← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 89

Sashe 58

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"ihu yasa yaci gaba da juyi acikin ruwan' ihun sane yasa zhrdee juyowa a guje yaje ya daukesa shima yana ihu a guje yafita zuwa d'akin Hjy' Aisha najin ihunsa itama gudu tasa zuwa d'akin taga abinda ke faruwa"

"zhrdee yana zuwa Hjy ta tarasa h'ade da salati garin yaya h'akan yafaru?" amsarsa tai ta cire masa riga gaba daya jikinsa ya salube amma banda fuska"

"rikesa tai tana masa addu'a tana tofa masa' zhrdee yace Hjy muje hospital' Hjy tace a'a barshi mu gani tuku"

"juyawa zhrdee yai yakoma d'akin yana shiga sukai karo da Aisha zata fito zuwa d'akin Hjy' yanzu Aisha abinda kikaimi kin kyau kenan?"

"me nayi k'uma?"...

" kafin ta karisa ya dauketa da mari h'ade da tokari' tana f'adi yasake binta ya hayeta da duka' yana f'adi Dan tsabar b'akin ciki sai ki konami yaro..

"Aisha naso tayi mgn amma ina zhrdee be barta da fukaba"

"jin hayaniya yasa Zainab b'ude kofa tafito daga d'akin ta' jin hayaniyar daga d'akin Aisha ne yasa ta zuwa nan' gani Aisha ta dan'no a guje zuwa d'akin Zainab' gani h'aka yasa itama Zainab komawa a guje suka shiga d'akin suka rufe"

"biyosa zhrdee yai d'akin Zainab tabawar da zaiyi yaji shi a rufe' kofa yasa yana tokarin kofar yana f'adi dan baki b'ude ba wlh saina fasa kofar' gani zai fasa da gske yasa Zainab b'ude kofar"

"batare daya tsaya duba ko wayeba fisgo Zainab yai waje"

"ihu tasa tana f'adi a'a banine ba"

"snn yasake ta ya koma kan. Aisha' ko kafin yai kanta Aisha takoma d'akin ta' a guje zhrdee yabita kamar mahaikaci' gani zai rufe kofa da'ita a d'akin yasa Aisha daukar mayafinta a guje tabar g'idan"

"duk da h'aka binta yai shima da gudu' a guje Zainab tazo ta rikesa ta baya tana ihu h'ade da kuka"

"zhrdee yai kokarin tureta yabi Aisha' amma kuka ko mai yagani ohoo tsayawa yai yana ajiyar zcy"

"itama Zainab tai h'aka ne sbd gajeran wandone kawai a jikinsa"

"kamo Zainab yai suka koma cikin' gani zasu shiga bangaren Hjy yasa Zainab cewa a'a kaje kawai"

"Aisha na fita kai tsare g'idan su tanufa' a kasa kafa babu ko takalmi

📖🖊
☘☘


*AURE IBADA NE*

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

🌳 *impacting valuable knowledge and Entertainment is our concern* 🌳

*story written by Mmn uswan*

_*I didecated this page to Ahmad (FAHIM) Zhrdee Yahya maburya kwantagora*_

_*gareku masoya aure ibada ne ngd sosae da soyayyarku a gareni ngd sosae*_

_*masoya Aisha duk naga conmment naku k'uma ngd sosae' but kunsan ba kowani mutum ne yake ina controlling kansa a lkcn da yai fushi bako' k'uma dole zhrdee ya nuna nushinsa akan Akbar sbd zaiga kamar da gangan tai masa h'akan' zai ma iya cewa dan bata haihu bane yasa tai masa haka*_

_*idan har namiji mai son yarane koda kece kika haifa saikinyi hkr dashi akansu sbd duk abinda kikai baki iya bane' k'uma bazai ganiba' banle ba kece kika haifa ba' shiyasa Aisha sai tai hkr sosae da zhrdee' duk da irin soyayyar da yake mata' karkuga laifinsa' saidai dukan da yai matane too much wlh har taban tausayi*_ 😉😉

_*Aisha kada ki damu zhrdee nakine forever cool ur mind*_ 🤣

🇮🇳 *_FASMA NIGER_* 🇮🇳

_*ina tayaki murnar kammala littafinki mai suna (sanadin accident) hakika kin wa'azartar k'uma kin nishadarta' dukkan kura' kuran da kika samu a ciki ubangiji Allah ya yafe maki' wa'zartarwa da kikai kuma Allah tabada ikon aiki dashi' Allah ya kara basira da zakin hannu ameen. sai mujiki a littafi na gaba*_ 🤣🤣

4⃣5⃣

"zhrdee yana shiga d'akin Hjy gun *Akbar* yanufa' gani yadda yake faman kuka yasashi zama kusa dashi h'ade da daukarsa har zai rungume kenan Hjy ta daka masa tsawa"

"h'aba zhrdee menene kakeyi h'aka baka gani ciwone a jikinsa zakaje ka rungume sa' ka shinfidashi kawai yasha iska"

"to ai gani nayi be daina kuka"

"to ba dole yai kuka ba kuna wasane' wai ma garin yaya akai ya konene?"

"wlh jawo plast yayi jikinsa"

"to idan banda hali irin naku' kusan akwai yaro me rarrafe zakuje ku ije plast a inda yaro zai iya ja"

"wlh Hjy tsotsayine"

"tsotsayi ko ganganci' wani halin banza kawai"...

" dan Allah Hjy kiyi hkr"

"waini ina matan kane gaba dayan su fa babu wanda ya leko"

"duk Hjy na mgnr ne tayiwa angon nata fifita"

"tananan"

"ban gane tananan ba' tananan ko sunana"

"who Zainab tana ciki"

"ita Aisha fa?"

"shiru zhrdee yai"

"da kaifa nakeyi"

"nakoreta g'idan su"

"g'idan su kace' me tai maka?"

"laifine taimi"

"eh"

"wani irin laifine tai maka h'aka da har zaka koreta g'idan su"

"laifi dai tayi' Hjy yaronga har yanzu be daina kuka ba' kodai na daukesa na kaisa gun mmnsa tabashi nono ko zaiyi shiru"

"a'a bassa kawai taji da kanta' kamar cikinta zaikai wata bakwai ko"

"eh tashiga na bakwai kenan"

"to kagani ko' kyalesa kawai itama tasamu ta huta k'uma taji da kanta"

"Hjy ban fahimata ba?"

"yayesa za'ayi kawai"

"yaye fa kikace Hjy da wnn ciwon?"

"eh' kada karamu babu abinda zai samesa"

"Hjy Dan Allah kiyi hkr a barsa har yawarke"

"zhrdee kenan idan akace a barsa har sai ya warke ashe zasu sha nono tare da kanisa kenan"

"kamar yaya Hjy?"

"snn ta haihu mana"

"yanzu Hjy kina nufin Abbana bazai warkeba har Zainab ta haihu"

"to Ai kuna h'aka take"

"himm kawai yace"

"snn yace to Hjy yanzu menene abinyi?"

"kamar yaya?"

"wlh Hjy nidai nafi aminta da akaisa hospital"

"to shikenan tashi muje' amma kafin mufita jeka ka kirami Zainab"

"to kawai zhrdee yace snn ya mike' yana shiga d'akin Zainab ya sameta kwance' Zainab Hjy nakira"

"tace h'ade da mikewa tanufi d'akin Hjy' riga yasa kawai yafita"

"da sallama Zainab ta shiga Hjy ta amsa da shigo'

"har kasa Zainab ta duka tace gani Hjy' duk a lkc *Akbar* bebar kuka ba' shiyasa Zainab ta dauke kanta daga garesa bata kallesa amma tanajin zafi kukan da yakeyi har cikin zcyrta"

"waini Zainab ko kinsan abinda ya h'ada Aisha da zhrdee da har ya koreta g'ida?"

"nima bansani ba' ihunta naji tashigo dakina a guje' yana biye da ita"

"subhanallh' harda dukane?"

"wlh a guje tabar g'idan' ko takalmi babu"

"dawa ya tambyeki' waya tashi ki koma daki"...

"ita kanta Zainab da hjyn basusan zhrdee ya shigoba"

"da sauri Zainab ta mike har zata fita *Akbar* ya rike mata haban zani yana kuka ta daukesa"

"da sauri zhrdee ya daukesa cikin tsomma' gani yadda Abba ya koma kwallane kawai suka zubowa Zainab ta saurin fita sbd kada Hjy ta gani' amma zhrdee yagani' kai kawai ya kada' hijab kawai Hjy tasa snn suka fita"

"saida Hjy ta shiga mota ta zauna snn zhrdee ya mika mata *Akbar* ya shinfida mata shi a cinyarta snn ya zaga yashiga suka nufi hospital' a hanyarsu na tafita hospital ne Hjy take sake tambyarsa abinda ya hadasa da Aisha"

"duk da h'aka shiru zhrdee yai yaki fadan abinda Aisha tai masa"

"dama ni bance dole sai ka sanar dani tsakanika da matarka ba' amma koma me tai maka inaso yazama shine farko k'uma shine karke kada kasake dukan ko daya daga cikinsu' kanaso ka zama namiji me dukane?" to wlh kada ka kasake h'aka"

"to naji Hjy k'uma ngd"

"idan har laifi ne tai maka meyasa bazaka hukuntata a d'akin taba' bayan ka duketa k'uma ka koreta?" to wlh kada ka sake h'aka' k'uma muna dawowa daga hospital inaso kaje ka dawo da'ita"

"shiru zhrdee yai be tanka ba"

"kana jina kuwa?"

"eh' naji Hjy' amma dan Allah kibari zuwa yamma snn natafi daukota"

"amin amma ka tabbata yau tadawo"

"eh zanje ai"

"suna isa hospital doct ya dubasu' maguguna ya basu suka dawo g'ida"

"waya Zainab ta dauka ta kira inna *Hulaira* inna na dagawa Zainab tasa kuka' a gigice inna tace lfy Zainab' meke faruwa?"

"cikin kuka Zainab take fadiwa inna *Akbar* ne ya kone"

"subhanallh' Zainab garin yaya?"

"cikin kuka tace nima ban saniba a d'akin Aisha ne"

"Aisha fa!!!"

"eh Aisha"

"nima ban saniba Bbn sane ya kaisa d'akin"

"to shikenan Zainab amma dan Allah ki daina kuka h'aka' k'uma in Allah ya yarda idan bbnki yadawo kasuwa munanan zuwa"

"to inna sai kunzo"

"to Zainab' amma fa kidaina kuka kinga bake kadai ace bako"

"Zainab na kashe wayar zhrdee yashigo' ita k'uma Hjy tai bangaren ta da *Akbar* Zainab naji shigowar zhrdee da sauri ta share hawayen dake fuskanta' tace kadawo"

"nadawo' amma yah!!! naga kina kuka?"

"wasu kwallan suka sake zubowa tace babu komai"

"matsowa yai kusa da'ita snn ya jawota jikinsa ya rungumeta h'aba Zainab kuka me kikeyi h'aka kiyi hkr mana abban ma da kike kuka danshi yasamu sauki har yai bcc'

" himm kawai Zainab tace"

"da gske Zainab"

"to garin yya akai ya kone?" bayan ka daukesa lfy daga nan d'akin?"

"tsotsayine kawai Zainab".

" tsotsayi kamar yaya? " kodai Aisha ce ta konasa"...

"a'a ba'ita bace' tsotsayi nedai kawai"

"idan ba'ita bace to metai maka da har kai mata irin wnn duka h'aka' bayan tunda nake dakai baka taba koda marintaneba banle duka".

" laifi kawai taimi raina ya baci yasa nayi mata duka' amma ba'ita ce ta kona Abba ba' *Akbar* a hannuna ya kone"

"a hannunka k'uma kai da kake daki ina kasamu ruwan zafi da har kasamu ruwan zafi?"

"eh ninace takowomi daki' bayan tadawo ta'ije har na b'ude plast d'in sai naje dauko abu kafin nadawo shine *Akbar* yaje ya yawo plast d'in jikinsa"

"himm kawai tace amma bata yarda da mgnrsa ba"

"kiyi shiru Zainab"

"yanzu ina Abba d'in?"

"yana gun Hjy yana bcc"

"zama Zainab tai a b'akin gado taci gaba da sharban hawayenta"

"da yamma bayan sallar isha'i zhrdee yaje g'idan su Aisha' da sallama yashiga cikin g'idan' ummata ta amsa da shigo mana"

"bayan su gaisa shiru zhrdee yai"

"umma tace yaya dai zhrdee?"

"gun Aisha nazo"

"kwanawa Aisha kira tai"

"da sauri Aisha tazo' tana zuwa taga zhrdee duka gaban umma' tsaki tai ta juya zata wuce"

"tsawa umma ta daka mata' waye sa'arki anan da mikewa tsaki"

"nifa banji dake ba"

"to dawa kikeyi?"

"tai shiru"

"dawo nan ki zauna"
Chapter 58 · 0% Book details