← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 89

Sashe 5

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A wanga lokacin zama ya gagari Aisha sai dai kwanciya ' ko rintsawa batayi ga azabar kaikayi da suke mata' cikin dare da kurajen suka hanata bcc mikewa tai ta lallaba tashiga toilet ta kunna ruwan zafi saeda ya kusan cika bath snn tashiga cikin ta zauna h'ade da daukar sabulun dettol protection anty bacterial soap dashi take wanke kurajen duk da zafin da takeji amma h'aka ta hakura ta d'anne'bayan ta gama ne tai wanka daga ta daura towel ta dawo bedroom magani da doctor ya bata na shafawa tube shine ta dauka h'ade da auduga' bude audugan tai yai falefale sai da ta shafe tube din snn ta dauko audugan ta lulube gun dashi snn ta kwanta kafa a bubude ko zani bata iya rufe jikinta dashi ba' tana kwanciya bcc ya dauketa.

"Aisha bata tashiba sai bayan shadda na safe' tashi tai taje tai alwala tazo tai sallah bayan ta'idar kwanciya tai tana jiran xuwan Yallabai shiru2 har goma bezoba h'aka ta sake lallabawa taje kitcher ta h'ada tea tasha da magani'bayan ta gama ne takoma d'akinta ta dauki waya tai dilling nmbr Nasir sai da tai kira biyu ana uku snn ya daga.

"Cikin natsowa Aisha tai sallama' Shima da fara'arsa ya amsa' snn ta gaidashi'bayan sun gaisa ne Aisha tace gani nai baka shigo dubani bane da safe yadda kasaba shiyasa nace bari na kiraka naji ko lfy? Allah yasa dai lfy ne.

"Nasir yace wlh Aisha aikine yimin yawa shiyasa bansamu biyowa ba'amma kiyi hakuri dan Allah' murmushin karfin hali tai tace babu komai' Nasir yace nagode wa Allah daya banike k'uma yasa kinada fahimta Allah yai maki albarka kuma ina Allah ya yarda yau dawori zan dawo kinji yan'mata na.

"Murmushi tai h'ade da cewa naji Yallabai Allah ya kawo dakai lfy'.

"yace amin nagode' amma jikin yayi sauki sosae ko?

"Aisha tace ai nawarke' Nasir yace alhamdullh Allah ya kara lfy' saena dawo.

"daga nan sukai sallama' Da yamma kafin Nasir ya dawo shiga kitcher tai ta h'ada masa tuwon semo da miyar kubewa busassa tana gamawa ta kwashe ta kai dinning snn taje tai wanka bayan ta fito doguwar riga kawai tasa batare da ta tsaya wani kwalliya ba ko pan babu a jikinta parlour ta koma da kwanta tana jiransa.

"Bata dade da kwanciya ba alh Nasir yai sallama cikin dabara ta mike taje ta amshi jakar hannunsa h'ade da yimasa sannu da xuwa' Yace yauwa Aisha ta' ya jiki?

"Tace naji sauki'

"yace Allah ya kara sauki".

"Kamo hannunsa tai xuwa cikin d'akinta'Bayan ta'ije jakar hannunta shima ya zauna a b'abin gado' dukawa tai tana cije masa igiyar takalmin dake kafarsa.

"Dankwalin dake kanta ya f'adi ido alh na kaiwa kanta hannu yasa yana fashe masa kitson dake kanta h'ade da cewa gaskiya yan'mata na kina shagwabani da yawa' wanga irin kitso duk sbd ni akayita gaskiya naji d'adi sosae Allah yai maki albarka.

"Murmushi Aisha tai h'ade da cewa Amin' Bayan ta gama cire masa takalmin dagowa tai tana kwance masa igiyar rigarsa da yake suit ne yasa sai da tagama snn ya mike ya tube' itama mike tai ta shiga toilet ta h'ada masa ruwan wanka bayan ta fitone yashiga.

"Kafin yafito taje ta kara gyara dinning ta zuba masa abincin sa a plate h'ade da juice d'in da tai masa ta zuba a cup da ruwan sanyi snn ta koma parlour ta kwanta' koda yafito sanye yake da farar jallabiya a jikinsa dinning ya nufa gani tai masa arraging komai zama kawai yai yaci gaba da cin abincin sa.

"Itako Aisha tana parlour tana kallon tashar zeeworld wani films da dukeyi mai suna my lost home' Gani tara yayi ta canxa channel d'in zuwa Nigera news sbd kallon labarai.

"Jin za'ara labarai yasa alh Nasir cire hannu daga abincin da yakeci dama lokacin ya riga ya koshi' xuwa yai ya zauna kusa da'ita sukaci gaba da kallon labarai tare sunayi suna yana janta da hira har aka gama.

"Aka koma nuno rahotanni gani goma ya wuce ya kashe TV yace tashi muje mu kwanta sbd gobe idan Allah ya kaimu inaso na fita da wuri' TO kawai Aisha tace h'ade da mikewa suka shige cikin bedroom' suna shiga Nasir ya tube ya rage daga sai short nike ya kwanta' Itako Aisha da rigarta ta kwanta can gefen gado taje ta rakube sbd bataso tai kusa dashi banle harya yajawo wani abu ya shiga tsakaninsu.

"juyawar da zaiyi yaga bata kusa dashi' hannu yasa ya jawota jikinsa ya rungume ta' yace cewa Aisha yau k'uma wani sabon salon wasane kika samu h'aka? Na lura kedai baki rabuwa da wasa' shiru Aisha tai tana jinsa.

"Nasir yace yan'mata na' Aisha ta dago kai tana kallonsa' yace tashi ki tube wanga rigan nasha f''idan maki babu kyau mutum ya kwanta da suturunsa masu kyau' karkiga kamar f'ade nane annabi Muhammed ( S. A. W) ya f'adi h'akan' idan h'aka kada ki sake kinjiko.

"Aisha tace to.

"Gani ta tsaya nawa kamar bazata iya tashi dagowa yai ya zauna akan gado snn yasa hannu ya yaye mata rigan daga kasa zai cire mata jan da zaiyi yaga batada komai a jiki inba rigan ba' da sauri ya saki rigan snn yace h'aba Aisha wani irin d'abi'a ne wanga ke ko tsoro bakiji kada wani shedani aljani yazo ya shigeki.

"Shiru Aisha tai.

"Nasir yace wlh koda wani idan nasake shigowa g'idan nan na sameki h'aka sainayi maki abinda baki taba tsanmani ba' wani rainin wayo ka wala kanci kirinka zama kina wala kantarmin da jiki sarai-sarin wani katon banza yashigo a kuskure ya gane min jikinki ko? To wlh bazan dauki irin wanga abin ba idan kika sake sai kinyi mmkin abinda zaiyi maki.

"Aisha na hawaye tace dan Allah kayi hakuri.

"Alhj yace ba zance nayi hakuri bane Aisha gani nayi dame na rageki nasan duk wani abinda zaki bukata na tanada makisu enough a g'idan nan ko sun karene bansani ba' Kai Aisha ta daga masa.

"Yace to menene dalilin walakantamin jiki h'aka?

"Shiru Aisha tai.

"Snn yace bayan h'aka banace kada na sake dawowa g'idan nan na sameki da wanga rigan ba? Koda badake nakeyi bane Aisha.

"Shiru Aisha tai tana shaeishekan kuka' Nasir yace wlh idan baki rufemin baki ba k'uma ki goge hawayen nan ba sai na maki duka idan yaso sai kiyi kuka me dalili' jan h'aka da sauri Aisha ta goge hawayen snn ta daina kuka' tsareta yai da ido.

"gani bata tashi ba banle ta cire rigan' sauka yai daga gadon snn ya jawota da karfi ya cire mata rigan jikinta' hannu Aisha tasa tana rufe gabanta snn ta matse kafafuwarta' da alh ya lura da h'aka yace menene a gun da bakiso na gani? Da sauri Aisha tace babu komai.

"Nasir yace banyarda ba.

"gani ta kara matse cinyoyinta k'uma tana matse fuskanta alamar tana jan zafi' yawota yai dakin gadon snn yasa hannu da karfi ya bude mata kafafuwan' gani gun yai damage mmki ya kamashi yana f'adin me zangani h'aka Aisha? Tun yaushe wanga ciwon yasameki Aisha?.

"Fashewa da kuka Aisha tai takasa bashi amsar tambayarsa.

"Nasir be tsaya jiran amsar ta ba' toilet ya shiga ya h'ada ruwan zafi mai zafin gaske snn yazo ya dauketa xuwa baht room d'in cikin bawon wanka ya yasa snn ya dauko dettol da soso xuba dettol d'in yayi a ruwan zafin snn ya dauko medicatet soap ya goge a cikin soso h'aka ya dunga dibo ruwan zafin yana gurje kurajen.

"Aisha inba ihu ba babu abinda takeyi duk da h'aka besa Nasir ya daina dirje kurajen ba' duk sai da suka farfashe suna jini snn ya kyaleta h'aka ya dauki ragiwar ruwan yai mata wanka dashi' bayan ya gama mata wankan ya dauketa xuba bedroom tube d'in da take shafawa ya shafa mata a gun snn ya rufeta da bargo shima ya kwana.

"Aisha batasan lokacin da bcc ya dauketa ba.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F. O. W ☘.

MMN USWAN

0⃣6⃣

"Cikin dare koda Aisha ta falka taji saukin radadin da takeji' lokacin ido Nasir biyu gani ta b'ude ido yasashi cewa Aisha yaya jikin? Aisha tace naji sauki.

"Nasir yace ya kikejin radadin dake maki? Tace yai sauki.

"yace alhamdullh' Allah ya kara sauki.

"Tace amin.

"Da safe bayan yai wanka ya shirya juyowa yai gun Aisha yace tashi muje asibiti' Aisha tace kabari kawai nasamu sauki' Nasir yace wani sauki ne h'aka kina gani yadda kika koma kuwa.

"hawaye ne suka xubo mata h'ade da cewa bazan iya zama bane shiyasa' Kai kawai alhj ya kada h'ade da cewa ayya sorry insha Allahu nan bada dadewa ba zaki samu sauki kinji.

"kuka Aisha tasa tana f'adin dan Allah kakiramin ummata naji muryarta dan Allah.

"Gani kukan da takeyi ne yasashi cewa ya'isa h'aka zankira maki ita amma ba yanxu da sassafen gaba' kabari anjima' Aisha najin h'aka tasa kuka tana f'adin dan Allah ka taimakeni ummata.

"Matsowa Nasir yai kusa da'ita ya duka a gabanta snn yace h'aba Aisha kiyi hakuri mana xuwa rana' idan muka kirata a irin wann lokacin me kike zaifaru? H'aka kawai bamu kirata ba sai da kike ciwon' Aisha tace eh nidai kakiramin ita naji muryarta.

"Nasir yace to Aisha amma dan Allah koda na kirata bazakiyi kuka ba? Aisha tace eh na yarda' wayarsa ya ciro daga aljihunsa yai dilling nmber mmn Aisha' yanajin ya fara ringing ya mika mata wayar.

"Aisha najin ummata tai picking call d'an ta fashe da kuka tana kiran umma' umma tace na'am Aisha' jin kukan da takeyi yasa umma cewa Aisha kiyi hakuri ita rayuwar aure dan hakuri ne' sbd ita AURE IBADA NE zaki hadu da jarabawa kala kala amma idan kikai hakuri wataran sai labari' Aisha tace Umma!!!! Umma tace Aisha banaso naji komai daga gareki sbd Allah subbuhanahu wata'ala yana fushi da macce da take tona asirin mijinta.

"dan h'aka kiyi hakuri banaso ki kasance kina daya daga cikin wanda Allah zaiyi fushi dasu' nagode da gaisuwa k'uma ki gaida maigidanki sai anjima' ta kashe wayar.
Chapter 5 · 0% Book details