← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 71 OF 110

Sashe 71

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A cikin ƙasa da kwanaki bakwai Raihan duk ta lalace ta fita hayyacinta ta rame, idan ka ganta a yanayin da take ciki za ka yi tsammin ta yi wata doguwar jinyar. Ta koma tamkar mahaukaciya da yake gashin kanta ba a kitse yake ba ya sa duk ya hargitse, fuskarta duk ta jeme ga koyaushe cikin kwanan fargaba take babu wadataccen bacci idan ba ɗaukanta ya yi bata sani ba. Kullin cikin kuka take da addu'ar Allah ya kawo mata ɗauki take yi, sallah kuwa tun ranar da ta yi da dare kullin sai dai ta yi taimama ta yi, daga ƙarshe ma da ta tsorata sai wani ƙaramin dutse ta samu ta riƙa yin taimamar da shi. A kullin ta wayi gari sai Huzaifa ya ziyarce ta har yana nuna mata buƙatarsa a fili amma ƙarfin addu'a da Ayatulkursiyyun da Raihan take yi ya gagare shi ƙarasawa koda kusa da ita ne, sai dai ya tsaya daga nesa da ita. Hasalima sai ya riƙa tsoratata da waɗansu ƙananan halittu masu yanayin mutane amma ba sa kama da bil'adam ga su gajeru ko tsayin gwiwar Raihan ba sa kaiwa. Waɗannan Halittu su suka sake haukata Raihan don wani lokacin har ji take kamar suna yawo a jikinta, bata da aiki sai ihu da kiran sunan su Mommy. Abinci kuwa duk yadda Raihan ta kai ga tsoron cin abincin da take kawo mata dole ta zubar da makamanta ta fara karɓa tana ci, duk da ba kullin yake bata ba a cewarsa sai ta bashi haɗin ya yi mu'amala da ita. A ranar da Raihan ta cika kwana bakwai a wannan yanayin ta yanke shawarar bashi kanta don ta gaji da irin wahalalliyar rayuwar da take ciki, gara ta bashi kanta ko mutuwa za ta yi ta huta don ta lura a wannan wurin da take babu alamar fitarta, idan ta mutu ta sa mu sauƙin rayuwarta kowa ya huta. Tana nan zaune ta ji shigowarsa a wannan karon sanye yake waɗansu irin kayan saƙi tare da wuri sai waɗansu baƙaƙe da jajayan duwatsu, a wurin da ya saba tsaya wa ya tsaya yana kallonta ya ce, "Raihan na nuna miki ƙauna da kulawa amma ko kaɗan baki gani ba, a duk lokacin da na zo wurinki idan na koma sai na yi jinyar jikina saboda a kullin sai kin ƙona min ni, Raihah da ba na sonki ba zan juri haka ba." Durƙushe wa ya yi a wurin cikin rawar murya, nan take hawaye ya fara bin dakalin fuskarsa. Kuka yake sosai kamar ƙaramin yaro wannan ya sake raunana zuciyar Raihan, wata irin soyayyar Huzaifa da tausayinsa ta ji na ratsata. Kuka take sosai tana jin babu daɗi a zuciyarta, tana cikin haka ta riski muryarsa. "Duk duniya ba na ƙaunar wani abu kamar yadda nake ƙaunarki ba, na tabbata wannan yana daga cikin tsarin ƙaddarata. Raihan na haukace a kanki na yi nisa ba na jin kira ta yadda kunnuwa suka doɗe ban da harshenki babu abin da nake iya ji. Ni ba Mutum ba ne kamar yadda kike tsammani ni aljani ne, ina mata da ƴaƴana amma saboda ke duk na haƙura da su na haƙura da kowa nawa don Allah ki ƙaunace ni koda na rana ɗaya ne." Kuka ne ya ci ƙarfin Raihan don ko tsoron ma ya fita daga zuciyarta, cikin kuka ta dube shi ta ce: "Idan na ce ba na ƙaunarka na yaudari kaina ina sonka kamar yadda kake sona Huzaifa, amma zaman mu a inuwa ɗaya ba zai taɓa yuwa ba, saboda kai ba jinsina ba ne. Me ya sa ka hura wutar soyayyarka a zuciyata bayan kasan ba za ka iya kashe ta ba, ina ƙaunarka Huzaifa ina jin soyayyarka amma ka dubi girman Allah kar ka cutar da iyalinka a kaina, ka ci gaba da bawa iyalinka kulawa kamar yadda kake ba su a baya." Raihan ta goge hawayen idonta sannan ta haɗa hannuwanta wuri ɗaya alamun roƙo ta ce, "Ka dubi girman Allah ka mayar da ni wurin iyayena don na tabbata yanzu haka suna cikin wani hali." Cike da farinciki Huzaifa ya dubi Raihan ya furta, "Tabbas zan aiwatar kamar yadda kika buƙata zan ci gaba da bawa Iyalina kulawa, amma don Allah ki daina zancen na mayar da ke gida. Tun da har kin amince kina ƙaunata don Allah ki watsar da komai mu ci gaba da rayuwa, ni Huzaifa na yi miki alƙwari ba za ki taɓa hawaye ba. Zan baki kulawar da ba babu wani ɗan'adam da zai baki ita, wallahi ko kallon banza babu wani mahaluki mai numfashi da ya isa ya yi miki shi. Matuƙar baki amince min ba wallahi ba za ki taɓa fita daga wurin nan ba, balle wani namijin ya samu damar raɓarki har ya kai ga aurenki." Raihan na jin haka ta rushe da kuka don zuciyarta ta fara yi mata wasu-wasi akan ta amince da buƙatar Huzaifa.

Fuska ɗauke da damuwa Daddy ya dubi Malam ya ce, "Shi kenan Allah ya zaɓa mana abin da ya fi alheri amma a wannan lokacin da muke ciki na fara sare wa da samun Raihan, shi kenan ya yi nasara a kanmu." Malam Usman ya girgiza kai haɗe da cewar, "Da ƙarfin addu'a da ikon Allah Huzaifa ba zai taɓa nasara akan mu ba. In sha Allah nan ba da jima wa ba Raihan za ta bayyana, mu ci gaba da addu'a kuma na gaya maka tuni akwai aljanun da na tura don su nemo min su a ko ina suke." Jikin dadi ya gama sanyi don haka murya na rawa ya amsa, "Shi kenan na gode Malam." Yana shirin fita Al'amin ya shiga har ƙasa ya russuna ya gaishe da Daddy tare da sake jajanta masa akan ɓatan Raihan, Daddy ya yi musu sallama ya koma asibiti. Mama Hafsa ita take jinyar Mommy akan dole aka bar wa su Inno Muhammad suke kula da shi, da yake ya saba da su ko rigima baya yi. Jikin Mommy yana sake samun sauƙi jininta ya sauke har tana iya miƙe wa ita kaɗai ta yi wasu abubuwan da kanta, nasihar da su Daddy suke yi mata ne ya sake ƙarfafa gwiwarta ta faula wa Allah lamuranta.

Lokacin da Kabiru ya ƙarasa gida ba ƙaramin tashin hankali ya shiga ba sakamakon ganin yadda jikin Baffajo ya rikice, ƴan uwa sun zagaye shi sai koke-koke ake yi. A daren ranar da ya koma ya sa aka ɗauki Baffajo aka wuce da shi babban asibitin garin Shanono, duk wanda ya ga yadda Baffajo yake jin jiki sai ya tausaya masa. Suna zaune a asibitin Kabiru ya dubi Inna wuro ya ce, "Inna ya kamata ki koma gida ni zan kulla da Baffa, kin ga an bar gida ba kowa ki wuce kawai." Gabanta ne ya faɗi a ɗan firgice ta ce, "Shi kenan wataƙila ya shiga gari." Da mamaki ya dube ta ya ce, "Waye Inna." Miƙe wa ta yi tana yafa mayafinta ta ce, "Ɗan tsintuwa ne Kabiru Allah sa dai bai shiga gari ba." Kabiru sam bai fahimci maganar Inna wuro ba don haka ya sake tambayarta. Inna wuro ta ƙarasa bakin gadon Baffajo sannan ta ce, "Wani yaro ne ƙaninka ya tsinto shi a kogin Iro mai garke, to da yake makarai sun taɓa shi ya rinƙa nema guje-guje kenan don haka muke kulle shi a ɗaki, amma duk da haka yara suna zuwa suna tura shi." Kabiru ya sauke ajiyar zuciya sannan ya ce, "Allah ya bashi lafiya." Inna wuro ta amsa sannan ta yi musu sallama ta wuce gida.

Hasken rana da hayaniyar yara ne suka sata farkawa jiki a tsamame, wani mummunan wari ne ya doki hancinta da ƙarar ƙudaje da ta karaɗe kunnenta. A zabure ta miƙe tsaye tana dube-dube sakamakon tsintar kanta da ta yi a tsakiyar bola, tana shirin karkaɗe jikinta ta riski muryar yara suna faɗin: "Mahaukaciya ƴar macu kul..."

Littafin kuɗi ne 300 idan kina buƙata ki min mgn 0706 206 2624

39
Chapter 71 · 0% Book details