← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 89

Sashe 22

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"lalla Aisha Akwai matsala dama shine dalilin zuwana kenan sbd su umma koda su kira number baya shiga h'aka ma na maigidanki k'uma ga munanar mafarkai da umma keyi a kanki.

" Aisha naji h'aka fashewa da kuka tai.

"gani kukan da takeyi yasashi kasa cin abincin dake gaban sa' jikinsa yai sanyi sosae.

" mikewa yai ya fita waje can gefe ya samu ya kira umma bayan sun gaisa h'ade da tambayar ya yasami aishan' Abdul yace gskya umma akwai matsala sbd ni kaina banji dadin ganita da nai ba.

"nan yazare komai ya sanarwa umma'umma harda kukanta take cewa idan mijin aishan yadawo yace tanaso mgn dashi.

" Abdul yace to umma.

"bayan fitar Abdul ne Aisha ta d'au abincin daya barshi yafita taci' dama kukanta da biyu sbd yunwar daya addabeta.

" itako Fatima ruwan Lipton tasha' gani eleven yayi yasata shiga kitchen taduba taga abinda yarage masu' shinkafa ya kare h'aka semovitar sae kuskus da taliya wanda basufi three three bag ba' tsayawa tai tai shiru tana tunanin ta'ina zata fara? ita k'uma a yadda takeji a yanzu a zcyrta bazata iya siyo kayan abinc ta ciyar da wata ba' sbd ma inda zata duba irin abinda Nasir keyi mata wlh koda ruwan g'idan bazata bari wata tasha ba.

"amma abu daya take dubawa sbd itama ta haihu k'uma bazataso yau ace yar'ta tai aure ta f'ada irin wnn yanayin ba' shine kawai dalilin dayasa duk yaran da Nasir zai aure bayan ya gama ci moriyarsu snn k'uma ya koresu suke bata tausayi.

" Amma suna Allah ya kara masu da kwadayinsu daga gani mutum bakasan daga inda yakeba kabashi aure' Ai ga irinta nan.

"wani d'an karamin tsaki tai h'ade da kuna gas tasa sanwar taliya jallop gaba daya dafa harda na dare tana gamawa tasawa Aisha da Abdul a kula daya sauran k'uma tazuba a kula ita da yara.

" koda ta kira Aisha tazo ta dauka da aishi tazo Fatima tace gashi keda Abdul k'uma harda na dare nayi d'an g'idan babu wani abu da yai saura komai ya kare.

"Aisha tace to' snn ta dauka takai daki.

" itama Fatima d'akin' ta tashaga wayarta ta dauko bugu daya taiwa number Nasir yashiga sbd ita kadae ce takeda wann number' daga ita sae shi kawai suke amfani dashi' ko Aisha batasan yanada wann number ba.

"Nasir yana gani kiran Fatima da sauri ya daga h'ade da cewa hello gimbiyata' Fatima najin h'aka sae tai marerece tace batada lfy tun ranar daya fita dake fama da ciwo.

"Da sauri Nasir yace kifito kice drive yakawoki hospital d'in doctor kamal nima ganinan tafe.

" to kawai tace.

"yana kashe wayar toilet tashiga ta watsa ruwa snn tafito riga kawai tasa batare da kwalliya ba ta d'au key d'in motarta ko sallamar Aisha batai ba tafita.

"dama kwance yake a hotal d'in daya kama yake hutawarsa mikewa yai ya d'au key yafita' koda Fatima ta'isa hospital d'in can gefe tai parking motar ta inda ba lallane ya ganta ba' tana gani shigowarsa tai saurin fita daga motar taje jikin wata itaciya ta rabe.

" Nasir yana parking har ya bude mota zai fita da sauri tashige juyawar da zaiyi ita yagani yace Fatima yaya jiki dae' wani Orin mugun kallo tai masa snn tace lfyta klau.

"dawowa cikin motar yai Fatima taci gaba da cewa h'aba Nasir waikai meyasa bakada imanine da tsoron Allah tun yaushe nace maka abincin mu yakare amma baka tankaniba' to wlh yau ko sanwa bamu dora ba' h'aka yara suka tafi schl.

" b'ude makin Nasir yace kinsone.

"kamar yaya Nasir?.

"bakinada kudi ba? bangane ba?.

"wlh Fatima idan Aisha tana g'idan nan bazan sisina na siye abinci ba' kinfi kowa sani ina nimana sbd iyayena nan da kuma yarana sae kuma ke...

'" haba Nasir wani irin mgn kakeyine h'aka sbd Allah' to wlh bazan yarda ba' idan har baka siyo mana abinci ba saena buga g'ida na f'adi duk irin abinda kakeyi anan' k'uma wlh har abbana saena f'adi mawa na gwammaci idan auren zai mutu nema ya mutu..

"kina mgnr banzargi ne idan akwai uban da ya'isa ya kashemin aurena dake inaso na gansa'ke bakisan aurena dake mutu karaba bane.

" cikin masifa Fatima tace toni wlh bazan zauna ba sae dae ko nakoma g'ida.

"A isgilance yace ga hanya.

"Ni dae abu daya nasani kudina nasa na auro yarinyarga a lkcn da nake sonta yanzu k'uma nace banayi dolene?.

"haba Nasir sbd Allah me baiwar Allah ga tai maka?

"bataimin komai ba gajiya ne kawai nai da'ita wlh Fatima wani aure nakeso naji shiyasa' ni k'uma banida ra'ayin tara mata dayawa' ko Hauwa ma da kikaga mun dade da'ita dan bazama takeyi ba shiyasa' kinga da'ita da babu duk daya ne..

"cikin fushi tace kai wlh baka isa ba' k'uma wlh kai da auren saedae idan anayi a lahira' amma a duniya kagama kenan.

" dariya yai h'ade da cewa wlh shiyasa nake kara sonki Fatima ta.

"Amma yanzu abinda za'ayi ga wasu kudi sae dae babu yawa Dan basufi ten thousand ba kisiyewa yarana sweet sbd nasan dae wanda na siyo yakare' amma idan kinaso nasiyo abinci a g'idan nan to ki tabbata Aisha tabar g'idan.

" dole yasa Fatima amsar kudin d'an batada yadda zatayi.

"Washe gari Abdul na idar da sallar asuba ya d'au jakarsa zuwa bauchi' Aisha tai kuka kamar me' d'an a zcyrta ji take kamar tabisa....

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

MMN USWAN

ALHAMDULLILAH
FANS INA MIKA GODIYATA GAREMU A GSKYA INAJIN DADIN CONMM D'INKU D'AN SHIKE KARAMI KARFIN GWINWA WAJAN TP. NAGODE NAGODE SOSAE FANS ALLAH YABAR ZUMUCI.

BABY ZULAIHAT
BEST FRIEND GRP

MAIMUNA MUHAMMED MMN USWAN GRP

AISHA MAGAJI KD
LONG LIVE HOME OF NVL

JIJJINAR BANGIRMA GAREKI MMN MEEMA MARUBUCIR RAIHANA AND YARAN MIJINA NAGODE ALLAH YABAR ZUMUCI.

DUK INA MIKA GODIYATA A GAREKU, CMM DINKU BA KARAMIN KARAMI KARFIN GWIWA YAKEYI BA TNX SO MUCH ALLAH YABAR KAUNA DA ZUMUCI.

READERS GA QUESTION PLS MISALI ACE KECE KISHIYA TA D'AU TAKARDAN SAKI TA BAKI, BAFA MIJIN DA KIKE ZAMANSABA KISHIYA DAN ALLAH YAYA ZAJI???

AMSATA TANA GAREKU. INA SAURARO👂.

2⃣1⃣

"Abdul be'isa ba sai bayan sallar magrib snn ya'isa g'ida' lokacin umma na zaune akan sallaya tana lazumi h'ade da jiran isha'i yayi tai Abdul yai sallama.

" jin salamarsa ne yasa umma shafe addu'a snn tai masa barka da zuwa Abdul' yana murmushi yace yawwa umma sannu da g'ida' umma tace yawwa sannu da hanya.

"bayan sun gaisa ne umma ta mike ta kawo masa abinci' Abdul yaci suna hira har Abba yashigo'shima zama yai sukaci gaba da hira' sae dae duk irin hiran da sukeyi be yarda ya f'adi halin da Aisha take ciki ba har suka kare hira.

"Da asuba lokacin Abdul ya dawo daga masallaci kai tsaye d'akin Abba yashiga gaida shi' bayan su gaisa ne Abdul yake bayyanawa Abba halin da Aisha take ciki' wuf umma tai ta antayo d'akin ashe dama tana gada b'akin kofa zata shigo jin suna mgn ne yasata dakatawa ta tsaya daga b'akin kofan.

"Cikin gigita umma tace mekace!!! Abdul Ashe dama halin da 'yar'uwanka take ciki kenan shine ka boyemi Abdul' umma tana karisa mgnr da fashe da kuka h'ade da cewa ni dama tunda naketa mafarke munana nasan ba lfy.

"shiru Abdul yai yana sauraran maganganu da umma keyi' Abba dake zaune akan cushion yace h'aba Hafsatu wani irin mgn kikeyi h'aka ta yaya za'ace mutum zaiyi rayuwa batare da jarabtaba banlema rayuwar aure.

"Ita rayuwa ta gaji h'aka dole sai da jarabta wani yazo maka a farko wani k'uma a tsakiya wani k'uma a karke' idan Allah ya jarabceta a farko ta gode masa ma wata kila jin dadin ta na gaba' d'an h'aka a guna ba wani abu bane Allah ya fidda dasu lfy.

" Nace dae duk suna lfy ita da maigidan nasu? Abdul yace ni wlh Abba tunda naje garin har nabari banga maigidan ta ba'wani abu mmki koda na tambayeta takasa bani amsa guda daya kwankwara sae faman kame kame takeyi.

"umma tace kaga abinda nake f'adi h'aka ko Alhj to nidai wlh bazan yarda nayi asarar yan'daya da Allah yabani ba wayasani ma ko d'an yankai kaine....

"A take Alhj ya daka mata wani irin tsawa h'ade da cewa h'aba hafsatu wani irin mgn kikeyi h'aka sbd Allah' to wlh idan bcc kikeyi ki falka k'uma ina mai tabbabatar maki da kiyi gaggawar rokonsa gafara sbd mummunar zato da kikai masa.

"Umma tace nifa ba zarginsa nakeyi ba.

" Abba yace idan ba zarginsa kikeyi ba to menene amfani irin wnn mgnr? ni dae abinda nakeso dake shine nafi bukatar da kitayata da addu'a Allah yabata zaman lfy ita da mijinta' idan ma wani hali take ciki Allah ya fidda'ita.

"jinsa kawai umma keyi amma duk mgnr da Abba keyi bekai zacin ta ba.

"shiru da tai tana share kwalla yasa Abba cewa hafsatu kina jina ko' umma tace nidae gskya Alhj hnklina be kwanta ba sbd Allah kadae yasan halin da Aisha take ciki' in da zaka amince ne da sae naje na ganta...

" kije ina hafsatu?

"gun Aisha mana.

"Tab d'in jam wlh bantaba sani bakida hankali ba sae yau'Ashe h'aka kike? dama ance ku mata habkalinku daya yake dana yaro' idan banda rashin hankali daga yaro yazo da zance sae kice zaki' to wlh bari kiji ko da wasa kada ki sake tunanin h'aka' ba keba wani ka daga cikin g'idan nan babu wanda zaisake zuwa tunda abin yazama h'aka.

"Umma tace amma Alhj....

"Amma me? banaso nasake jin b'akin wani daga cikin ku' d'an h'aka kutashi kubani gu.

"H'aka duk suka mike jiki a sanyaje.

~~~ ~~~~ ~~~
Tun bayan tafiyar Abdul Aisha kullum cikin kuka take' ko fitowa parlour batayi' idan har kinga ta fito to abinci tazo dauka bayan h'aka zama takeyi a daki tai ta faman tunani kala kala.
Chapter 22 · 0% Book details