← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 89

Sashe 35

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"yar'aike ko da taji shiru komawa tai tace tariga tai bcc' yyan Hjy tace saida aje a tada'ita sbd idan ba'a hadasu yau anmasu fada ba sbd Allah wani lkc ne za'a hadasu.

"har tamike da sauri Hjy tace a'a abarta kawai.

"Aisha najin shiru tacewa zhrdee kagani ko' da kabarni naje naji kiran da akemi' wata kilama Hjy ne ke kiran.

"idan Hjy ne sai me' Dan Allah kizo mu kwanta.

"kamo mata hannu yai suka koma.

"bayan kowa yai nasa jawabin ne aka dauki amarya zuwa gidan ta".

"koda suka isa dakinta aka sauketa kanwar Mmn zainab ce ta dauko wasu maguguna tasake bawa zainab tasha hade dana shafawa a jiki' bayan ta gamane ta dauki bokitin ragowar magugunar ta bata da k'uma nuna mata yadda zatayi anfani dasu' ko wnn da lkcn shansa.

"Zainab ta amsa sukuma suka mike h'ade da sallama' drive ya medasu gida' gani za'a watse a bar gida babu kowa gashi har lkcn ango bezoba yasa yyar Hjy ta buga gida ta sanarwa Hjy akan har yanzu zhrdee bezoba ita k'uma gida takeson dawowa sbd bcc takeji.

"Hjy najin h'aka taje ta sanarwa Abba abinda ake ciki'murmushi kawai Abba yai hade da daukar wayarsa ya kira zhrdee.

"zahradee yana gani number Abba amma be daga ba sbd yariga da yasan kiran da ake masa.

"Abba yai kira har yagaji amma zhrdee be daga ba' tun ran Abba be baciba har yakai ga yabaci.

"himm Alhj kaga abinda nake fadi maka ko?" tun yanzu kenan yaronga yana niman zuba mana kasa a ido.

"mikewa Abba yai batare sa yai mgn ba yana gaba Hjy na baya' bagaren Aisha Abba ya nufa da kansa yake knocking jin muryan Abba ne yasa Aisha mikewa da sauri hade da cewa zhrdee tashi Abba nefa da kansa.

"a lkcn har bcc ya fara daukar zhrdee jin ance Abba ne yasashi mikewa da sauri ya dauki wandonsa yasa snn yaje ya bude kofar".

"yana budewa Abba yace fito kawuce".

"to kawai zhrdee yace hade da komawa cikin d'akin' toilet yashiga yaje yai wanka snn yazo yasa kaya yafita' yana fita Aisha tasa kuka.

"zhrdee na fita Abba yasashi a mota da kansa yakejan motar tafiya suke amma babu wanda ya tankawa wani har sukakai gidan.

"suna isa zhrdee ya bude kofa ya fita a lkcn ne Abba yace son saida safe' idan ka karisa ciki kakirami yya tafito.

"to kawai zhrde yace snn yakarisa ciki.

"yana shiga Hjy tai masa sannu da'isowa h'ade da cewa saida safe.

"Allah ya bamu alkairi.

"tana fita yarufe gida ko'ina kai tsaye wani extra room yanufa koda yashiga dakin babu komai empty ne ko katifa babu dawowa yai parlour ya dauki pilon cushion yaje yai pilo dashi rigarsa k'uma ya shinfida a kasa ya kwanta.

"Zainab shiru-shiru ango zaishigo amma shiru' gashi har bcc ya fara daukarta' shiko zhrdee yana can bemasan tanayiba.

"Abba yana isa gida Hjy ta taresa da yya dai Alhj?".

"murmushi kawai yai batare da yace komai ba.

"gani 1C-lock yayi k'uma har yanzu zahrdee be shigoba mikewa tai tanufi parlour a hankali take tafiya sbd tsoron daya kamata a tunaninta ita kadaice a gidan.

"koda ta jijina kofar parlour jinshi tai a rufe gam da key' dawowa da baya tai tafara dube-dube gidan' duk inda taduba babu wanda tagani wani Sabon tsoron yasake kamata da sauri ta juya zata koma daki sai nepa suka dauke wuta' gida yasake rufewa da duhu.

"hankalin Zainab yayi matukar tashi a hankali take laluba tana niman hanyan zuwa daki dan kunna light din wayarta.

"duk juyin da Zainab zatayi saita bige sakamakon rashin light garin lallabawa tana niman hanya yasa duk ta rikito da jeren banga da akai mata glass din suka faffashe.

"da sauri Zainab taja da baya' taje ja dabaya ne Glass ya soketa a kafa' a take tasa ihu tana kuka.

"duk abinda Zainab keyi a kunni zhrdee amma besa ya fitoba.

"da h'aka tai tayi tana karo da bango har ta'isa d'aki' ga bigewar da goshinta yai' da h'aka har tasamu tashiga d'akin.

"Zainab najin ta dafe gado ta fashe da kuka tana kokarin daukar waya ta kuna' bayan ta kunnane taje ta rufe kofa a gefen gado ta rakube taci gaba da kukanta.

"ga waya a hannunta amma batai tunani kiran zahrdee ba'da h'aka har safe yai.

"jin kiran sallar farko zahrder yamike yabar gidan' itama Aisha mikewa tai taje tai alwala tazo sallah' bayan ta'idar da sallah ne taji bcc ya kamata pilo ta jawo ta kwanta akan sallaya taci gaba da bcc.

"zahrdee bedawo gidan ba sai around 11AM koda ya dawo parlour ya zauna' bayan ya zauna ne yake gani barnan da Zainab tai.

"mikewa yai ya tara kayan gefe glass din da suka fashe k'uma ya sharesu ya zubar snn ya dawo ya hade da kunna TV yana kallo' be dade da zama ba su Amatullah da Amatulrahman sukai sallama dauke da kayan abinci a hannu' zahrdee da fara'arsa ya taresu bayan sun gaisa amatullah tace Hjy ce tace akawo maku abin karyawa.

"Allah sarki kice mata mugode.

"yya ina amaryan taka?".

"tana ciki tana bcc".

"jin haka yasa basu sake mgn ba suka mike hade da sallama.

"har bakin kofa zahrdee yai masu rakiya sann yadawo.

"zama yai dirshan ya dibi abinci yafara ci' yana cikin ci kenan yar'uwan Zainab sukai sallama suka shigo.

"da fara'arsa ya karbesu' suka gaisa bayan sun gaisa ne yace dasu tana cikin daki.

"gani su tsaya basuda niyar shiga yace bismillh mana.

"ido suka sake hadawa suna kallon junasu' da yake duk yar'mata ne mace daya ne me aure a cikin su.

"mikewa zhrdee yai ya fita ya bar masu g'idan.

"yana fita idon su yakai gun kayan da zainab ta barnatar da sauri har suna h'ada baki suna cewa lahhhh! duk abinda sukai kamar wasu yara".

"to mema ya kawosu parlour?".

"a'a kekuwa kila garin wasane.

"h'aba wani irin wasa?" wasa yabar bedroom sai parlour.

"k'uma dai da wani irin tunani wlh' jiya-jiya da daurin aure shine har zasuyi wani abu?".

"kekuwa rai da marmari' rai dangin goro".

"yanzu dai duk kumubar wnn mgn kuzo muje cikin d'akin muganta.

"duk su hudun duguma sukai zuwa cikin bedroom'koda suka shiga ganita sukai kwance kan sallaya tana bcc' shigowarsu ne yasa ta b'ude ido' tana cewa su walida har kunzo sannuku da zuwa.

"duk Zainab na mgnr ne a kwance bata tashi ba.

nusaiba dake kusa da walida tace Zainab amarya to tashi zaune mana.

"to"kawai tace".

"da kar zainab ta laluba ta mike zaune' snn tace da wani lkc ne kuka shigo.

"bamu dade da shigowa ba' mushigo musamu angonki a parlour yana karyawa amma ganimu yasashi fita.

"himm kawai zainab tace' gani gado a mutsutsuke ko gyara shi ba'ai ba yasa walida cewa zainab meyahanaki gyara d'akin tunda safe sbd Allah' yanzu inda bakin kunya ne suka shigo mezakice?" Dan Allah kitashi ki gyara gadonki tun kafin jama'a suyi yawa.

"to kawai tace".

"saida Zainab ta kamo katakon gado snn ta mike.

"h'ada ido suka sakeyi suna murmushi.

"gani takasa daga kafa sakakoman ciwon dataji garin yai mata tsami.

"nusaiba tace me k'uma ya samu kafar zainab?".

"yankewa nayi".

"yankewa k'uma?".

"Eh" wlh".

"garin yaya?" k'uma da me?".

"dauke light akaji nikuma naje mikewa ban saniba na bige da katakon friend dake parlour shine glss dinsa ta yanke ni.

"to fa' Allah ya sauwake".

"amin".

"jawo zani gadon da Zainab zatayi taga Ashe shima jini yabata bata saniba' suma suna gani suka sake h'ada ido.

"kwashewa Zainab tai ta zuba a gefe har ta daga kafa kenan tanaso taje wadrop ta dauko wani zanin gadon taji kafarta ya rike mata' tsayawa tai tai shiru h'ade da matse baki.

"walida tace yah?" dai Zainab?'.

"kafa nane yaimin tsami".

"to!!! koma ki zauna".

"koma gefe tai ta zauna.

"nusaiba da walida suka gyara mata gadon tas' zani gadon daya baci da jini suka kai bathroom suka ije sbd a nasu tunanin najasa ne a ciki yasa basu wanke ba.

"walida tace Zainab kinyi wanka?".

"a'a".

"sbd me?".

"himm kawai tace".

"h'aba Zainab sbd Allah da saniki da komai kike zama da najasa har wnn lkc?".

"shiru Zainab tai bata tanka ba".

"amma kinyi sallah ko?".

"nayi".

"to shikenan yanzu tashi kije kiyi wanka daga nan ma saiki gargasa jikinki da ruwan zafi.

"to kawai tace".

"mikewa Zainab tai gani yadda takejan kafa yasa walida riketa zuwa bathroom bayan ta fitone suke mgn nusaiba ke cewa walida kodai na karfi yai mata?".

"me kika gani nusaiba?".

"ke baki gani yadda taji jiki' k'uma ga barna da sukai har parlour fa sbd Allah' wann wani irin abune h'aka?".

"gskya kam"da alima".

"matar aure dake tare da sune mai suna SAMEENRAT tace a'a basai yai mata na karfiba dama dole asamu h'aka tunda ba taba sani namiji taiba'amma idan ta daure kafin nan da sati tasaba.

"duk baki suka h'aka suna cewa ko 🤔 ?"!!!.

"Eh" mana amma kuce mata tarinka amfani da ruwan zafi wajan tsarki".

"duk suka hada baki da cewa to".

"fitowar Zainab daga toilet ne ya katsesu.

"Su walida da nusaiba yaran yyan Alhj Musa ne Uwa daya uba daya' ita k'uma SAREENRAT matan yayan su walida sai dayan da suka shigo tare mai suna Rahma ita k'uma da bbnta da Alhj Musa uba daya ne duk suna karatu a nan bauchi university ne.

"aiki suka taya Zainab sosae harda abinci saida sukai mata suka zubawa zhrdee nasa a kula snn sukai wanke wanke gam da sallar magrib suka tafi gida' bayan fitarsu ne zainab tashiga wanka tana gamawa tai alwala saida tai sallah snn tai kwanlliyarta shikin sket da riga na material light blue tayi matuka dawowa parlour tai ta zauna tana kallo.

"koda zahrdee yabar gidan can wata uguwa yaje ya boye inda babu wanda yasan yana gun' saida ya daidaici magrib yayi kowa yatafi masallaci mata k'uma maybe suna daki suna nasu sallar snn ya saci jiki yazo gun Aisha' Aisha na sallah kamar daga sama taji anfado dakinta.

"h'akan yasa tai kananu sura sbd ta'idar da sauri' bakin gado zhrdee ya zauna yana jiran ta'idar' tana sallama tace lfy?" me yakawoka kaida kake da amarya?".
Chapter 35 · 0% Book details