Sashe 98
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mommy na shiga ɗakin Daddy ya nuna mata gefen gado, ganin haka ya sa ta zauna jiki a saluɓe tana shirin yin magana ta riski muryarsa yana cewa, "Tsugunne bata ƙare ba." Mommy ta kalle shi ta furta, "Da aka yi yaya?" Wayarsa ya ciro ya fara lalubar lambar Baffan Kabiru sannan ya dubi Mommy ya furta, "Huzaifa ya taka muhimmiyar rawa akan mutuwar auren yarinyar nan domin yanzu haka saki uku Al'amin ya yi mata." A hargitse mommy ta furta, "Saki uku fa?" Daddy ya gyaɗa kansa sannan ya kanga waya jikin kunnensa nan take ta fara shiga, ba a jima ba ya ji Baffan Kabiru ya ɗauka suka gaisa cikin mutumci sannan Daddy ya sanar masa da dalilin kiransa akan kawo Kabiru wurin Malam. Sanin halin Fula ni da mutanen karkara ya sa Daddy ya tabbatar masa da kafin ɗaukan Kabiru zai yi magana da jami'an tsaron garinsu, Baffa ya fahimci abin da Daddy yake nufi don haka ya yi dariya ya furta, "Alhaji yanzu ai babu wannan a tsakaninmu domin mun san ba za ka taɓa cutar da mu ba, Kabiru ai ɗanka ne Allah ya nuna mana gobe da rai da lafiya." Daddy ya ji daɗi don haka ya amsawa Baffa sannan ya tambayi jikin Kabiru, Baffa ya tabbatar masa da yadda yake kullin haka yake har wannan lokacin baya ummm baya umm-umm. Suna gama waya Daddy ya dubi Mommy ya sanar mata da duk abin da ya faru tun daga zuwan su Malam har tafiyarsu. Lamarin ba ƙaramin ɗaga hankalinta ya yi ba, tausayin Raihan ya mamaye zuciyarta ta dubi Daddy ta ce, "Daddyn Raihan an ya Raihan na da rabon aure kamar kowacce cikakiyyar mace kuwa? Ta yiwu haka tata ƙaddara take ƙila mu muke ta abin mu..." Daddy ya katse Mommy da cewar, "Haba Zainab ke fa kike ƙarfafa min gwiwa ta yaya za ki furta irin waɗannan kalaman, Raihan Allah ne ya ba mu ita kum shi zai yaye mata duk wasu matsaloli da ke tattare da ita, duk wanda kika ga bata zauna da shi ba dama can Allah ya rubuta adadin zaman da za su yi da lokacin rabuwarsu, ina kika bar yaron nan Salim wa ya taɓa tsammanin ba za su yi zaman aure da Raihan ba? Wannan abin da ya faru da Raihan da ma can Allah ya ƙaddara mata sai dai mu yi fatan Allah sa haka ne ya fi zama alheri, ta yuwu mijinta yana gaba ta yuwu kuma akasin haka amma duk abin da Allah ya yi mai kyau ne." Jinjina kai Mommy ta yi ta ce, "Tabbas haka ne shi ya sa tun lokacin da yarinyar nan ta ƙwallafa ranta akan yaron nan nake yi mata faɗan ta nemi zaɓin alheri ba son zuciyarta ba, domin ba kowanne abu ne idan muka so shi muka a lokacin yake zame mana alheri ba. Kuma ba komai muke nema a rayuwa mu samu ba don haka a komai ake so ɗan'adam ya riƙe neman zaɓin Allah domin shi ne zaɓin da ba a yin kaico ko nadama a ciki." Daddy ya ajiye wayarsa sannan ya furta, "Wannan gaskiya Allah ya zaɓa mana abin ya fi alheri ." Gabaɗaya suka amsa da Amin.
Tun a cikin daren Daddy ya kira Direbansa ya sanar masa da tafiyarsu zuwa Shanono, gari na wayewa suka ɗauki hanya sai dai kafin tafiyarsu tun asuba Malam ya kira Daddy ya bashi wasu addu'o'in tsari daga shaiɗanu, sannan suka yi sallama. Tun da suka fara tafiya Daddy ya sa aka ware sautin Alƙur'ani mai girma a cikin motar, don haka zuciyarsa wasai yake jinta babu tsoro ko fargaba a zuciyarsa a haka suka shafe doguwar tafiya har Allah ya kai su rugar su Kabiru lafiya. Cikin mutumci da karramawa su Inno wuro suka tarbi Daddy, duk yadda ya ƙi yarda ya ci abinci sai da Inna wuro ta dama masa fura ya sha. Yana gamawa ta yi masa iso wurin Kabiru da yake zaune a ɗakinsa shi kaɗai. Daddy yana shiga ya kalle shi a hankali ya furta, "Allah sarki, Allah ya baka lafiya ka ji Kabiru." Kabiru bai ɗago ba kuma bai tanka masa ba sai Inna wuro ce ta je ta kamo hannunsa, kamar raƙumi da akala haka Kabiru ya bi bayanta har suka ƙarasa wurin Daddy ta damƙa shi a hannunsa. Ba don Baffa ya so ba Daddy ya tilasta masa akan sai sun tafi tare an yi komai akan idonsa, da farko Baffa cewa ya yi shi Daddy ya wadatar a yi komai amma Daddy ya nuna sam ba zai yiwu ba. Kabiru da ƙafarsa ya ƙarasa ya shiga motar sannan su Daddy suka shiga Musa Driver ya fara tuƙi suka ɗauki hanya. Ba su suka shigo cikin garin Kano ba sai bayan sallar Magriba, kai tsaye Daddy ya sa aka wuce da Kabiru wurin Malam. A ɗaki mai lamba biyar aka bawa Kabiru gado, sai da suka saka shi ya gabatar da Alwala ya yi sallah sannan Malam ya sa aka kai masa abinci . Daddy da Baffa suka wuce gida a cewar Malam sai wayewar gari da safe zai fara yi wa Kabiru magana tun da ya lura jinnun jikinsa musulmi ne baya hana shi yin ibada. Baffa na zuwa ya saki baki yana kallon irin dukiyar da aka narka a gidan Daddy, ɗakin da aka kai shi na saukar baƙi kaɗai ya isa abin kallo, ɗakin da Auwalu ya nuna masa da sunan na shi ne gani ya yi har ya kece na Gunduman garinsu. Mamakin irin sauƙin kan Daddy yake don idan kana mu'amala da shi kamar ba shi ne mai tarin dukiya haka ba, abinciccikan da aka ajiye masa kuwa kasa cinye su ya yi sai da gari ya waye aka kwashe wasu.
Lokacin da Al'amin ya fita daga gidan yana shiga mota ya kifa kansa akan sitiyarin mota, haka kawai ya tsinci kansa a cikin nadama bai san dalili ba. Tausayin Raihan ya ji don ya san a zamantakewar da suka yi ba ƙaramin cutar da ita ya yi ba, ji ya yi yana dana-sanin rashin neman yafiyarta don ya san akwai tarin haƙoƙinta akansa da bai sauke ba. A haka ya kunna motarsa ya nufi asibiti yana cikin tafiya ya ga wayarsa na haske, sai a lokacin ya tuna da ya saka ta a slient tun tuni. Misscall ya gani rututu na mahaifiyarsa da Mahaifiyar Sumayya sai kuma na Sumayya da baƙuwar lambar da ake tura masa hotunan tsirancin Raihan, alamar gajeren saƙo ya gani don haka da sauri ya gangara gefen titi ya shiga yana dubawa. Wannan lambar ce da aka saba yi masa magana yana shiga ya ga saƙon kamar haka:
_Ina taya ka murnar rabuwa da Matata da ka yi domin wannan shi ne samun kwanciyar hankalinka, Raihan tawa ce ni kaɗai har abada babu wani lusari da ya isa ya zauna da ita a inuwar auratayya. Ka gode Allah duk irin cin kashin da kake yi mata ban ɗauki fansa mai tsanani akanka da iyalinka ba, daraja ɗaya ka ci shi ne Azkar ɗin da kuke yawan yi, shi ne ya katange ni da ku amma ban ƙyale ka haka ba indai ina numfashi kai da haihuwa sai dai ka ga wasu suna yi, don dama cike nake da mahaifinka saboda abaya ya so halaka ni akan iyalina Raihan. Tun da har Mahaifinka ya gano lagona zan sake tabbatar maka da komai, domin ni Huzaifa ba na tsoro komai ka ga ya faru Raihan ba ta da masaniyar akai, kuma mahaifinka ya yi ƙarya ya sa a kamo ni matuƙar ina numfashi._" Takaici, baƙinciki da ɓacin rai ne ya mamaye zuciyar Al'amin a fusace ya daki sitiyarin motarsa sannan ya fisgi motar da gudun gaske cikin ɗacin zuciya. Yana zuwa Ammi ta riƙa jero masa tambaya sai dai babu wacce ya ya amsa mata don cewa ya yi ta wuce gida zai zo da safe ya same ta. Mahaifiyar Sumayya kuwa saboda ɓacin rai ko ƙurarsa bata kallah ba, yana shiga Sumayya ta kalle shi haɗe da yin guntun tsaki ta ɗauke kanta gefe. Mahaifiyarta ce ta miƙe ta fita sannan Al'amin ya samu damar janyo kujera gaban gadon Sumayya, yana shirin magana Sumayya ta furta, "Tafi ka koma gidansu. Don Allah ka rabu da ni tun da ta fini muhimmanci a wurinta." Al'amin ya haɗiye yawu mai ɗaci don har lokaci ransa a ɓace yake sannan ya ce, "Ya jikinki?" A daƙile ta furta, "Ciki ne ya riga ya fita me ya yi saura, ai dama na san matsiyaciyar matar nan ba za ta bar ni haka ba. Kwartonta ya sa na yi amma ka saka ƙafa ka tafi gidansu, na san ko limamin garin nan za ka kawo aure ne kai da ita ya ƙare tun da saki uku ka yi, kuma duk mai son aurenta da kai sai dai ya yi haƙuri. Cikin fa ya zube Hubby yanzu wannan ma mun yi asararsa?" Sumayya ta fashe da kuka. Tausayinta ne ya kama shi ya kwantar da murya ya fara lallashinta, kuka Sumayya ta saka sai da ƙyar ta yi shiru. Mahaifiyarta na dawowa ya ce su tafi shi zai kwana da ita a asibitin, yadda ya ga rana haka Al'amin ya ga dare don tunanin Raihan ne ya riƙa yi masa kai-kawo a zuciya, tuno waccen rashin lafiyar ta Sumayya ya yi da irin ɗawainiyar da Raihan ta riƙa yi, haka ya riƙa saƙa da warwara har gari ya waye.