Sashe 50
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Katafaran gida ne mai ɗauke da ɗakuna kala-kala an ƙayace shi da kayan alatu na more rayuwa, ƴan uwa da abokan arziki ban da santin gidan babu abin da suke yi, lokacin da su Inno suka shiga gidan sakin baki da hanci suka yi ban da kalle-kalle babu abin da suke yi. Suna shiga kitchen Goggo ta dubi Inno hannu riƙe a haɓa ta ce, "Ni kam Audullahi ya san zafin dukiya kuwa?" Inno ta wara hannuwa ta ce, "Taya ni duba wa Zinaru wai nan fa madafa ce. Ki duba ki ga yadda wasu gilasai suke sheƙi sai kace shagon ɗan kasuwa." Inno na ƙarasa maganar ta miƙa hannu kan wasu fulasai tana shafawa, gabaɗaya ɗakunan babu inda ba su shiga ba. Da sun keɓe za su fara mitar Daddy ya narkar da dukiya, don gidan Raihan sai mahassadi shi zai kushe shi. Kafin wani lokaci tuni kowa ya watse an bar Raihan daga ita sai su Safna ƴaƴan Mama Hafsa ƙanwar Mommy. Raihan na zaune Salim ya kirata a waya, a hankali ta zame mayafinta ta ɗauke muryarta har ta dashe saboda kuka. Haka kawai ta ji gabanta ya faɗi har sai da ta sauke ajiyar zuciya, tattaro jarumta ta yi a hankali ta furta, "Hello!" Daga can ɓangaren Salim ya amsa mata cikin fara'a tare da faɗin, "Habibity ina ta tunaninki." Murmushi Raihan ta yi ta ce, "Amma zan yi missing ɗin su mommy da rigimammun tsofaffin nan." Salim ya kwaikwayi muryarta yana faɗin, "Ni ma missing ɗin ki nake tun ɗazu da safe, kuma ni hanyar nisa take min na ƙagu na ƙaraso wurin Cutie." Kunya ce ta kama Raihan har sai da ta saci kallon su Safna ta ga suna ta danne-dannen waya ta bashi amsa, "I really miss you My Zauji." Dariya sosai Salim yake don shi mutum ne mai barkwanci da fara'a, Raihan ta yi murmushi tana shirin magana ya ce, "Kin san me nake tunani?" Raihan ta ce, "A'a sai ka faɗa." Salim ya yi jim sannan ya ce, "Gaskiya na musamman ne idan na ƙaraso sai na fi jin daɗin sanar miki." Raihan gabanta ya sake faɗuwa don haka kawai take jin faɗuwar gaba tun da aka taho da ita hanyar gidanta. Ta yi ƙarfin halin cewar, "Allah ya kawo min kai lafiya." Salim ya yi ƙasa da murya kamar mai raɗa sannan ya ce, "I so much love you Cutie." Raihan ta yi ƙasa da murya don kar su Safna su ji ta ce, "I Love you too Zauji." Daga haka suka yi sallama sannan suka ci gaba da hira.
Kimanin ƙarfe goma na dare Safna ta kalli Raihan ta ce, "Raihan ni fa na gaji wallahi bacci nake ji, ki kira mijinki su yi su ƙaraso don kar bacci ya ɗauke ni." Raihan ita kanta ta ji shirun ya yi yawa sai dai tana kunyar kar ta kira shi ta ce shiru bai ƙaraso ba, tana cikin nazari suka ji ƙarar tsayawar mota a ƙofar gidan. Tsayuwar motar ya yi daidai da faɗuwar gaban Raihan, ta dubi Safna ta ce: "To ga shi nan ma sun zo da har kina niyyar yi min tijara." Safna ta miƙe tsaye tana gyara ɗankwalinta ta ce, "Babu wata tijara wannan Angon ai ya fiye jinkiri har kusan goma bai ƙaraso ba." Tana rufe baki suka fara jin bugun gida, Safna ce ta fita ta buɗe ƙofar. Da mamaki take bin ta da kallo tare da faɗin, "Mami lafiya ke ce da daren nan?" Mama Hafsa bata kula Safna ba ta ƙarasa ɗakin wurin Raihan a daidai lokacin saƙo ya faɗo wayarta, da sauri ta duba don a tunaninta Salim ne sai dai baƙuwar lamba ta gani, tana shiga saƙon ta riske shi kamar haka:
" _Amarya! Amarya!! Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida, ina taya ki murnar amarcewa tare da yi miki jimamin babban rashin da kika yi. Daga mai ƙaunarki ba dare ba rana_." Tun bata ƙarasa karantawa ba jikinta ya fara rawa gabanta na ci gaba da tsananta faɗuwa, muryar Mama Hafsa ce ta risketa tana faɗin, "Raihan ta so mu wuce gida." Bugun zuciyarta ne ya tsananta ta riƙo hannun Mama Hafsat ta ce, "Mama Hafsa gida kuma? Me yake faruwa? Ina Salim yake?" Mama Hafsat ta fakaici idon Raihan ta ce, "Salim yana can gida wurin Daddy wani uzuri ya kawo shi ya sa Daddy zai haɗa ku ya yi muku magana." Raihan za ta yi magana ta ji wayarta ta fara ringing ganin wannan baƙuwar lambar ya sa ta saurin ɗauka jikinta na ci gaba da karkarwa. Murya na rawa ta furta, "Waye?"
Tun bata rufe bakinta ba ta ji an ce, "Mijinki ne, ku hanzarta ɗauke wancen mushen da ke cikin mota shi da abokansa kafin su ƙone su zama toka, na faɗa musu ni kaɗai ne mijinki ni kaɗai zan mallake ki har abada. Duk wanda ya sake yin gangancin aurenki sai na yi masa abin da ya fi wannan muni." A haukace Raihan ta furta, "Waye kai? Ina Salim yake?" Ƙit ta ji an kashe wayar. A furgice ta dubi Mama Hafsa ta ce, "Wani abu ya faru da Salim wallahi ni na sani, tun ɗazu Salim ya ce min ya kusa ƙarasowa amma har yanzu shiru don Allah karki ɓoye min Mami me ya faru da Salim." Raihan ta ƙarasa maganar kuka na cin ƙarfinta. Mama Hafsa hawaye ne ya fara zuba a fuskarta ta dafa kafaɗar Raihan ta ce, "Mu je gida Raihan." Mama Hafsa na rufe baki Wani kiran ya sake shigowa wayar Raihan, number Farida ta gani. Jikinta har rawa yake ta ɗauka sai dai kukan da ta ji Farida na yi ne ya sake karya mata zuciya, tana shirin yin magana Farida ta ce.
"Matar.Yaya yanzu shi kenan Yaya Salim ya rasu ɗazun nan fa muka rabu ina tsokarta wai shi ne ya..." Raihan bata ƙarasa jin abin da Farida take faɗa ba wayar ta zame daga hannunta luuuu ta faɗi sumammiya.
Hankali a tashe Mama Hafsa ta kama Raihan, Safna na ganin haka ta ɗauko ruwa aka fara yayyafawa Raihan amma ko motsi bata yi ba. Hankali a tashe Mama Hafsa da yaranta suka kama Raihan suka fitar da ita kai tsaye suka saka ta a mota, ban da ruwan hawaye babu abin da Mama Hafsa take yi. Kulle gidan suka sannan suka wuce gidan su Mommy hankali a tashe, saboda irin gudun da take sharawa ya sa ba su jima ba suka ƙarasa gidan. Tun kafin su ƙarasa hankalin Mommy a tashe yake don babban tashin hankalinta bata san halin da Raihan za ta shiga ba matuƙar ta ji rasuwar Salim, Daddy ban da zarya a falo babu abin da yake yi gabaɗaya mutane kowa ya yi carko-carko. Inno na daga kan kujera ban da sharɓar hawaye babu abin da take yi, Goggo ta dubi Inno ta ce, "Kaico mutuwa duniya zancen banza.Ɗazu yaron nan ya gama zolayata wai yanzu shi ne ya yi hatsari motarsu ta ƙone ƙurmus, Allah ka jiƙan Salmanu ka gafarta masa." Inno ta sharce hawaye da gefen zaninta ita ma ta ce, "Ki duba irin budurin da aka yi ni babban tunanina halin da Raihanu za ta shiga, Allah ya sani Salmanu yaron arziƙi ne halinsa na gari ya bishi." Suna cikin wannan halin Mama Hafsa ta shiga ta sanar musu halin da Raihan take ciki, da sauri Daddy ya fita hankali a matuƙar tashe. Ganin halin da Raihan take ciki ya sa Daddy bai yi wata-wata ba ya wuce da Raihan asibiti, da matsanancin gudu ya bar cikin unguwar wanda ya yi daidai da fitowar Mommy cikin kiɗima don ganin halin da Raihan take ciki. Zuciyarta ba ƙaramin karyewa ta yi ba nan take da fara hawaye sai ƙanwarta Hafsat ce ta kama ta suka wuce gida.
Daddy na zuwa asibiti da sauri likitoci suka shiga bawa Raihan taimakon gaggawa, sun jima a kanta sannan suka samu numfashinta ya daidaita, suka yi mata allurar bacci don ta samu hutu. Daddy ban da zarya babu abin da yake yi hankalinsa gabaɗaya baya jikinsa, wayarsa ce ta fara ƙara don tun yana tuƙi wayar tashi take ringing bai samu sukunin ɗauka ba. Jiki a matuƙar sanyaye ya ɗauki wayar ya kara a kunne ba tare da ya furta komai ba, Mommy na jin an ɗauka ta fara magana cikin kuka. "Daddyn Raihan kuna wane asibitin don Allah me yake faruwa da ita? Ina Raihan..." Tattaro jarumta ya yi irin ta Namiji ya daidaita muryarsa tare da katse ta da cewar, "Zainab!" Ya kirata da wata irin murya, Mommy na jin haka kuka ya sake kwace mata jikinta har rawa yake ta ce, "Don Allah Daddyn Raihan..." Sake katse ta ya yi da cewar, "Zainab ki ba ni hankali ba na son shiririta." Shiru mommy ta yi hawaye na zarya a kan dakalin fuskarta. "Raihan ta samu bacci a halin yanzu, ba na son ki sawa kanki damuwa saboda duk abin da kika ga ya faru da bawa rubutacce ne a wurin Ubangiji. Idan Allah ya rubuta Raihan ɗin za mu rasa muna da ikon hanawa ne?" Daddy ya yi maganar zuciya a dake. Kamar Mommy tana gabansa ta girgiza masa kai sannan ta ɗora da cewa, "Ina fargabar halin da Raihan za ta shiga, ban san ya abin zai zo mata ba. Yanzu kuna wane asibitin zan ƙaraso." Ajiyar zuciya Daddy ya sauke sannan ya ce, "Idan har kuka za ki zo kina yi tun wuri ki haƙura da zuwa, yaron nan Salim ya samu kyakkyawar shaida tun daga wurin mutanen gari. Shin ita Raihan ba musulma bace da ba za ta karɓi jarrabawar da Allah ya yi mata ba, idan kina faɗan irin haka ta yaya za ki bata ƙwarin gwiwa har ta cire komai a ranta?" Jiki a sanyaye Mommy ta ce, "Haka ne na fahimce ka, gaya min sunan asibitin yanzu na ƙaraso. Allah ya gafarta masa halinsa na gari ya bishi." Kwatanta mata asibitin ya yi sannan suka yi sallama. Mommy ita da Mama Hafsa ne suka tafi suna zuwa Daddy ya wuce gidansu Salim.