← Book details Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 89

Sashe 1

Aure Ibada Ne Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Copied By
YAYA HAYAT
(admin
Hayat hausa novels
Hausa novels and fashion
Cool novel, makeup and kitchen1⃣
AND
Cool novel, makeup and kitchen2⃣)

☘☘


AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.☘

TRUE LIFE STORY

ABIN LURA

Yana da kyau mu kula mu gane cewa munufar yin rubutu ko karatun kanshi ba wai don nishadi bane kawai ko rage lokaci, a'a, muna yine don fahimtarwa da wa'azantarwa ta hanyar nishadantawa don muyi gyara kan kurakiran da muke aikatawa.

Misalin a lokutan da yawa mukan dauki aure wani abin da ake yin shine don a samu dadi a cikin shi, in dai ba kuskuren fahimta nayi ba wannan shine burin yawancin mata har ma da wasu mazan akan aurarrakinsu, har ma auren da yawa kan kasa kai kabari a dalilin an kasa samun abin da za'ayi zaton samu tun farko.

Don haka naga bari mu tunatar da juna don mu kara fahimtar menene AURE?

Farko dai dukanmu mun sani mu kuma yarda cewa, shi aure IBADA NE, haka nan mun yarda shi aure raya sunna ne na manzo rahma ( S.A.W.) daga yin shine kuma zamu mallaki rabin addininmu, ma'ana duk kokarinka akan aiyukan ibada matukar baka da aure, to ladanka rabin na mai aure ne. Ina gani daga wannan kawai ya'isa mu fahimci cewar, akwai wani babban al'amari mai wahala gaske a cikin shi.

Kamar misali biyayya mai karfi da aka sanya tsakanin mu da mazajenmu, mafi yawancin mazajen namu bass mu'amala damu irin mu'amalar da za ta sanya muji saukin yi musu wannan biyayyar, domin basa bamu 'yancin da shari'a ta bamu, basa yi mana adalci da manzon rahma yayi musu wasiyya da suyi mana SBA tsabar son zuciya irin tasu da sonkai.

Muna mata munada namu komisino din Allah ya ganar damu amin.

JINJINA

Ga dukkan wani wanda Allah ya jarabta ya kuma yi hakuri da jarabawar da Allah yayi masa, hakuri kyau.

SADAUKARWA

Sadaukarwa wannan littafi ta tabbata ga dukkan matan da suke aure suke kuma hakuri da abinda Allah ya kaddara musu a gidajen mazansu, Allah ya kara mana hakuri da kuma jin tsoronsa Amin.

GAISUWA MAI TARIN YAWA GAREKI HJY ZABBA'U BUKUR PARCK JOS PLATAEA STATE

Bazan mance dake ba uwar daki ta gari Allah ya kara girma da daukaka yaiwa dukiya albarka amin

0⃣1⃣

"Zauna take cikin dankararriyar parlour wanda yasha kayan alatu a jin dadin rayuwa' tasha kyau har tagaji cikin foguwar rigar shadda wanda yasha aikin sama mai ruwan kore.

"Bini saeta kalli window dan ta kagu taga mijinta ya shigo' da taji shiru mikewa tai taje gidin window ta yaye labulaiyar da yake jikin bango ta tsaya shiru batafi mintuna da tsayuwa ba saega shigowar sa da sauri taje ta yanayin parking ta bude masa mirfin mota.

"Yana fita da rungumesa hade da yi masa sannu da xuwa.

"Murmushi yai hade da cewa yauwa Aisha ta'ya gida?".

"Tace alhamdllh.

"Suna tafe tana gaba yana biye da'ita suka shiga ciki kai tsaye dakinta suka shiga tana ije handbag dinsa ta shige toilet ta hada masa ruwan wanka snn tafito bedroom ta sameshi zaune a bakin gado.

"Dukawa tai ta tana tayashi cire takalmin kafarsa shima hannu yasa yana cire botir din wiyar riganshi.

"Mikewa tai ta dauko masa towel ta mike masa ya yana daurawa yashiga wanka kafin yafito taje kitchen ta kwanso abinci takai masa dinning ta jere masa.

"Yana fitowa jallabiyarsa yasa yafito parlour gani bata gun dinning ya nufa kai tsaye daga ido da zatayi taga yana xuwa da sauri ta saki abinda takeyi taje ta gyara masa kujera ya zauna hade da cewa har ka fito.

"Murmushi yai hade da cewa nafito Aisha ta sannu da aiki' kedae baki gajiya da yimin hidima.

"Murmushi kawai tai masa plate ta dauko tafara xuba masa abinci' gani hannunta na rawa sbd nawin plate din da sauri ya tanlafo hade da yimata dariya yana fadin kinga abinda nake fadi ko?

"Tace na mefa Yallabai?" Yace na rashin cikin abinci mana.

"Murmushi Aisha tai hade da cewa to ai bacin abinci be kesa kiba ba' gaba daya hannayesa ya hada ya tablafo habansa dashi ya xuba mata ido ko kibtawa ba yayi yace to menene?".

"Tace nifa haka Allah yayini...

Da sauri ya tareta da cewa ai banace ba haka Allah yayi kiba nima kaina nafi sonki a haka kodan naji dadin sarrafaki yadda nakeso.

"Da sauri tasa hannu ta rufe fuskanta sbd kunya.

"Jawo plate din abinci yayi ya fara ci hade da cewa xubamin ruwa.

"Daukar jug din ruwan tai ta xuba masa yanaci suna hira har yagama snn ya mike hade da cewa biyoni inada mgn dake.

"To kawai tace tamike ta bishi tana gaba yana baya suka shige dakin ta.

"Bakin gado ya zauna' gani ta tsaya a tsaye jingine da bango yasashi cewa ki zauna mana.

"Snn ta samu gu ta zauna a kasa hade da nade kafa tana fuskantarsa saeda yasake kallonta snn yace Aisha.

"Tace na'am.

"Yace da farko dae nasan ke me hakuri ne kuma mai biyayya wanda bata bujirewa umarni maigidanta ko ba haka ne ba?".

"Yana mgnr ne hade da dago fuskanta.

"Murmushi kawai tai masa.

"Snn yaci gaba da cewa shiyasa duk cikin matana nake alfahari dake' sbd kedin ta dabance.

"Aisha dake zaune taji kanta yakara girma sbd yadda maigidanta yake yabonta.

"Yaci daga da cewa Hauwa ce ta kirani tace tana hanya dawowa daga tafiya kuma kinga be kamata ta dawo bata sameni a gidan ta bako?".

"Shiru Aisha tai bata tanka ba.

"Yace kinga daganan idan na fita gidan ta zan wuce sbd na riga na sallami Fatima kece kawai be sanarwa ba shiyasa nazo na sanar dake' sbd gudun musake irin wancen karo.

"Wasu kwallane suka cika mata ido kafin ta ankara sun xubo.

"Da sauri Nasir yace subbuhanallah Aisha menene kuma haka meye abin kuka kuma?" Hannu yasa ya dagota ya dorata akan cinyarsa yana share mata hawaye snn yace dan Allah banaso na sake gani hawaye sun xubo akan kyankyawar fuskanki kina jina ko.

"Kai kawai ta daga masa.

"Snn yaci gaba da cewa wlh Aisha ba lalla bane kisan irin sonda nake maki bazan mance farkon ganina dake ba' tun daga lokacin Allah ya jarabcemi da sonki.

"Idan zan zauna ina jero maki irin sonda nake maki da kuma yadda nakeji a cikin zuciyata idan naganki cikin bacin rai ba lallane ki amince ba daga karkema zakice karya nake maki ko kuma kice dadin ba amma wlh Aisha ina matukar sonki.

"Murmushi tai hade da cewa nagode.

"Nasir yace kukan yakare ko yan'mata na?".

"Murmushi tai hade da boye fuska cikin jikinshi.

"Mikewa alhji Nasir yai hade da daukarta cak kamar jinjira ya juya ya shinfidata a gado snn ya cire jallabiyarsa hayewa kan gadon yai hade da cewa bari naiwa yan'mata na tausa.

"Tsanle Aisha tai tana fadin nashiga uku' da sauri Nasir ya cabkota ya maidata karkashinsa Aisha tace dan Allah Yallabai kabari.

"Da haka yaci gaba da janta da wasa har yasamu ya biya bukatar sa snn suka tashi yana rike da'ita suka shiga toilet sukai wanka yaxo ya shirya yatafi gidan Hauwa sbd kada ta iso baya gida.

"Duk da tana shakkansa amma kuma yafi kowa sani halinta batada mutunci' mafi yawancin har gara yaiwa Aisha da Fatima zasu dauke amma ba Hauwa ba.

"Nasir yana fita Aisha taje ta kwashe kayan abinci dayaci takai kitchen.

"Ko kafin alhji Nasir ya'isa har Hauwa tarigashi iya gidan yana parking yashiga daga cikin gidan' wani irin kallo tai masa snn tace sae yanxu kaga damar xuwa ka taroni?".

"Murmushi yai hade da cewa sannu da zuwa malam Hauwa.

"Karisawa yai gun da take zaune ya rungumeta yana fadin kinsha hanya.

📖🖊
🍀🍀
🍀

AURE IBADA NE

FASAHA ONLINE WRITES F.O.W.🍀

MMN USWAN

0⃣2⃣

"Murmushi itama tai masa hade da cewa haba alhji sbd Allah ka kyauta kenan?" Tun kafin na isa na kiraka na sanar dakai ina hanya a tunanin kafin na'iso zakazo nan kajirani ne ashe ba haka bane.

"Yanx sbd Allah ka kyauta kenan? murmushi alhji yai snn yace amma kinsan kafin nazo sae naje na sallami yan'uwanki ko?".

"Hauwa tace ina xuwana dasu wann matsalar kace ba tawa bace idan ni babu ruwana dasu' amma kasan tunda ba dadewa zanyi ba anan har nakoma ko?" Tunda kaga ba dade zanyi ba nan da jibi zantafi.

"Alhji yace Hauwa kenan dadina dake son kai babu ruwanki da damuwar wani taki kawai kika sani.

"Murmushi ita tai kasa snn suka gaisa hade da hiran yaushe gamo.

"Hauwa ita matar alhji Nasir ta biyu a da' gun cikinsu daya kafin ya aureta amma bayan sunyi aure tabar aikin ta koma international business xuwa kasashen larabawa dana turawa tana saro kaya shiyasa ita kanta batada lokacin kanta banle na wani.

"Ita da maigidanta sae sukai wata 2-4 basu hadu ba tun alhji yana korafi har yagaji ya hakuri sbd babu yadda zaiyi da'ita.

"Bayan sunyi sallar isha'i yafita yaje family kitchen ya siyo masu abinda zasuci sbd yasan koda yai mata mgn cewa zatayi tagaji baxata iya shiga kitchen ba'maje fada banxa banle sarki yai sako ba daga tafiya take ba bata shiga kitchen sae tayi ra'ayi banle yau da ta dibo gajiyar hanya.

"Shikuma alhji Nasir a rayuwarsa babu abinda ya tsana a rayuwarsa kamar yaje siyo abinci a kanti a cewarsa da girman sa da mutuncinsa bayan haka gashi da mata har uku amma ace yana siyan abinci a waje?".

"Wancan karo da taxo Aisha yasa tai masu girki akabawa draver ya kawo masu gidan Hauwa' Hauwa batasan daga ina ne abinci yake ba saeda takare ci snn take tambayar Nasir.

"Nasir yace daga gidan Aisha ne'Hauwa tace wata Aisha kuma?".

"Yace Aisha amaryata a take ta haushi da fadi inda take shiga banan take fita ba'tsayawa yai yai shiru yana kallonta mmki ita kanta Aisha bataso girka wanga abincin ba sanadiyar takura mata da yai akan girkin harda kuka saeda ta amma besa taki yiba sbd son da take masa da kuma shakkansa.
Chapter 1 · 0% Book details