← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 89

Sashe 29

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"kai son kenan babu damuwa insha Allahu.

"ngd Abba".

"Aisha ma tana shiga gida ta sanarwa umma mgnr da sukai da zahradee.

"da umma da Abba suyi murna sosae dajin h'aka.

"bayan fitar zahradee Alhj ta shigo kwanciya shine Abba yake sanar mata.

"haba Alhj wani irin mgn kakeyi h'aka?' sai kace ita kadaice autar mata' auren fari shine zaifara da bazawara' bazawararma Aisha da tanimi kashemin shi.

"to wlh tana isa ba"

"ko k'uma kece baki isa ba' idan har na'isa dake banaso kikara cewa kala' tunda bazaki sawa lamarin albarka ba.

"shikenan k'uma Dan Allah kayi hkr.

"babu komai ya wuce"

"amma Dan Allah ina rokon arzikin abarsu mu zauna tare sbd idan kutafi kasuwa nasamu a bokiyar hira.

"babu damuwa Alhj gida ga dakuna burjik nan' kiduba inda yafi dacewa sae a gyara masu.

"to ngd"

"a nata zcyr tana f'adin Aisha zakici ubanki Dan wlh saina ramawa dana abinda kikai masa.

"washe gari Abba da kansa yaje g'idan su Aisha'Bbn Aisha yana fitowa cikin girmamawa suka gaisa h'ade da bawa juna hakuri snn Abba yafadi abinda yakawosa.

"abban Aisha yai murna sosae snn yace babu damuwa.

"nan suka daedae ta mgn juma'a me zuwa daura auren Aisha da zahradee.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

MMN USWAN

KAI,KAI,KAI, AMINCI 1 AND 2 FOLLOW BY MMN USWAN GRP GSKYA INAJI DADIN COMMENT DIN KU SBD COMMENT DINKU KE KARAMIN KARFIN GWIWA GSKYA NGD NGD SOSAI ALLAH YA BAR KAUNA.

HOME OF HAUSA NVL WTSPP AND HAFSAT HAUSA NVL H2 FCBOOK DUK INA GODIYA FANS ALLAH YA BAR KAUNA.

2⃣7⃣

"washe gari da safe Aisha taje g'idan ubaida bayan su gaisa take sanar da'ita mgnr zahrd.

"ubaida tai murna sosae da fatan Allah yasa ayi a sa'a".

"amin ngd ubaida"

"amma Dan Allah na tambayeki mana Aisha".

"Allah yasa nasani".

"Dan Allah Aisha yaya kikaji a lkcn da zahrd yazo a matsayin yadawo gareki?".

"him ubaida kenan".

"a rayuwata ubaida babtaba tsammani zahradee zai dawo gareni amma wani hukunci na ubangiji yau way nine zahradee zai aura.

"him" Aisha kenan"

"wlh dama tun farko banso aurenki da Nasir ba' kawai dae dan naga yaddau kika zake kika nuna kinfi sonsane akan zahradee shiyasa' k'uma kinsan ance matar mutum kabarinsa koda na yini daya Allah yariga ya rubuta zaki zauna da Nasir.

"h'aka be ubaida' wlh bantaba tsammani Nasir zaimi h'aka a rayuwa ba' shiyasa har yanzu nake kwankwanto Nasir din dana sanine kuwa"

"a'a" Aisha ba shibane wanisa ne".

"Aisha idan zaki kwantar da hankalinki ki rungumi masoyi dae da yafi maki".

"Nasir d'in me Nasir din bazan' idan yana soki da bazai turoki g'ida ya mance dake h'aka ba'daga mgn sae ya'aiko da takardan saki.

"Ni wlh idan banda ina gani girmansa dako gaisawa bazamuyi ba.

"ba mmki dama tun farko ba sonki yakeyi ba' sha'awace tasa ya aureki' yanzu k'uma da kika daina bashi sha'awar ya koroki.

"wlh Aisha duk da kinki f'adiwa kowa irin zaman da kikai da Nasir amma duk wanda yasan menene jin dadi Aisha baki tare dashi sbd jikinki ya nuna.

"ke idan bandama abin ubangiji da yake dauke mana nawin mazajanmu kawata ina zakikai Nasir' mutum ga girma ga tsayi kamar basamude.

"amma ke dubeki kamar akama a karya".

"dariya Aisha tai".

"Aisha idan zaki kwantar da hankalinki ki kwantar kibada kai biri ya h'au.

"a rayuwa idan ka auri me sonka wlh kagama komai koba komai ke kuruciya shima h'aka kinga sae kumore kuruciyarku banlema ke da kika taba aure kinga kenan sae yadda kika juyashi sbd yanzu kinfishi sani kan duniya.

"amma kinsan yakamata kiyi gyara ko".

"gyaran me k'uma?".

"keko kigane mana".

"shewa sukai h'ade da tafi".

~~~ ~~~ ~~~

Gskya Nasir ya kamata muje g'ida kano' sbd mudade bamuje ba".

"h'aka ne Fatima amma kinsan na f'adi maki banida lfy ko?" baki gani ko fita banayi?".

"h'aka ne' Allah ya baka lfy".

"amin Fatima".

"Nasir kodai hospital ne zamu?".

"a'a" kibari mugani tuku kin dict kamal yana zuwa har g'ida ya dubani idan muka tafi hospital zaice banyaba da kokarin da yakemi bane.

"h'aka ne kam"

"amma kibari mugani zuwa gobe".

"gobe k'uma?"

"Eh"

"to' Allah ya kaimu".

"amin"

"amma yanzu ya kakeji jikin naka?"

"wlh Fatima ni kadae nasan abinda nakeji' cikin jikina kamar wuta ake huramin".

"a'ahhhh!"

"kashi magani rana?"

"a'a" ban shaba"

"bari to na dauko maka kasha".

"a'a" dibomi ruwa nayi addu'a kawai sbd nafi jin dadinsa".

"to tace h'ade da mikewa".

"daga nan ki kirami su Jabeer da Khadijat.

"Fatima na dibo ruwan tare suka dawo dasu Jabeer.

"amsar ruwan yai yafara addu'a' saeda yadade yanayi snn yasha ragowar k'uma Fatima ta amsa ta shafa masa a jiki.

"bayan ta gama bayansa taje ta zauna gab dashi h'ade da dora hannayenta a kafadarsa tana masa tausa" musmushi yai alamu nuna jin dadin abinda take masa".

"gani su Khadijat da Jabeer suna kallonsa bude masu hannu yai alama suzo.

"a guje sukaje jikinsa".

"h'aba Khadijat meyene kukeyi h'aka?" baku gani beda lfy ne".

"a'a kyalesu kawai' basuda inda yanan.

"amma gani nayi bakada lfy ne ai".

"kamar ki damu".

"Nasir nace kodae a sanarwa g'ida ne?'.

"me fa".

"a'a barsu kawai".

"himm Nasir kenan".

"tun daga lkcn Fatima bata sake mgn ba.

"cikin dare around 12AM jikin Nasir ya tsanata'gani yadda yake hasa-hasa Fatima ta kira gateman ya taimaka mata suka dauki zuwa mota.

"Da sauri tai rushing dinsa zuwa hospital din doct kamal' suna isa emergency room aka kaisa doct kamal ya bashi taimakon gaggawa h'ade da samasa drip da allurai snn yasamu bcc.

"Tunda Nasir ya sa bcc be falkaba sai bayan allar asuba snn ya falka' yana falkawa daidai lkcn Fatima na zauna a gefen kasan' gani ya bude ido yasata dagowa da sauri tana f'adin sannu Nasir yaya jikin?".

"kai ya daga mata alama da sauki".

" a hankali yake kiranta amma batajiba sai dai kawai gani bakinsa tai yana motsi' hakan yasa ta kara kunnita a bakinsa snn taji abinda yake cewa.

"Ashe yara yake tambaya.

'"Fatima tace suna gida.

"da hannu ya nuna mata alama taje gunsu.

"Fatima tace aa Nasir babu damuwa kaidae kaji da kanka kawai.

"duk da h'aka Nasir yaki yarda gani ya nace yasa Fatima taje ta dauko su.

"anan su Khadijat suke yini da yamma Fatima ta medasu gida ita k'uma ta dawo hospital.

"a hankali Nasir ya fara samu sauki dan har mgnrsa yafara fita ba kamar da ba.

"da Bilyaminu yazo bayan sun gaisa da Fatima Nasir yace Fatima tafita ta basu gu zasuyi mgn.

"h'aka ta fita dan babu yadda zatayi' bayan ta fitane suka sake gaisawa da Nasir snn yai masa mgnr da yakawoshi.

"Nasir yace babu damuwa bari yanzu nai kama transfer a account dinka idan yaso sae kaci gaba da aikinka.

"Okay kawai yace".

"bayan ya fitane Fatima ta tare Bilyaminu tace Dan Allah Bilyaminu inaso nai maka wani tambaya?".

"Allah yasa nasani".

"Dan Allah bilyaminu waini me kuke kullawane kaida Alhj Nasir?".

"haba Hjy me kike tunanin zamu kulla kuwa".

"humm bilyaminu kenan' kasan dae ni matan Alhj ne k'uma bazan so ace yau ya aikata abinda zaije ya dawo ba ko?"

"haka ne but Dan Allah kiyi hkr sbd alkawari naiwa Alhj akan koda wasan bazan bari wani yasani ba..

"haba bilyaminu wani irin abu kuke aikatawa ne da bakuso wani ya sani.

"babu komai sai alkairi'amma tunda kin matso kiji zaki iya tambayar Alhj idan yafadi maki da kansa fanilabihamduli.

"to shikena ngd".

"Allah ya kara sauki"

"amin ngd".

"bayan Fatima ta koma daki gu tasamu kusa da Nasir ta zauna hade da dora hannayeta akan kirjisa' snn tace Nasir Dan Allah na tambayeka mana?"

"Allah yasa nasani'.

"Dan Allah Nasir mekuke kullawane kaida bilyaminu?"

"na mefa?"

"kusan lkt da dama idan yazo zakuyi mgn bakason yi a gabana".

"Eh" h'aka ne'be shafeki bane yasa".

"yanzu sbd Allah Akwai abinda zakayi kace be shafeni ba?"

"amma kinsan a rayuwa babu abinda nake boye maki idan zanyi me'kyau ko akasin hakan ko?"

"h'aka ne".

"to kiyarda mi beshafeki bane".

"himmm"

"Fatima abinda nakeso kigane wnn Abu inayine dan ni dake da k'uma yaranmu fa"

"to shi abin beda suna?".

"yanada suna amma kibari idan lkc yayi zaki sani.

"Allah yasa a aikata alkairi".

"alkairi nema Fati na".

~~~ ~~~~ ~~~~

Allah ya kawomu yau daurin aure Aisha da zahradee' gidan su Aisha kam babu wasu mutani sbd ummata tace bazatayi taroba sbd ba'a dade da taron farko ba yanzu k'uma ace ana wani taro' ita gskya bazatayi ba.

"hakan yasa babu wasu mutuni sosai' saidai wanda baza'a rasaba.

"goga zahradee kuwa yaiwa Aisha dike dike na ban mmki' h'aka shima kanshi.

"gidan su suma Alhj bata sanarwa abokanar arziki ba'sai dangi kawai suna yakama dole ne yasa.

"karfe goma daedae aka daura aure.

"zahradee najin anshafe wani irin kabbara yai wanda shima kansa besan lkcn da yai ba.

"bayan sallar magrib aka kai amarya gidan mijinta.

"ya kumbo ita ta kai Aisha dakin uwar miji bayan sun gaisa matan dake dakin kowa ya tofa albarkacin bakinsa da fatan zaman lfy.

"fuska Aisha a rufe da kyale ta mike kenan zasu fita kyalen yai santsi fuskanta ya bude.

"da sauri taja ta rufe.

"a lkcne daya daga cikin matan dake zaune a dakin ta karewa Aisha kallo.

"mikewa tai h'ade da kiran Hjy su shiga daga cikin bedroom' duk matan dake zaune su baza kunni suji abinda zatace.

"suna shiga matan tace ke Hjy dama wnn aishan ne zahradee ya aura?"

"Eh ita ce".

"amma kika yarda".

"kamar yaya menene da'ita?"

"hmm" Hjy kenan".

"lfy?"

"yanzu sbd Allah zakice bakisan komai a kanta ba".

"kamar yaya?".

"kodan tabata aure?"

"aure me?" idan sbd aurene Ai me sauki ne".

"to menene?".

"na tabbatar maki Aisha dai HIV ne da'ita k'uma ance ba'a gun kowa tasamuba sai gun tsoho mijinta.

"HIV fa kikace"

"kwarai da gske".

"kan ubantan uban nan' Ashe da kasa.

"yau za'a yita".

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F. O. W.☘.

MMN USWAN

2⃣8⃣

"me za'ayi Hjy?"

"Dan Allah duk sbinda zakiyi bazan hanaki tunda d'anki ne' k'uma lfyrsa tafiye maki komai amma kibari idan jama'a saragu duk abinda za'ayi sai a yisa.
Chapter 29 · 0% Book details