn taje ta shiga suka tafi' har suka isa babu wanda ya tankawa d'an'uwarsa' yanayi parking Aisha ta b'ude mota zata fita' kitsaya"

"snn ta tsaya"

"fuska a daure' to ba nadawo dake ba' saura koda wasane kibari Zainab ko Hjy susan da hannunki a cikin konewar Abba' idan kika bari daya daga cikin mutani g'idan nan suka sani wlh duk abinda akai maki babu ruwana"

"Aisha bata tankashi ba ta b'ude mota ta fita shima shima fita yai' suna shiga sukaga iyayen Zainab duk sunzo harda bbnta dukawa sukai suka gaisa snn Aisha ta shige cikin dakinta"

"zama zhrdee yai kusa da abbansa' itama Zainab na zaune kusa da innarta mahaifiyar Zainab k'uma tana kusa da maigidanta' Hjy k'uma tana kusa da Alhj' *Alhj Musa* yaiwa zhrdee Allah ya kyauta"

"murmushi kawai zhrdee yai"

"inna tace toni wai garin yaya ako konami maigidana ne h'aka?"

"murmushi zhrdee yana shafan kansa h'ade da cewa wlh tsotsayine kawai Allah ya kawo"

"Allah ya kiyaye na gaba"

"amin yace"

"tunda yazama h'aka abani maigidana kawai naje na kula da kayana"

"dariya Hjy da Abba sukai Hjy tace wlh da dai yafi nima nahuta"

"zhrdee dake zaune ya daure fuska"

"Mmn Zainab dake zaune duk mgnr da sukeyi bata tanka masu ba saidai tai murmushi kawai"

"da suka tashi tafiya inna ta mikawa Hjy *Akbar* snn sukai sallama Zainab da zhrdee har b'akin mota suka takasu' bayan sun wuce snn suka dawo ciki"

"zhrdee d'akin Aisha yashiga' yana shiga ganita yai zaune tana kuka' Aisha har yanzu kuka kikeyi' ba mgn ya wuce ba?"

"Aisha tai banza dashi taci gaba da kukanta"

"Aisha badake nake yiba?"

"still tai banza dashi"

"zama yai kusa da'ita h'aba Aisha Dan Allah ki daina kuka h'aka' kinsan tsotsayine idan Allah ya kawo babu wanda ya'isa ya hana faruwan abu".

" fisge jikinta tai h'ade da cewa tsotsayin banza tsitsayin wofi' ai kai bakasan da h'aka ba' ida kasan da h'aka da bakaimi abinda kai ba"

"to naji yanzu dai abar mgnr yawuce"

"hannu yakai zai riketa' da karfinsa ta igijeshi kadan yarage ya f'adi' yana mikewa ya dauketa da mari' kafin ta mike yasake kai mata wani' har ya daga kafa zai kai mata tokari mgnr Hjy ce ya fado masa yasashi meda kafarsa yana cizon lebersa"

"Aisha tasa ihu tana kuka' hannu yasa ya toshe mata b'aki sbd Zainab zata iya ji"

"besan tun gaba lkcn da yashige d'akin Zainab ke makale tana jin duk abinda sukeyi ba"

"Aisha na kokarin kwace kanta' zhrdee ya igijeta gefe yana cewa banza kawai' kin dauka wani abu nake nima a gunki' da har kike nima ki walakantani?" ke d'in me' nifa kikaiwa laifi' amma ban dubi laifinba nazo ina baki hkr shine dan tsabar raina hankali kike tureni"

"halin kin dauka nazo niman wani abune a gunki?" wlh Aisha idan badan darajan soyayyar da nake makiba wlh da...

"himm kawai yace' snn yace anya kuwa Aisha bakida aljannu? gani nayi konami yarofa kikai k'uma har kinada b'akin mgn"

"banza dashi Aisha tai' taci gaba da kukanta' suna h'ada ido saidai ta hararesa"

"shima tsareta da ido yai yana mmkin ta' da haushi ya sake kamashi yace wlh Aisha inda badan darajan Hjy ba na rantse da yau nai maki shegen duka amma ki kiyaye"

"hanyar kofa yai zaifita' Zainab naji tafiyarsa a guje tabar gun' Aisha na gani zai fita f'adi tai a kasa taci gaba da kukanta'

" gani abinda takeyi yasa zhrdee dawowa daukarta yai tsaf kamar yarinya ya kaita gado ya kwantar da'ita yana rarrashinta shima kanshi yaji babu dadi a zcyrsa

📖🖊
☘☘


*AURE IBADA NE*

FASAHA ONLINE WRITES F.O .W.☘.

🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳

*story written by Mmn uswan*

_*oyoyo my special aunt ina maki barka da dawowa my sister' yadda kika fara lafiya ubangiji Allah yasa kigama lafiya' duk wani kura kuran da zaki samu a ciki ubangiji Allah ya yafe maki' tare damu daki daya amin' Rahma Rufa'i nalele Hausa Fulani ina yinki sosai wlh my sister*_ ❤ 🤝

_*OYOYO SIS AYSHA ALIYU GARKUWA'INA TAYAKI MURNAR FARA SABON NOVEL NAKI' UBANGIJI ALLAH YASA YADDA KIKA FARA LAFIYA KIKARE LAFIYA DUK WANI KUSKURE DA ZAKI SAMU ACIKI UBANGIJI ALLAH YA YAFE MANA BAKI DAYA AMIN' GASHI BAN'IYA FILLANCIBA SISTER BANLE NA SUBURBUDO MAKISHI DA FILLANCI AMMA HAKA KIYI HAKURI DASHI. ALLAH SARKI BABANA ABUBAKAR KATAFI KABARNI DA KEWARKA UBANGIJI ALLAH YA JIKANKA YASA KAHUTA AMIN SISTER ALLAH YA KARA DAUKAKA*_

4⃣6⃣

"zhrdee yana fita daga d'akin Aisha na Zainab yashige' yana shiga daidai lkcn Zainab na zaune a b'akin gado tana hawaye' gani shigowarsa ne yasata share hawayen dake fuskanta"

"fuska a daure tace kashigo' nashiho Zainab ya naga kamar kika kuka"

"kuka k'uma?" babu wani kukan danakeyi"

"amma ga alamar kinyi kuka"

"kawai kewar Abbana ne"

"kewar Abba k'uma bayan yanzu suka fita wanda ko g'ida basu kaiba"

"kwanciyata tai bata sake tanka masa ba"

"gani taki sauraransa yasashi fara tsirguwa kodai taji mgnr da sukai da Aisha ne"

"zuwa kusa da'ita yai ya kwanta h'ade da shafe mata ciki' yana f'adin Zainab kodai wanine ya bata maki rai?"

"kai kawai ta kada masa"

"to meya sameki' kodai bakida lfy ne?"

"kai tasake kadawa"

"nine na bata maki rai?"

"Zainab tace a'a"

"jawota yai jikinsa ya rungumeta yana cewa zona matata Dan Allah ki daina kuka h'aka wlh banajin dadin ganinki kina kuka"

"k'uma kinga gash bake kadai bace' Dan Allah kibari kaga irin laluran daya sameki a lkcn cikin Abba yasake kamuki kinji Zainab"

"zhrdee yana rungume da Zainab ne duk yake wnn mgnr"

"a zcyr Zainab ji takeyi kamar ta f'adi masa mgnr dataji sunayi da Aisha' amma k'uma idan tafadi zai gano cewa labe take masu' ko k'uma yace dama h'aka takeyi' ita k'uma wnn shine farkon labe da tai' shidima Allah ne yasa da k'uma rabon zataji mgnr da sukeyi' har tawuce jin zhrdee yana cewa *kecefa sanadiryar konewar Abba* jin h'aka yasa yadawo da sauri"

*Dan dama tuni ta dade da zargin h'akan a zcyrta' h'ade da k'uma yadda zhrdee yake mata nuku nuku lkcn da ta tambyesa garin yaya Abba ya kone' duk wata hanyar da zaikare Aisha saida yabi ya kareta"

"wani zcy na cewa wlh kije ki fadiwa Hjy ne kawai"

"wani zcy k'uma ta yace kyaleta kawai gaba yafi baya yawa"..

" shiru da tai ne yasa zhrdee cewa Zainab tunanin me kikeyi h'aka?"

"saida Zainab ta share hawayenta snn tace babu komai"

"mikewa zhrdee yai ya tube ya kwanta har bcc yafara daukarsa Zainab tace tashi kaje' ka mance kamar ba nan kakeba bane"

"mikewa yai ya fita batare daya dauki kayansa ba' yashige d'akin Aisha"

"washe gari da yamma lkcn *Alhj Kailani* wato abban zhrdee da shi kansa zhrdee da yayyinsa duk suna g'ida a zaune a parlour su Hjy yya Shamsudee ne ke rike da *Akbar* suna hira iyayen Aisha sukai sallama' dayake sai kawuce parlour su Aisha snn kashige nasu Hjy yasa abbanta da ummanta tsayuwa a d'akin kofar g'idan"
Chapter 59 · 0% Book details