← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 20 OF 89

Sashe 20

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Nan Hjy ta h'au f'ada inda take shiga banan take fita ba' h'aba Alhj ni da kae be'isa muyi shawara ba sae da zahradee?

"Murmushi Alhj yai snn yace son ina sauraranka.

"Zahradee yace Abba abar mgnr kai kayan nan tuku' a gigice Hjy tace mekace zahradee?

"Shiru zahradee yai.

"Alhj yace son kasan abinda kake f'adi kuwa? Murmushi karfin hali yai amma duk wanda yasan me ake kira damuwa fuskan zahradee ya baiyana.

"Karewa zahradee kallo Alhj yai snn yasa hannu ya dagosa ya zuba masa ido cikin ido ya kare masa kallo snn yace son any prbms?.

"Kai kawai yakada sbd a yadda yakeji a zcyrsa bazai iya masu bayani ba' gani ransa yafara baci da sauri yafita yabar d'akin.

"Jikin haifiyarsa yai sanyi sosae'dukkansu su biyu sun kasa mgn.

"Da sauri Alhj yasa jallabiyarsa yafita zuwa part d'in su zahradee.

"Koda yashiga gani zahradee yai zaune a bakin gado ya zabga uban tagumi hannu bibbiyu' dukaww Alhj yai a g'aban zahradee h'ade da dafe kafadar sa yace son wani abune yake faruwa wanda ka kasa sanar dani?

"Shiru yai sae dae ido kawai.

"Son pls talk.

"Nothing'k kawai yace.

"Lock son inaso kasan da cewa ni fa mahaifinka ne' wanda a duniya bakada kamarsa' idan har kasan nine na haifeka inaso jin abinda yake faruwa.

"Zahradee naji h'aka fashewa da kuka yai' hade da kifewa a gado yana f'adin Allah Abba kafita kawai Abba....

"Kukan da yakeyi ya sashi kasa mgn.

"Gani irin kukan da yakeyi har jikinsa na rawa yasa Abba dagashi ya rungume yana f'adin is okay son.

" mgn Abba yai ta bashi har sae da ya numfasa yaga ya dae na kuka snn Abba yafita a dakin.

"Yana fita sukai karo da Hjy har zata shiga dakin Abba yace kada ta shiga ta rabu dashi.

"Hakan yasata komawa da baya.

"Batare da bata lkc ba Abba ya shirya ya fita zuwa g'idan su Ruslayni a kofar g'ida ya tsaya yasa yaro dake wucewa yai masa sallama da Ruslayni.

"Dayake shima yashirya zuwa kasuwa inda yake harkokin kasiwancinsa yasashi fitowa tare da d'an aiken.

"Gani motar Abba ne yasashi karisawa da sauri yaje inda Abba yai parking har kasa ya duka ya gaidashi' bayan sun gama gaisawa ne Abba yace nasan zakayi mmkin ganina a kofar g'idan ku' k'uma da safiya h'aka ko.

"Murmushi Ruslayni yai h'ade da cewa wlh kuwa Abba' amma Allah yasa dae lfy.

"Abba yace babu komai dama akan mgn abokin kane...

"Da sauri Ruslayni yace wani abune yafaru dashi?.

"A'a".

"Akan mgn aurensa ne ko kasan abinda ke faruwa a tsakanisa da yarinyar da yake so?

"Gaskiya abba banida lbr komai.

"Batare kuke zuwa g'idan su yarinyar dashi bane?.

"A'a" abba ni tun farkon zuwwnsa g'idan su Aisha yadda suke masa yasa naga kamar abin da rainin hankli shiya na dae na binsa.

"Amma wani abune ya hadasu da aisha?.

"Daga nan abba ya kwashe iya abinda yasani ya f'adiwa Ruslayni.

"Himm wlh nidae dama tun farko wlh Allah Abba Aisha kwata-kwata bata min ba'SBD daga gani idonta batada da mutunci' amma yanzu ina yake?.

"Abba yace to fa' Allah ya'kyau ta.

"Yana g'ida".

"Okay daga nan can kawai zanwuce.

"Nan sukai sallama.

"Tun daga lkcn Aisha tahana Alhj Nasir zuwa kofar g'idan su' Alhj Nasir babu yadda beyiba akan Aisha ta sanar dashi dalilin h'aka amma taki' cewa tai yai hkr tanaso koda zaizo yazama mgnr aure ne yakawosa amma yanzu idan yazo zai'iya bata mata shiri.

"Shima dayake akwai abinda yake shiryawa zcyrsa yasa hakan be damesa ba.

"Washe gani da yadda abba yatara duk yan'g'idan snn yasa aka kira zahradee dake kwace a daki yazo parlour' abba yace son gani da yan'uwanka' idan ni bazaka iya f'adimi ba to ga yayyinka sae kasanar dasu abinda ke faruwa.

"Shiru zahradee yai kansa a kasa.

"Shamsudee yace ba dakae akeyi bane.

"Zahradee yace Abba nafasa auren...

"Zahradee ya karisa mgnr ne h'ade da mikewa yabar gun.

"Gun yayyin hada ido suka duk sunkasa mgn SBD mmki.

"Salati kawai Hjy tai ta sanarwa ubangiji.

"Shamsudee da Nurudee mikewa sukai suka bishi daki' koda suka shiga babu irin tambayar da basu masa ba amma zahradee yace shidae fasawa ne kawai yai.

"Gani sauran kwana hudu biki babu wani abuda yashigo daga g'idan su zahradee' yasa umma tasami Alhj Muhammad da mgnr' shima yace abinda yana damusa amma idan yakira beyi laifiba?

"Umma tace laifi me? Kaidae kira muji abinda yake ciki.

"Wayarsa ya daga ya kira Alhj Kailani bayan su gaisa ne Alhj yace dama bugowa nai na tambaya sbd saura kwana hudu baku zoba baku turo wani daga bangarenku yazoba banle muji ina muka tsaya.

"Alhj yace eh hakan da kai yayi ko dama baka kiraba ni da kaina zanzo nasar dakai cewa mgnr aure dae babu idan yarodae yace yafasa.

"Yana fadin mgnr ya kashe wayarsa.

"Salati Alhj Muhammad yasa' cikin gigita umma tace lfy? Alhj yace mgnr aurene babu sunce su fasa.

"Fashewa da kuka umma tai hade da salati tana fadin yanzu SBD Allah irin cin mutunci da zasu mana kenan.

"Jin kukan umma ne yasa Aisha fitowa a guje daga dakinsu tana fadin umma lfy.

"Cikin kuka umma tace idan su zahradee ne wai sun fasa auren.

"Wani irin doguwar tsaki Aisha tai hade da cewa dan suce su fasa sae me sae kace shikadae ne autan maza'ni wlh na dauka ma mutuwa ai.

"Dan Allah umma ki daena kuka haka.

"Haba Aisha kinsan abinda kike fadi kuwa? Yaya kike mgn kamar wanda batasan ciwon kantaba.

"A lokacin ne Aisha tai dan guntun kwalla tana fadi to umma ya kikeso nace umma.

"Abbansu dake zaune kasa mgn yai.

"Umma taci gaba da cewa yanzu yaya zamuyi?

"Abba yace nima kaina tunani da yakeyi kenan' wlh hafsatu inda inada wani da zanbashi Aisha kodan na tura masu bakin cikin da suka cusami da jibi zan daurawa Aisha aure.

"Aisha najin haka wani irin dadi ne yakamata.

"Umma tace gaskiya kam' gashi babu wani dake zuwa gun ta banle ace yafito' to koda ma yafito ba lalla bane ya'amince a kwanaki hudu ga da suka rage.

"Aisha naji haka tace idan haka ne Abba ka kwatar da hnklinka insha Allahu bazakaji kunyaba duniya da lahira' idan har ka'amince akwai wani dake zuwa guna zan gwada nagani kodan naga na share maku hawaye.

"Shiru umma tai.

"Abba yace a'a aisha bazanso na takura makiba dan wata biyan bukatarmu' tunda abu yazama haka nabarwa Allah komai Allah yabaki wanda yafishi.

"Umma tace amin alhj.

"Aisha dake duke tace abba kada kadamu zan gwada nagani.

"Abba yace a'a aisha bazanso kiyi auren kiyayyaba nafiso ki auri wanda kikeso.

"Aisha tace karka damu abba.

"Mikewa tai tabar dakin' tana komawa dakinsu ta kira alhj nasir ta sanar dashi gobe yashigo gida.

"Nasir yai murna sosae dajin haka.

"Washe gari yazo gidan su Aisha' bayan sun gaisa da Bbn aisha ya gabatar da kansa kuma yace shi ko yaune idan sun shirya shima a shirye yake.

"Jin hakan abba yai murna sosae hakan yasa sukabar shi a ranar da akasa ita da zahradee.

"Zahradee wasa wasa ko fita baya iya yi' anyi anyi akaisa asibiti amma yaki.

"Ranar asabar aka daura auren aisha da nasir' zahradee najin labari fashewa da kuka yai' hade da yanke jiki yafadi sumanme.

"A gigice abba ya daukesa zuwa asibiti.

"Ana daura aure da safe da yake yan'uwan nasir sunzo' anayi azahar aka basu amarya sbd gari ba daya ba' kuma akwai tazara a tsakaninsu.

"Gani zatabar gida da yan'uwa da iyaye yasa Aisha kuka har ana riketa.

"Kwata kwata mutu 3 kawai Abba yabari suka bita SBD nisan guri.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

MMN USWAN

1⃣9⃣

"Rushing d'insa zuwa hospital' Abba dake rungume dashi a mota in ba addu'a babu abinda yakeyi' idan yai wann baya karisaea yake sakewa ya kamo wani' Shamsudee shike driving gudu yake kamar zaitashi sama.

"Da h'aka har suka isa hospital ko parking kirki basuyi ba Abba ya b'ude mota h'ade da fitowa da zahradee emergency room aka kaisa doctors dasukan duty to sukai can a kansa' kowa na nasa bakin kokarin'abba da Shamsudee da suke waje sae faman leke sukeyi.

" Da taimakon Allah yasa zahradee ya farfado' but still sama sama yake numfashi gani yabude ido yasa doctors d'in juna masa drip gani ya koma wani bcc yasasu fita daga d'akin' suna fita Abba da Shamsudee sukasa kai zasu shiga d'akin' da sauri doctors d'in suka dakatar dasu' h'ade da cewa dan Allah yana cikin critical condition dan h'aka yana bukatar hutu.

"Ido cikin ido suke kallon juna snn Abba ya kamo hannu Shamsudee suka zauna kan kujeran dake gefe d'akin' basu dade da zama ba saega su Hjy da Nurudee sun shigo hospital d'in ganisu da tai zaune a gefen d'akin yasata tambaya lfy?.

" shiru Abba yai mgn ta gagaresa' Shasedee yai masu bayani abinda ake ciki' salati Hjy tasa da salallami.

"Zahradee be falkaba sae gam da magrib snn ya falka Abba kawai yake ambato a bakinsa' da sauri Abba ya mike shida Shamsudee suka shiga d'akin' suma su Hjy suka bisu ciki gani hawayen dake gangaro masa ta gefen ido yasa Abba matsawa gun gadon tissue ya diba yana goge masa haeayen.

" zahradee yace Abba Aisha' Abba Aisha ta cuceni Abba.

"Abba yace son kabar mgnr Aisha d'in nan kaji da kanka son.

" wani muguwar tsaki Hjy tai h'ade da cewa Aisha me? Aishan banza.

"Shamsudee dake gefe yace to kai zahradee idan banda abinka wayasan abinda ya h'ada ku? Banle har a tayaka.

" zahradee yaci gaba da cewa Abba bansan abinda naiwa Aisha ba Abba Aisha ta gujeni Aisha ta daena sona Abba' dan Allah Abba kaje ka dawomin da Aisha wlh Abba inason Aisha Dan Allah Abba.

"Abba dake tsaya kusa dashi tsayawa yai shiru yana kallon zahradee dake kwance' gani shiru da yai yasa zahradee yunkurin mikeww zai tashi' da sari su Shamsudee suka rikeshi suna kokarin medashi ya kwanta' zahradee yace a'a ku barni kawai ni masamu sauki.

" duk zahradee yana mgnr ne amma bedae na kuka ba.
Chapter 20 · 0% Book details