← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 89

Sashe 21

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Gani zasu gwada masa karfi yasashi rike Abba' a lokcin ne Abba ya dawo daga tunanin da yake' hannu kawai ya daga masu alama su bari.

"Abba da kansa ya jinginar da zahradee a jikin gado' snn shima ya h'au gefen gado ya zauna' cikin kuka zahradee ya kwashe duk abinda Aisha tai masa ya sanarwa iyayensa' yanayi yana kuka' har ya kare' yana karewa yasake fasawa da wani kukan h'ade da rungume Abba sa.

" Hjy dake gefe a take tace kan'buhun uba! Ni zata kawo rainin hankali to wlh bata isaba' ni da tuntuni ma ka sanar dani wlh har gida zanje naci ubanta' wai tsayama tukun waye ubanta a garin nan? Da zcy ya dibeta fisgo hannu Nurudee tai dake tsaye kusa da'ita h'ade da cewa kai zomuje har gidan naci ubansu marasa mutunci.

"Har sukai bakin kofar fita Abba yace ina zani?

" babu ko tsaoro bale shakka tace g'idan su Aisha.

"Abba yace in har kikabar nan ba gida kika jeba to bada izinina ba.

" Hjy laila macece me zafi sosae amma kuma me biyayya bata tsallake mgnr mijinta' h'akan yasa ta dawo tasamu gu ta zauna duk da h'aka inda take shiga ba nan take fita ba.

"Alhj yace kiyi hakuri h'aka nafiso naje da kaina' sbd idan har nabari kikaje nasan komai zaki iya aikata masu" kuma banaso ki aikata abinda zamu dawo muna danasani SBD bamusan abinda gaba zaiyi ba.

"Cikin goats one tace yayi dawa Allah ya saukake.

" zahradee dake manne jikin Abba cire drip d'in yai h'ade da cewa Abba muje gida ni na warke.

"Abba yace a'a son kabari kakara samu sauki.

" suna cikin h'aka doctor ya shiga koda yasake dubashi yace yasamu sauki dama damuwace tai masa yawa shiyasa amma Dan Allah arinka kulawa dashi da kuma gujewa abinda zaisa yasake shiga irin wani yanayi.

"Abba yace insha Allahu.

" daga nan aka rubuta masu magunguna h'ade da sallama' suka koma gida.

"Tunda suka dawo guidance Hjy mmnsa da yayyinsa kae har ma da Abba suke bawa zahradee kyakykyawar kulawa h'ade da kwatar masa da hankali dan gani yadawo normal kamar da' kusan kullum sae Abba yai masa addu'a a ruwa yabashi yasha sbd ko Allah zaisa a cire mgnr Aisha a ransa.

" d'an koda suka dawo g'ida kullum mgnr kenan Aisha'aisha ta tafi ta barni Abba da Hjy suyi fada har sugaji' amma zahradee bedaena ambaton su Aisha ba' idan ka gansa kamar mahaukaci sbd yadda ya koma' shiyasa har bada kudi Abba yai arinka yimasa addu'a ana bashi yana sha' shima kuma yana yimasa da kansa.

"Cikin hukucin Ubangiji komai yafara daedae ta har fita kasuwa yakeyi shida Abba' amma ko da wasa bayaso a kawo masa mgnr budurwa' h'aka yaci gaba da rike kansa' amma idan har ya dauki wayarsa yafara duba pict d'in sae kawai kaji yana nisawa' da Abba yaga h'aka canza masa wayar yai wanca k'uma ya goge komai dake cikinta snn ya kai d'akin sa ya boye.

" tunda daga lkcn zahradee ya dawo normal life kamar kowa' duk wanda yasan zahradee k'uma yasan bayason mgnr budurwa bayayi masa' shima yaci gaba da harkikin kasuwancinsa gani suna samun Improvement yasa Abba ya sakan masa komai Dan yanzu kusan duk dukiyar Abba a hannu zahradee yake sbd zahradee irin mutaninan ne wanda duk abinda zasu taba sae yayi albarka' shiyasa Abba yake matukar son zahradee akan sauran yaransa.

☘☘☘ ☘☘☘

CI GABAN LABARI

Abdul be'isa garin binni kebbi ba sae gam da magrib ana saukeshi a tasha yai amfani da address d'in da umma tabashi dashi ya'isa har g'idan su Fatima a bakin gate ya tsaya sae da yasake tambayan gateman snn yace dan Allah shi kani matar maigidan ne Aisha ko zai taimaka masa ya sanar da'ita?

"Gateman yace ba matsala ga gu ya zauna ya jirashi yaje ya sanar dasu snn yashiga daga ciki' wani d'an karami bechi dake gefe ya nuna masa ya zauna' snn shikuma ya shiga daga cikin g'idan lkcn Fatima na zaune a parlour ita da yara gateman yai sallama Fatima tai masa izini daya shigo.

"Yana shigowa bayan ya gaisheta snn yace dama wani bakon saurayine yazo yace wai shi kani madam ne daga garinsu yake sunasa Abdul shine nace ya tsaya na sanar maki snn.

" Fatima tace okay bari a kirata tuku' juyawa tai gun Khadijat dake zaune kusa da'ita tace jeki ki kira antynku.

"Khadijat tace to' mikewa tai taje da sallama tashiga d'akin lkcn Aisha na zaune bakin gado ta zabga uban tagumi' gani Khadijat ta shigone yasata dagowa da sauri tace Khadijat ya akai ne?

" Khadijat tace Anty momy ne tace kizo kinyi bako.

"Aisha tace bako k'uma? Daga ina?.

" mikewa tai suka fita tare' suna tafita parlour Aisha tace Anty gani' Fatima tace gateman yashigo yake sanar dani kinyi bako' Aisha tace bako k'uma Anty toni wama nasani a garin nan da zaizo guna.

"Murmushi kawai Fatima tai sbd yadda Aisha take mgn' snn tacewa Aisha jeki kiga ko waye.

" komawa tai ta dauko hijab tasa snn tafito h'ade da kiran Khadijat ta rakata' Aisha na fita gani bataga kowa kusa a gun ba tajuya zasu koma ciki da sauri gateman yace Hjy ga bakon nan snn Aisha ta tsaya fita yai yakira Abdul suka shigo tare' Aisha na ganisa a guje taje ta rungumesa h'ade da fasawa da kuka tana kiran Abdul dama Ashe zansake ganika?.

"Abdul yai matukar mmkin gani Aisha sbd gaba daya ta lalace ta fita a haiyacinta kamar ba Aisha daya sani ba' dan ma jinisane inda badan jini ba da ba lalla bane ya shedata.

"Shirun da Fatima taji yasata lekawa gani Aisha na rungume da Abdul yasata fita taje gunsa kallo daya taiwa Abdul taga kamanni Aisha a fuskansa' tace a'a Abdul yau bakone h'aka mukai to kukariso ciki mana.

" snn suka karisa ciki' tana gaba suna baya suka shiga a parlour suka zauna Fatima ta kira Khadija sukaje kitchen ruwa da juice tabawa Khadijat tace takaiwa su Abdul parlour' Khadijat na gaba Fatima na baya suka koma parlour a gaban Abdul ta'eje try d'in' bayan ya sha ruwan ne suka gaisa h'ade da tambayarsa su ummansu.

"Abdul yace duk suna lfy' sun cema a gaida ku.

" Fatima tace muna amsawa.

"Mikewa tai da Khadijat snn ta dauki Jabeer dake bcc suka basu gun' bayan tashiga dakine yasake aikan Khadijat ta kira Aisha' tare suka tafi da Aisha kitchen Fatima taje ta d'au abincnsu na dare wanda zasuci da yara ta raba biyu tace Aisha ta dauka h'ade da bata hakuri sbd abinci babu yawa k'uma abincin gida kadan yarage banle ace za'a sake dafa wani.

'" Aisha tace ba komai ngd sosae Anty.

"Itama Fatima tace babu damuwa.

" kai tsaye d'akinta takai masa abincin snn ta d'ibi nata da zataci na dare ta kara masa a nasa snn takoma parlour ta kirashi daki yazo yaci abinci.

"Zama yai dirshan akan carpet yanaci suna hira yana bata lbrin su Abba da umma' suna cikin hira ta dauko nata zataci gani abincn kadin ne yasa Abdul cewa Anty kije ki kara mana amma wann abinci kamar zakibawa yaro.

"Yage Aisha tai h'ade da cewa a'a h'aka ma ya'isheni.

" ragowar abincin da Fatima da eje tabawa yara sukaci ita k'uma tasha ruwan Lipton' lkcn kwanciya da yayi extra d'akin da babu kowa Fatima tace Aisha ta bude wa Abdul ya meant a a ciki.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.

MMN USWAN

2⃣0⃣

"Da safe cikin abinda Fatima ta h'ada wa yara na breakfast ta d'ibawa Abdul tea ne da arish ko madaran kirki babu a ciki' da Aisha tashigo gaidata ne tace taje kitchen ta dauki abin breakfast takaiwa Abdul, Aisha tace to ngd Anty.

" har tajuya sai Fatima tace amma ke hkr zakiyi sbd bekai damu ba' koni bansamu wanda wajan nawa ne nabawa Abdul tunda shi bakone be kamata a barsa da yunwa ba.

"Aisha tace hakane Anty babu damuwa nagode.

" kai tsaye d'akin ta takai abincin ta'ije duk da yau ta tashi da yunwa sbd ragowar abincin tane wanda zataci da dare ta karawa Abdul yaci ita k'uma ta hkr, shiyasa ta tashi da yunwa amma yaya zatayi dole yanzu d'inma ta hakura tunda bashida inda zaije yaci inba nan ba.

"table d'in dake gefen gadonta tadora akai ta eje masa' Abdul be tashi ba sai around nine snn ya tashi bcc yana fitowa daga daki parlour yazo ya zauna snn ya kira Aisha ta waya' Aisha na fitowa tace yazo suje d'akin ta.

" mikewa yai suka shige bayan su gaisa ne Aisha ta d'au abin breakfast ta mika masa' Abdul yaci suna hira' duk hiran da sukeyi ba shigar Aisha yake yiba kawai amsashi takeyi amma bekai ciki ba' idonta su cika da kwallo k'adan yarage su xubo da sauri tasa hannu ta goge.

"Da Abdul ya lura da h'aka yace Aisha lfy? murmushin yake tai masa wanda bekai zuci ba' h'ade da cewa babu komai tun dare ne wani abu ya f'ada min a ido shiyasa kaga duk idanu suyi ja.

" Abdul yace sorry' idan kinga zai dameki ki sanarwa maigidanki ya kaiki hospital sbd ba'a wasa da ido fa.

"To kawai tace.

" Snn Abdul wayya ni tunda nazo banga maigidan nakuba kodai baya gari ne? Aisha tace yana nan wasu aiyukane sukasha kansa shiyasa baya samu isaishen lokcin da har zaka gansa.

"okay kina nufin baya kwanan g'ida kenan?.

"shiru Aisha tai bata sake tankasa ba.

"Abdul yace yauwa Aisha.

"na'am.

"nidae tun jiya da nazo wani iri na ganki kamar mara lfy kodae tun cuwon da umma tace kinji shine har yanzu baki dawoba.

" Eh"kawai tace.

"Amma ai kinkai wata uku da rashin lfy ko?.

" Eh"

"To kina amfani da magugunar da aka baki kuwa?.

'" ina amfani dasu mana.

"amma gaskiya yakamata ace kin canza' dubi yadda kika koma kashi kashi fa' kamar wanda batacin abinda' Aisha kodae kina zama da yunwane? ko k'uma bakijin dadin zaman g'idan ne?.

" shiru Aisha tai kanta na kasa.

"Abdul yace Aisha kiyi mgn mana.

" hawayene kawai suka zubo mata.
Chapter 21 · 0% Book details