← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 89

Sashe 65

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"zhrdee da asuba lkcn ya shiga gaida Hjy bayan su gaisa ne Hjy ke cewa Zainab ta kirani mu gaisa"...

" da sauri zhrdee yace nima ta kirani ai"

"Allah sarki' to Allah ya taimaka"

"amin Hjy"

"har zhrdee ya mike Hjy tace zhrdee"

"na'am Hjy"

"dan Allah koda zuwa gobe ne idan kasamu lkc kaje ka dubo yaran nan kaji"

"yara k'uma?"

"eh mana"

"to shikenan Hjy Allah ya kaimu"

"amin' amma dan Allah idan zaka kadan rike masu koda sweet ne kaji"

"naji Hjy"

"bayan ya fitane yana shiga d'akin Aisha yace Aisha"

"na'am"

"ashe bakuwar number da aketa kirana dashi Zainab ce"

"kallon banza tai masa h'ade da cewa toni ina ruwana"

"lkcn zhrdee ya riga ya juya baya' Allah sarki Zainab kawai yace"

"Aisha tai banza dashi"

"duk da Allah sarkin dayace besa zhrdee tunanin kiran Zainab ba"

"itama da take can tunda bata sake kiran zhrdee ba sbd tana gani koda ta kirasa ba lalla bane ya daga' shiyasa Hjy kawai take kira su gaisa"

"tunda Zainab ta sauka a kasa me sarki duk inda taje ibada babu abinda takeyi sai addu'a akan Allah ya dorata akan maigidanta ya sanya masa soyayyar ta a zcyrsa"

*bayan kwana biyu da tafiyar Zainab Hjy tace zhrdee ya kaita g'idan su Zainab' a take gaban zhrdee ya f'adi sbd tunda Zainab tabar kasan be taba lekasu ba balle yasan halin da suke ciki"

"bayan Hjy ta shirya ta fito parlour su Aisha h'ade da kwadawa zhrdee kira' Aisha najin kiran Hjy ne yasata fitowa har kasa ta duka suka gaisa' Hjy tace Aisha' manyan gari kodan lekowa ciki bakyayi' idan kinajin kunyar hira dani baga kanni mijinki nan ba' amma sai kiyita zama a daki kekadai".

" karaf zhrdee yace wlh Hjy nima kullum abinda nake f'adi mata kenan' amma bataji"

"kila zaman gu daya baya damukine yasa h'aka"

"murmushi kawai Aisha tai h'ade da shigewa d'akin ta' suma su Hjy ficewarsu sukai"

"suna fita Hjy tace sai su biya kasuwa tai masu siyayya snn su karisa g'idan"

"wani supermarket ya kaisu Hjy da kanta take zaban abinda takeso' wanda tasan yara zasuyi sha'awa"

"kaya sosai ta diba snn zhrdee ya biya suka shiga mota zuwa g'idan su Zainab"

"suna isa har cikin g'idan zhrdee ya shiga yai parking snn suka fita' Hjy tace zhrdee ya dauko kayan' tana gaba yana biye da'ita a baya suka shiga har parlour h'ade da sallama"

"jin sallama ne yasa Hjy *maryam* mmn Zainab fitowa gani zhrdee da Hjy ne yasata komawa da sauri taje ta fadiwa inna *Hulaira* inna da fara'arta ta fito ta tarbesu"

" *Hjy maryam* hijab tasa snn ta fito suka gaisa snn ta koma ciki d'akin ta' inna ce taje ta kawo masu ruwa da abinda h'ade da su juice' snn takoma ta dauko yara suka fito tare' *Akbar* yana gani Hjy a guje yaje ya rungumeta itako *lslaha* gun zhrdee tanufa"

"Inna na gani h'aka ta mikawa zhrdee *Islaha* cikin jin kunya zhrdee ya amshi *Islaha* yana murmushi"

"itama Hjy daukar *Akbar* tai tana masa wasa"

"sun jima su hira snn Hjy tace zasu tafi' dauke *Akbar* tai itako *Islaha* gani zhrdee yanada niyar dauketa kuka tasa h'ade da makalewa a jikin bbnta"

"duk dariya sukasa shiko zhrdee dake dauko da'ita kunya ne ya kamasa' sbd kunya kasa mgn yai sai faman murmushi kawai yakeyi' gani ta kara makalewa a jikinshi h'ade da rike masa riga hannu bibbiyu tana kuka"

"banbareta yai daga jikinsa ya mikawa Hjy snn yafita' duk dariya sukasa' itama Hjy mikewa tai h'ade da mikawa inna ita snn sukai sallama' *Akbar* dake tsaye dagawa Hjy hannu yakeyi alama sallama"

"suna tafe Hjy tacewa zhrdee Allah sarki tsakani dah da mahaifi kenan"..

" menene k'uma Hjy"

"wlh wani irin naji da yaringa ke kuka' kodai mukoma mu daukota ne?"

"shiru zhrdee yai be tanka ba"

"zhrdee ko baka jina ne?"

"dauko wani zance yai"

"daga nan Hjy ta gano kunya ne yakeji irin na Hausa Fulani"

*dama duk wanda yasan Hausa Fulani an sansu da kara da kunya h'ade da girmama na gaba dashi*

itama data gano h'aka bata sake mgnr ba har suka isa g'ida'sai wani hiran suka dauko"

"ranar da Zainab zasuyi hawan arfa' tana tsaye a gaban ka'aba daga hannunta tai sama hannu bibbiyu tace *ya Allah ga baiwarka nan tazo da kokon baranta' Allah kafi kowa sani halin da nake ciki a g'idan aurena' Allah kai ka halitceni kafi kowa sani damuwata' ya ubangiji Allah dan tsarkin mulkinka' dan kadaitarka' dan tsarkakanken littafinka wato alkur'ani mai tsarki' dan fayayyan halittarka' shugabanmu annabi muhammedu (S.A.W.) Allah ina rokon ka kada dorani bisa kan mijina' kasanya masa soyayyata nida yarana a zcyrsa' Allah kada kabashi ikon walakantani' bashi bama duk wani abin halitta' ya Allah ka dorani bisa kan kishiyata, ni k'uma ya ubangiji Allah kabani hakuri da juriya a tsakani zamantakewar cikin g'idan aure na' kabani hakuri da juriya akan duk wani abu da zangani a gun maigidana, Allah kafi kowa sani ina cikin jarabawa a zaman aure na' Allah kabani hakuri da juriya akan h'aka' Allah ka ganar da mijina,3 ka k'uma shiryarmin da yarana shirin addini musulumci*

*Allah nayi tawassali da sunayenka tsarkaka' Allahu' arrahaman' almuminu' almihaiminu' alkundusu'' Innamaza amru iza aradda lahu an yakuluna lahun kumfa yakun*

snn Zainab ta shafawa' ko a madina masallaci annabi Muhammad (A.S.W.) nan ma taita addu'a akan niman zaman lfy tsakani ta da zhrdee da k'uma Aisha"

"bayan kwana biyu da tafiyar su Aisha hospital ta samu ciki wanda ita kanta batasan ta samuba sbd bataji kowani halimu ba' sai dai yawan tsardan da miyau da takeyi' dayake zhrdee bayaso sbd kyama h'akan yakeji yasashi yimata f'ada akan bayaso' tayi kokarin dai nawa amma abu ya gagara gani h'aka yasashi cewa suje hospital' gwajin farko doct ya gano ciki ne da'ita na sati biyu zuwa uku' koda aka fadiwa zhrdee murna yai sosai daga shi har Aisha"

"tun daga lkcn ya daina matsa mata' aikin komai ma ya hanatayi a g'idan"

"tunda Zainab ta tafi zhrdee be kirataba' itama tunda ta kirasa be daga wayar ba yasa bata sake kiransa ba"

"sai yau kamar wanda akaiwa asiri yaji yanaso yaji koda muryanta ne' bayan ya fita kasuwa yai rechaging sosai ya kira Zainab' gani number zhrdee yasata mmki' da sauri ta daga sbd kada ya tsinke' da sallama ta daga"

"zhrdee yace hjyta ina fatan kina lfy?' k'uma da fatan bakiyi fushi dani ba"

"dariya Zainab tai h'ade da cewa fushi me idan da sabo ai nasaba"

"kamar yaya Zainab dinta?"

"a'a babu komai"

"idan ma kiyi fushi ne to dan Allah kiyi hakuri"

"a'a wlh ni na'isa nayi fushi da maigidana"

"dariya Zainab yai h'ade da cewa Allah ko Zainab din ta"

"itama dariya tai snn tace yanzu kana lafiya ya g'ida dasu Aisha da k'uma kasuwa"

"duk alhamdllh"

"ina fatan kimi addu'a ko?"

"wace ni' ni na'isa ace naje kasa me tsarki sukutun banwa mijina addu'a ba?' ai dana dawo kai a kafata"

"da gske Zainab"

"Allah kuwa ai kafi da h'aka"

"kaee naji dadi sosai Zainab dita' Allah ubangiji ya kara maki hakurin nan dana sanki dashi"

"dariya kawai Zainab tai"

"yanzu dai nasan kun kammala aiki wani lkc ne zaku dawo?"

"lahh!!! yanzu da haka ma a layi muke"

"da gske Zainab"

"wlh kuwa"

"kice yau ko gibe zanga amaryata"

"dariya Zainab ta sake yi masa"

"yanzu me kikeso ayi maki"

komai ma Zainab"

"nidai bana bukatar komai' abu daya kawai nake bukata a gunka"

"kaimi addu'a Allah yakawomu lfy"...

"in Allah ya yarda ma zaku dawo lfy Zainab"

"Allah yasa h'aka"

"amin Zainab dita"

"to shikenan yanzu sai kin dawo ko"

"to ngd"

*I lov u*

*lov too*

"snn sukai sallama' suna sallama mikewa zhrdee yai h'ade da daukar key' mota ya shiga zuwa g'ida"

"yana shiga kai tsaye dakin Zainab yaje yasa key ya b'ude d'akin' tubewa yai daga shi sai gajoran wando gaba daya ya kwabe mata kayan daki ya h'au mata kwalima' lungu da sako saida ya shire snn yq canza mata gado ya koma dashi wani gefe h'ade da mirrow"

"Aisha na ciki tana bcc jin motsi yai yawane yasata lekowa taga waye' gani zhrdee ne ke kwalima yasata komawa taci gaba da kwanciyarta"

"zhrdee saida ya gyara ko'ina snn yai wanka ya kwanta sbd gajiya"

"washe gari da asuba saiga kiran Zainab' a birkice ya falka dubawan da zaiyi yaga number Zainab ce da sauri ya daga h'ade da cewa har ku iso ne?"

"Zainab tace eh"

"to ganinan zuwa"

"to kawai tace"

"Aisha naji taja wata uwar tsaki h'ade da juya masa baya"

"ko kafin zhrdee ya'isa tuni abbanta da inna suna gun' amma Zainab tace bazata bisuba zhrdee take jira"

"abbanta be nuna damuwa ba yace babu komai"

"zahradee yana isa can nisa ya hangosu a guje yaje ya rungume Zainab a jikinsa yana murna"

"itama murna tai sosai h'ade da jin dadi yadda mijinta ya nuna damuwa a kanta"

"zhrdee yana rike da hannunta sukaje suka shiga mota"

"shima Abba da inna nasu motar suka shiga"

"zhrdee cike da doki da murnar gani matarsa tadawo lfy' baki har kuni yake kallonta' itama nuna nata irin farin ciki takeyi har suka isa g'ida".

📖✍
☘☘


*AURE IBADA NE*

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘.

🌳 *impacting valuable knowledge and entertainment is our concern* 🌳

*story written by Mmn uswan*

5⃣1⃣

"zhrdee suna isa g'ida tun daga b'akin kofar shiga parlour yake kwadawa Aisha kira' Aisha najin muryar zhrdee da sauri ta mike zuwa b'akin kofa' ganisa rike da kaya Zainab na bayan sa yasata jan tsaki ta koma ciki tai kwanciyarta' karisaw ciki yai zuwa d'akin Zainab' saida ya ije kayan dake hannunsa snn ya b'ude kofa suka shiga ciki"

"suna shiga cikin d'akin Zainab ta zauna h'ade da cewa wash Allah na' snn Zainab yace snn ya'ije kayan dake hannunsa fita yai zuwa kitchen yaje ya dauko mata ruwa da juice' ko kafin ya dawo Hjy ta shigo d'akin' jin muryan Hjy ne yasa Aisha fitowa zuwa d'akin"
Chapter 65 · 0% Book details