← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 89

Sashe 49

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"wani prvt hospital zhrdee yakai Aisha sukaga doct maguguna aka basu' zhrdee basu dawo g'ida ba saida yabiya da'ita ya siye mata yoghurt da gasashiyar kaza snn suka dawo g'ida' kai tsaye dakinta suka shiga bayan ya tube itama ya tubeta ya daura mata zani har da kamata yai snn ta zauna da kansa yake bata namar abaki h'ade da yoghurt tana ci tana shagwaba' sai faman sannu yake cetama' bayan ta ko shine ya dauko ledar magani ya cire ya bata tasha' ta nasha tace bcc takeji' da kansa ya kamata ya kwantar da'ita' shima kwanciya yai kusa da'ita yana rungume da'ita'. juyi kadan tai saiyace sannu"

"shiru2 Zainab nasa idon zuwan zhrdee amma shiru' ji takeyi kamar tatashi taje ta kirashi ko tasanar dashi halin da take ciki amma gudu kada Aisha taga gazawarta yasa ta dan ne' taci gaba da nakudar da bana haihuwaba' tubewa tai tarage daga ita sai zani ko pan bata bari ba' kuka kuwa ba'a mgn"

"da yaudara Aisha tai ta jan zhrdee har suka kusan kwana tare'dan zhrdee bekoma dakin Zainab ba sai asuba lkcn anfara kiran sallah snn yakoma d'akin' ko kafin snn ma ciwon ya f'ada mata' yana shiga yaganta kwance a kasa kamar me bcc amma ba bcc takeyi ba"

"be tanka mata ba gado ya h'au y kwanta yana jiran lkcn tafiya masallaci yai' kama katakwan gado Zainab tai ta mike Zainab h'ade da cewa sai yanzu kaga damar dawowa?"

"eh yanzu gani damar dawowa"

"amma kasan a nan kakek?"

"sai me idan anan nake"

"nidai ba wnn ba wlh zhrdee banida lfy ko bcc ban'iya ba sbd ciwon ciki kamar wanda zan haihu"

"to meya hanaki haihuwar idan da gske ne'

" da gske fa"

"ke kinga alamar wasa a idona?'

" zhrdee ".

" meye ne?"

"to wlh da safe babu abinda zai hanani fadiwa Hjy' k'uma Allah ya'isa kwanar dakai a dakinta"

"dama Allah isashene ai' ni wlh baki birgejiba tunda bazakije yanzu ki f'ada mata ba"

"Allah ya'isa mugu alzalumi kawai' kuka Zainab tasa"

"sbd kada ta damesa pilo yasa ya tushe kunninsa"

"zahradee yana fita masallaci Zainab ta sabi hijab d'in ta zuwa g'idan su".

📖🖊
☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITERS F.O.W.☘.

🌳impacting valuable knowledge and entertainment is our concern🌳

story written by Mmn uswan

4⃣0⃣

"Zainab na fita takami hanyar g'idan su' tayi tafiya sosae dan tai nisa da g'ida' yawanci masallatai su idar da sallah' zhrdee ma yadawo g'ida d'akin Aisha ya shiga ya sameta ta idar da sallah' tana tafe a hankali sbd ta gaji da tafiya gashi gari be wayeba banle ta h'au napep k'uma kodama tasamu napep d'in batada ko sisi a hannunta"

"tsayuwa tai tai shiru tana tunani kala2 a zcyrta wata zcyr tace jeki kawai wata k'uma tace a'a Zainab idan har kikabar g'idan sbd Aisha shikenan zata rainaki' zatace kin tsorata da'ita gara ki koma kawai' kuma idan ma kikaje g'ida Abba bazai bari ki zauna ba' dawowa dake za'ayi kinga koba komai Aisha tasamu na gari' tsayuwa tai tai shiru' a pili k'uma tace kaeeee Aisha wlh kinyi kadan nabar g'idan sbd ke a fusace ta juya takami hanyar g'ida"

"kafin Zainab ta'isa g'ida gari ya waye tangaran'tana shiga zhrdee yana fita daga d'akin Aisha'gani Zainab ta shigo da sauri yace daga ina? banza tai dashi ta shige' da sauri ya bita Zainab badake nakeyi ba? tana shiga d'akin shima ya shiga h'ade da rike mata hannu yana f'adin ba dake nakeyi ba Zainab"

Zainab ta fisge hannunta' shigewa tai zata kwanta fisgota yai yana f'adin badake nakeyi ba Zainab' fita nayi"

"kika fita zuwa ina? k'uma da iziniwa?

" bansani ba"

"a fusace zhrdee ya shakota da iziniwa kika fita Zainab' Zainab tai shiru' ba dake nakeyi ba' Zainab babu amsa sbd irin shakan da tai mata k'uma ga dukani alama yanzu yai fushiga koma menene zai iya yimata na rantse da Allah idan kika kara fita koda nai da kofar g'ida ne duk abinda nayi maki ke kikaja' zhrdee ya karisa mgnr ne h'ade da igijeta gefe f'adi tai a kasa tasa kuka' toilet yashiga yai wanka be tsaya breakfast ba ya shirya ya fita kasuwa" da Zainab tai kukanta ta gaji' da taga kukan bazai fisheta ba sbd yunwa da takeji' mikewa tai tanufi kitchen taje h'ada abin karyawa arish ta dauko tana ferewa saiga Aisha ta shigo kitchen d'in' itama dibawa tai tana ferewa kowa na aikinsane babu wanda ya tankawa d'an uwansa Zainab ce tariga Aisha gamawa sai ta kunna gas ta dora mai' itama aisha mikewa tai ta kuna dayan gas d'in ta dora mai snn taje taci gaba da yayyankawa kananu mai yai zafi sosae snn tazuba a wuta' mai ya dunga tsalle yana dallan Zainab a hannu' Zainab ba hkr tace kiga gani ko?"

"banza da'ita Aisha tai' daga snn Zainab bata sake tanka mata ba' dauko abinda take juya arish dashi ta tsuma a cikin mai snn ta yarfewa Aisha a hannu' a gigice tace h'aba Zainab baki ganine?"

"Ashe kina mgn? na dauka da kurma nake tare"

"a'a tsaya nema"

"ke zakiga tsaya' tsaya k'uma yabiki"

"wlh Zainab kyaleki nakeyi fa"

"idan baki kyaleniba me zakimin?"

"koda yake be kamata na biyeki ba' ko bakin cikin dana barki dashi na jiyama kawai ya'isheki' kinaji kina gani na hanasa kwana a d'akin ki sbd na isa"

"duk da mgnr yaiwa Zainab zafi amma ta matse tai dariya h'ade da shewa snn tana Allah sarki Aisha d'an bakisan mgnr da zhrdee yakeyi akanki bane yasa h'aka ni wlh har tausayi ma kike bani"

"cikin kosawa h'ade da faskewa tace sai me? banle ma nasan duk abinda zhrdee zai f'adi akaina saidai yabo' ba irin su oh oh ba wanda ba'asan darajansu ba"

"ni wlh Aisha ma mmki kike bani idan banda rashin kangado irin naki ni har zanyi fariya da tuniya dan miji ya kwana a dakina' mutumi dayace yana dai tarawa dake ne kawai amma badan dadi ba'idan zaki lura duk ranar girkina har dawowa yakeyi da rana amma kefa idan yaje yaje kenan"

"Aisha taji zafin mgnr sosae amma matsewa tai tace sae me? wlh sbd rashin dadina ko yana kuka ne sai yayi" dariya Zainab tai h'ade da cewa tana f'adin Allah sarki Aisha"

"Zainab ai kece abin Allah sarki' kije ki tambyi kowa irin soyayyar da zhrdee yakemi' sbd ni har kwanciya hospital saida yai' ba kamar ke da'aka cusa masa ba"

"shi zhrdee d'in ne ya f'adi maki h'aka"

"ohh! ho!" nidai nasan ba karya nayiba "

"da haushi yakama Zainab cewa da h'aka dai gashi zan bashi abinda kika gagara"

"me kenan"

"baby' ko karya nayi banza kwanko kawai' juya"..

"kafin Zainab ta karisa Aisha ta dauketa da mari h'ade da ihu"

"daidai lkcn Hjy na fitowa jin ihu Zainab yasa ta kariso da sauri h'ade da tambyar lfy?"

"gani Hjy yasa Zainab cewa dama santsine nayi zan f'adi shine nayi ihu".

" garin yaya?

"h'aka kawai Aisha ta taimakami ta rikeni"

"a'a to Dan Allah kirinka ki yayewa' kinga bake kadaice bako"

"Dan Allah ki kiyaye banason abinda zaije ya dawo"

"to zan kiyaye"

"Aisha na tsaye tana kallonsu' Hjy na fita Zainab ta kwashe da dariya".

"da yamma zhrdee yana dawowa ya siyewa Aisha wata sabuwar waya wacce tafi nada tsada da'kyau"

"Aisha bajewa tai tai murna sosae hade da nunawa zhrdee soyayya' yau ko leka Zainab beyiba yananan like da Aisha tana kwance yana zaune a batanta suna hira yana matse mata jiki a hankali Aisha tace my baby"

"na'am you a lone,

" Dan Allah gobe inaso naje uguwa"

"uguwa kuma"s sweedy?"

"OK zakije dubomi ummata ne?"

"a'a gun ubaida zaki"

"ubaida k'uma?"

"ubaida tafi umma kenan?"

"a'a ba haka bane"

"to menene"

"just" himmm"

"just what dear?"

"idan bazakije gun umma ba babu inda zaki"

"to naji zanje"

"Zainab zama tai tana jiran zhrdee ya shigo amma shiru' ita kenan har shabiyun dare tana zaman jiransa amma be shigoba' ga yadda takeji a jikinta babu dadi kwanta2 zama tai taci kukanta sosae"

"shiko zhrdee suna can suna holarwarsu da Aisha' kwata2 yamance da mgnr Zainab harda guje guje sukeyi suna zagaje daki ita dashi"

"da asuba suna tashi zhrdee yatada Aisha yana rungume da'ita suka shiga toilet sukai wanka snn sukai sallar asuba' suna idarwa yaje ya gaida Hjy da Abba"

"yana fita yaje d'akin zainab lkcn tana kwance takasa tashi dan ko sallar asuba batai ba' yana shiga a b'akin gado ya tsaya h'ada da cewa kintashi lfy?"

"lfy klau"

"iya kacin abinda yace kenan ya juya zai fita"

"Zainab tace zhrdee"

"meye ne?"

"tsayuwa yai a tsakiyar daki yace ina jinki"

"rarrafawa tai ta sauko sako daga gadon gabansa tazo ta duka har kasa gwiwa bibbiyu tana dafe da kafarsa hawaye ne kawai ke zuba tace Dan Allah Dan annabi ka taimakeni ka kaini hospital wlh banida lfy"

"Zainab kenan aini bance bazan kaiki hospital ba' amma idan kinaso na kaiki sai kinje kinbawa Aisha hkr akan abinda kikai mata"

"cikin kuka Zainab tace h'aba zhrdee kasan abinda kake f'adi kuwa? Aisha fa kace?"

"kwanta da gske"

"a gskya bazan iyaba naje nabawa kishiya hkr"

"OK ban'isa dake ba kenan?"

"ka'isa amma kasan ba abinda yakamata kayi ba kenan ko' idan har sukai laifi kamata yai kahadamu dukkanmu mu biyu kai mana f'ada idan ma na hukunci ne kai mana amma ba kazabi daya daga ciki karinka fifitawa bako?"

"wah!! na fifita a tsakaniku?"

"kafin kowa sani"

"zhrdee nasan duk wnn abubuwan kanayimine sbd kana gadaran iyayenka ne suka haadamu badan kaine kagani kace kanasoba kamar Aisha shiyasa duk kakemi wnn abubuwa' amma abu daya da nakeso ka gane shiga koda h'akan be faruba idan har Allah ya rubuta saika aureni wlh baka'isa ka kaucewa tsarin ubangiji ba' nima k'uma kaina da nasan basona kakeyi ba wlh da ban'amice ba'amma babu komai h'aka Allah ya kaddaromi"

"a lkcn jikin zhrdee yai sanyi sosae' yace Zainab waya f'adi maki bani soki?"

"cikin kuka tace h'aka ne mana' bagashi har f'adi wa Aisha kakeyi ba"

"shiru yai sbd yasan mgnrta gskya ne"

"nidai dan Allah Dan soyayyar da kakewa iyayenka Dan albarkaci d'an ka dake cikina ka taimakeni ka kaini hospital"
Chapter 49 · 0% Book details