← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 89

Sashe 34

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"amma yace kai fa Nurudee shikuma yace habiba yakeso 'yar gidan Alhj sani shima koda yaje da mgnr aure cewa yai bayaso yaita bawa mutani wahala yafiso ayi gaba daya da sauran yaran gidan wata kanin habiba kenan suma wnn shekarane zasu kare karatu idan su kammala sai ayi mgnr auren kawai tunda gidan mazansu ma har sukai komai.

"to yanzu muma so suke mukai kenan?".

"a'a" Abba kabari dai lkcn yai tuku.

"to kenan amma Dan Allah kuyi kokari sbd banaso wann shekara takare batare da munada mata ba' kuna gani kaniku kenan har zaije ga nabiyu amma Ku dakuke manya ace bakuda ko daya.

"duk dariya sukasa.

"bangare Hjy kuwa sai faman shirye-shirye takeyi babu kama hannu yaro binni da kauye ta aika ba kamar lkcn bikin Aisha ba wanda ma suke binni ba kowane yasani ba banle na kauye.

"anko kuwa anyishi yakai kala biyar ko wacce rana da nata.

"kan Aisha ya daure sbd mafi yawanci lokuta takan sacijin kamar ana mgnr biki k'uma sunar zahrdee ake ambato.

"wani tunani daya zomata tace kodae na tambayesa ne?" can k'uma tace bari kawai na barsa idan yai ra'ayi dan kansa zai sanar dani tunda baya boyemi komai.

"zahrdee be kira Aisha ba saida yarage saura sati biyu bayan ta idar da sallar azahar tana zaune kan sallaya saiga kiran zahrdee yashigo' gani bakon number yasa taki dagawa har wayar ta tsinke.

"har ta mike saega wani kiran yashigo'gani kiran bame karewa bane yasa ta daga danjin wake damuta da kira h'aka.

"tana dagawa da sallama taji duk da bata gane muryaba amma besa taki amsawa ba.

"nasan kina mgnr ne batare da kingane dawa kike mgn ba ko?".

"wlh kuwa"Dan Allah dawa nake mgn ne?"

"zahrdee ne".

"eyya Dan Allah kayi hkr wlh bangane muryanka bane?".

"Eh" nasan da h'aka Ai".

"bayan sun gaisa zahrdee yace dama bugowa nai na tambayeki abinda kike bukata".

"murmushi Zainab tai hade da cewa bani bukatar komai".

"to shikena tunda baki bukatar komai gani number na idan bukatar yataso saiki kirani'idan k'uma kunya kikeji saiki bawa kawayenki nasan bazaki rasasu ba.

"to kawai Zainab tace".

"snn sukai sallama'bayan ya kashe wayar ne Zainab ta zauna shiru tana tunanin wann hali irin na zahrdee.

~~~ ~~~~ ~~~~

"Nasir tunda aka kaiaa Egypt dayake Akwai kwararron docts su bashi kyakykyawar kulawa jiki kam alhadumllh yanzu kusan komai da kansa yakeyi batare da yabawa Fatima wahala ba.

"sae dae docts din suce yana da'kyau yarinka zagawa yana exercise sbd dadewar da yai a kwance.

"Nasir ya samo wnn cutar ne a gun zuwaira daya aure batare daya san tana dauke dashi' ita kanta batasan tana dauke dashi ba sakamakon auren wani mutum da tai shima kusan irinta ne harma zan'iya cewa yafita sbd duk shekara yake zubi' ma'ana kowani shekara yake auren mata hudu kafin wani shekara duk ya sakesu ya dibo wasu.

"shine sanadiyar da yasa zuwaira tasamu wnn cutar' bayan rabuwarsu dashi Nasir ya aureta a nan ne shima ya dauki cutar'abinda yasa ma be cutar dashi h'aka ba Nasir mutum ne me kulawa da kansa wajan shan maguguna.

"ko'a lkcn da yaji canji a jikinsa yaje dan gani doct' doct kamal yace infection ne amma idan yana kulawa da magani babu abinda zaisameshi.

"da h'aka Nasir yaci gaba da kulawa da kansa wajan shan maguguna' inda ya godewa Allah ma jininsa (O) shida Fatima' a nan ne Aisha ta dauki cutar dayake ita jininta bekai nasu karfiba yai affecting dinta har mahaifarta.

"amma ita Fatima ma batasan ana yiba sbd bata dashi' shima Nasir yanzu yasamu sauki sosae' a cewar doct zasu iya komawa gida idan yaso yarinka zuwa chickcup' koda Fatima ta sanarwa abbansa sai yace aa sutsaya yakara samu sauki tuku.

"shima Nasir din gani yasamu sauki yasashi daukar Fatima suna yawo sauran kasashe suna shan iska..

~~~ ~~~ ~~~~

gida yashake fal da jama'a na binni dana kauye har babu masaka tsinke.

"bagaren maza kuwa duk sun shirya zuwa daurin aure.

"jikin Aisha yai sanyi sosae sbd duk halimu ya nuna mata zahrdee ke aure'amma wani abu daya daure mata kai ko jiya tare suka kwana dashi amma bece mata komai ba.

"daki takoma ta zauna bakin gado hawaye ne kawai takeyi wani nabin wani.

"gidan su Zainab ma duk sun shirya daurin aure gidan su zahrdee kawai ake jira.

"zahrdee Shamsudee nurudee duk kaya irin daya sukasa sbd Abba ne ya dinka masu sai dai na zahrdee da malum-malum ne' duk su uku suka shigo cikin gidan abokiyar wasansune mai suna Hajjo ta rangada guda hade da cewa zahrdee ango' kaga ta inda kafi yayyinka kenan har kakaiga mata biyu ga yayyinka marasa zcy dayan ma ya gagaresu.

"Aisha dake daki tanajin h'aka tafashe da kuka ashe dama zhrdee zai'iya yaudarata h'aka zai'iya cin amanata h'aka ya boyemi mgnr aurensa.

"fadawa tai a gado taci gaba da kukanta.

"around ten O'Clock shap aka daura auren zainab da zhrdee.

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.

(IMPACTING VALUABLE KNOWLEDGE AND ENTERTAINMENT IS OUR CINCERN)

STORY WRITENNG
BY
MMN USWA

SAKON GAISUWATA GAREKI SISTER MARYAM A.I. GITAL WLH INA YINKI SAHEBATA BABU ABINDA YA SAUYA ALLAH YA BARMI KE HAR ABADA TARE DA LAFIYA MAI DOREWA AMEEN INA YINKI TAWA UP UP UP DA YARDAN ALLAH.

3⃣2⃣

"ana gama daurin aure sukayo gida.

"ko kafin su dawo anriga an shirya walima'suna isowa aka fara walima.

"ango zahrdee yasha wa'azi sosae hade da fatan Allah yabashi ikon adalci a tsakanisu.

"bayan la'asar gidan amarya sukakai kaya daya daga cikin gidajen da Abba ya gina ne bangaren da tun farko Abba ya gina masa a nan ne Zainab zata zauna.

"tunda bayan dauri aure zahrdee yaso kiran Aisha kodan yai mata bayani amma besan ta inda zaifara ba.

"sbd shima kansa yasan be'kyauta ba kamata yai tun kafi lkc yai tasani tunda gaba daya gidan babu wanda ya sanar da'ita' k'uma koba h'aka ba shine ya kamata ya sanar d'aita tunda zamansa takeyi amma be sanar d'aita ba sbd yana gudun bacin ranta.

"shiru kawai yai yana tunani sbd besan wani Aisha take ciki ba a wnn lkc' gani duk irin tunane-tunane ga bazai kaisa ba wayarsa ya ciro daga aljihu yai dialling number Aisha zahrdee yayi kira yakai eight miss call Aisha na kallo amma batai picking ba' gani zaidameta takashe wayar daya baya.

"jin takashe wayar hnklin zahrdee yakai matuka gurin tashi' kai kawai yasa yashige cikin gida Allah yasa snn babu wasu mutani ta bangarensa hakan yasashi samu damar shigewa dakinsu hade da sa key yarufe dakin.

"yana shiga gani Aisha yai kwance sharbe-sharbe a kan gado kamar wanda akaiwa duka' da sauri ya karisa kan gadon h'ade da sa hannu ya dagota jikinshi yana cewa Dan Allah Aisha kiyi hkr ki yafemi' nasan nayi maki laifi amma Dan Allah kiyi hkr wlh ba laifi bane nima kaina bansan mgnr wnn auren ba wlh Aisha.

"fisge jikinta tai daga nasa' katashi ka bani gu zahrdee banaso ganika Dan Allah kafita kawai zahrdee' zahrdee banasonka banason ganika zahrdee katafi gun amaryanka kawai.

"haba Aisha wacce irin mgn kikeyi h'aka? wlh babu inda zani inanan tare dake Aisha ta..

"zahrdee kafita min a daki".

"babu inda zani".

"kafita min a dakina".

"wlh babu inda zani' sai dai duk abinda zakimi kiyi amma wlh ina tare dake.

"hannu zahrdee yakai zai rikota'juyawar da zatayi tasa ta igijeshi ya f'adi ta baya a kasa a guje Aisha ta sauka dan dagoshi.

"hannu tasa ta taimaka masa ya mike yana tashi tajada baya' binta yai da karfi ya riketa yana f'adin Dan Allah Aisha ki saurareni kiji mgnr da zanfadi maki Aisha.

"cikin galatse tace ina sauraronka.

"dukawa yai a gaba rike da hannayenta bibbiyu' snn yace Dan Allah Aisha Dan annabi ki saurari abinda zanfadi maki' wlh Aisha anyi aurenga ne kawai amma wlh kwata-kwata bada amincewa ta bane' su Abba da Hjy ne suka shirya h'aka amma na rantse maki da Allah Aisha bana sonta ko kadan wlh Aisha kece nakeso dake ne zcyta take rayuwa.

"nasan ba lalla bane idan na f'adi maki ki yarda ba amma wlh wlh Aisha tunda nake a rayuwata ban taba jin dindinon son wata mace ba bayan ke' Aisha kece rayuwata da sonki nake kwana nake tashi' idan har kika koreni kika rabani dake bansan inda zansa kaina ba' k'uma koba komai kinga kibawa duniya kofar shigowa rayuwarmu kenan su tarwatsa zaman damuke dake.

"Dan Allah kiyi hkr ki rungumi wnn aure a matsayin kaddara' ni zahrdee nayi maki alkawarin bazan taba canza makiba ko dede da kwayar zarra.

"idan ma banda abinki Aisha wlh bafa sonta nakeyi ba' kece kekadai tawa na mallaka maki kaina halak malak.

"murmushi kawai tai.

"hannu tasa ta dagosa sama' gani h'aka yasa zhrdee rungumarta.

"around 8-30 yyar Hjy da kanwar Abba da sauran da baza'a rasaba suka tafi dauko amarya.

"motocine lafiyayyu guda biyar masu bakike glass suna biye da juna' koda suka isa inna Hulairane da sauran jama'a suka taresu cikin girmamawa bayan sun gaisa batare da bata lkc ba aka fito da amarya' Kai tsaye bakin abbanta aka kaita yai mata nasiha sosae snn yabasu ita hade da cewa beyarda kowa ya kwana a gidan ba' ana kaita adawo.

"duk suka amsa tare da godiya' snn yace wa Hulaira ta kira masa Hjy umman Zainab tana zuwa yace ko kinada abin cewa?"

"a'a" alhjy Allah ubangiji ya basu zaman lfy?'.

"amin" kefa Hulaira?".

"a'a" Alhj duk abinda zamuce kariga da kafadi' mudai fatanmu Allah ya hada kansu ita da abokiyar zamanta.

"amin' tashi kuje".

"a lkcn ne Zainab tasa kuka' hade da kiran inna Hulaira.

"da sauri Hjy tabar dakin sbd hawayen da suke zabo mata.

"ana daukar amarya kai tsaye sai gidan su zhrdee' har dakin Hjy aka kaita snn aka tuwa daya daga cikin bakin da sukazo baki ta kira Aisha.

"koda yar'aike taje bakin kofa tanata sallama babu wanda ya amsa mata sakamakon Nisan da sukayi.

"Aisha naji tayi kokarin ture zhrdee dan tasamu mikewa amma ina zhrdee ya hanata dole yasa ta hkr.
Chapter 34 · 0% Book details