← Book details Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 110

Sashe 16

Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Abar bautarsu ta ji daɗin abin da suka yi, don haka ta yi na'am da wannan shawarar. Suna nan zaune aljanin da ya tafi ɗauko mata jinin da za ta sha ya dawo hannunsa ɗauke da wani Dattijon tsoho, suna shigowa tun ba su ƙarasa gaban abar bauta ba, ta miƙa hannunta guda ɗaya ya warto Dattijan haɗe da ƙwaƙule masa ido tun bai ƙarasa gabanta ba ya yi fata-fata da shi, sauran kawunan da ke jikinta suka kafa kawunansu nan take suka gama da Tsohon. Aljanin ya sake russunawa yana faɗin, "Abar bauta ya isa ko a ƙaro wani." Gyatsa ta yi, tana lashe jinin bakinta, sai da ta tsotse ƙashin ƙoƙon kan tsohon sannan ta ɗago ta ce, "A ina ka samu wannan hallitar mai daɗi?" Aljanin ya washe bakinsa yana murmushi bakinsa ya yi girman rijiya saboda wannan ne karona na farko da abar bauta ta yabi naman ɗan'adam. Ya russuna yana faɗin, "Fansar iyayena na mallaka miki abar bauta, ki fanshi wanda kike so. Ke kika hallakawa kike tseratarwa kike kashewa kike rayawa, na samu hallitar bil'adam a cen bakin wata ƙatuwar bola fitowarsa kenan daga wurin Boka Harisu, yana shirin saka laƙanin asirin da aka bashi a ƙarƙashin shara na ɗauko maka shi." Hatsabibiya ta sake kallon wurin da ƙoƙon kan Dattijon yake tana hura masa iska nan take ƙoƙon kan ya fara mirginawa, har sai da ya yi sau uku sannan hallitar tsohon ta sake dawowa kamar yadda take har da kayan jikinsa. Abar bauta ta kalli Aljanin da ya kawo Dattijon ta ce, "A ɗauke shi a mayar da shi wurin da yake rana ita yau a sake dawo min da shi jinin jikinsa bai ishe ni ba." A firgice tsohon ya kalle su nan take jikinsa ya hau tsuma, ya tsugunna yana roƙo da magiyarsu, yana cikin haka ya ga anɓace da shi daga wurin.

Abar bauta ta dube su ɗaya bayan ta ce, "Na wakilta guda ɗaya daga cikinku da ƙadangare da mage, kuma ya zama wajibi a yau ba sai gobe Raihan ta kawo mana ziyara, shi kuma Huzaifa ku bar min lamarinsa a hannuna amma ba zan cutar da shi ba ko halaka shi alfarmar Mugaza da take kawowa ƙungiya ci gaba." Wata gwauruwar ajiyar zuciya Intisar/Mugaza ta saki tana lumshe ido, ɗaya bayan ɗaya suka fara darewa daga wurin, Hatsabibiya ta yi wa abar bauta rakiya zuwa turakarta sannan ita ma ta ɓace daga wurin.

Daddy shi da abokinsa Alhaji Mustafa suka ƙarasa ofishin Hisbar da su Inno suke, yana zuwa ya samu su Inno a zaune duk sun yi zuru-zuru kamar waɗanda suka wuni suka kwana basu ci ba, musamman Inno da take tsaka da jin mutuwar Hasiya. Suna ganinsa Inno ta fashe da kuka ta kalli ɗan hisbar da ke gefe tana faɗin, "Amma dai kai ƙaramin ɗan sanda Allah ya watsa maka albarka, wallahi ku bar ni a ofishinku amma ni da gidan Audullah sai a lahira ma sadu da juna." Daddy yana shirin yin magana Goggo ta tsugunna a gaban ɗan hisban ta ce, "Yaro ka dubi Allah ka dubi Ma'aiki ko tasha ne ka kaini na wuce albasu." Daddy ya sauke ajiyar zuciya yana faɗin, "Inno me yake faruwa zuwa na yi mu tafi fa." Inno sunne kai ƙasa ta yi kamar ba ta ji me yake faɗa ba, ta kalli Goggo ta ce, "Don Allah ki duba min hallitar jikin Audullahi ta cika ko akwai nasaka, ada na ƙaryata ki amma Allah ya sani gidan Audullahi Makarai ne suke cin karensu babu babbaka a ciki." Daddy zai yi magana ɗan hisbar ya dakatar da shi, don labarin abin da ya faru tuni ya karaɗe ko'ina musamman da ƴan jarida suka samu zancen yaɗawa, Likitoci suka shiga binciken gawar Sulaiman a ya yin da suke neman Kabiru babu inda ba a duba ba amma basu ganshi ba.

Ɗan hisban da kanshi ya yi wa su Inno nasiha, ya sake faɗarkar da su da cewar duk wani abu yana faruwa ne da izinin Ubangiji kuma addu'a takobin mumini ce. Da ƙyar da suɗin goshi aka samu su Inno suka bi Daddy gidan har sai da ya tabbatar musu da cewar ya sauya musu wurin zama.
Lokacin da su Inno suka koma gida tuni gidan ya yi shara-shara babu mutane sosai, don tun a tsohon gidansu ganin abin da ya faru ya sa mutane da dama kowa ya yi ta kansa. Su Goggo a ɗaɗɗare suka shiga sabon gidan, suna tafe bakinsu na motsi da alama addu'a suke yi don ba ƙaramin tsorata suka yi ba. Mommy da kanta ta kaisu ɗakinsu, kowacce ta zauna shiru don ƙawayensu da suka zo gaisuwa tuni kowacce ta cika wandonta da iska.

BAYAN MAGRIBA.

Raihan na kwance a ɗakin mommy lamo kamar mara lafiya, don gabaɗaya wani sukuku take jin ta kamar ba ita ba tun da ta dawo daga duniyar aljanu. Tana daga zaune ta ga wurgawar abu, da sauri ta tashi zaune tsigar jikinta na tashi. Wani ƙadangare ta gani yana buɗe mata baki alamar dariya, sai kuma ya fara ƙada mata jela yana yi yana tunkarota. Ƙura masa ido ta yi lokaci ɗaya ta miƙe tsaye, ta fisge ɗankwalin kanta nan take gashin kanta ya hargitse, ƙananan kifaye ne suka fara fita daga bakin ƙadangare. Lokaci ɗaya ta yi kukan kura ta fisgoshi haɗe da ƙwalla uwar ƙara, tana ɗaukansa ta tura kansa cikin bakinta nan take ta fisge masa kai ta wurgar a wurin gangar jikin ƙadangaren yana hannunta. Mommy da wata ƙanwarta har rige-rigen shiga ɗakin suke saboda duk wanda yake gidan babu wanda bai ji ihunta ba. Suna tura ƙofar suka ganta a tsaye tana riƙe da gawar jangwalagwada jini yana ɗiga, ga kansa can gefe sai zare ido take tana faɗin, "Duk wanda ya ce zai hallaka mini Ɗana wallahi sai na fidda masa kai.

🤭🤭🤭🤭 WUYAR AIKI BA'A FARA BA, HAR YANZU FA ASHAFI NA BAKWAI AKE😎😎 KUN GA KUWA AKWAI SAURAN TAFIYA, AKWAI ƘURA A GABA.🤸🏻‍♀️💃🏼

Share Hilis🌚

*ZAUJATU JINNUL-ASHIQ*

© *AMEERA ADAM*

Littafin kuɗi ne idan kina buƙata 300 ne ta Account 3090957579 Aisha Adam, First bank. Za ki turo evidence ta wannan lambar 0706 206 2624 Whatsapp only Idan kati ne 300 MTN.

*FIRST CLASS WRITER'S ASSO...*

FREE PAGE 8

Ilahirin jikin mommy rawa ya ɗauka Aunty lubna ta zaro ido hankali a tashe don ko a mafarki bata taɓa cin karo da wannan mummunan abin da Raihan ta aikata ba. Mommy tana son tunkarar Raihan amma tana gudun hukuncin da za ta zartar a kanta, murya na rawa ta dubi Raihan ta ce, "Raihan lafiya me kike yi haka? Ƙadangare ne fa a hannunki." Raihan da har lokacin idonta jawur suke ta sake kai kallonta kan ƙadangaren hannunta, ta sake saka wurin jelarsa a baki ta cisgeta da ƙarfin tsiya ta kalli saitin da su Mommy suke ta tofar a wurin. Wani irin huci ta fara yi idanunta na sake firfitowa ta ce, "Ɗana yake shirin cinye min don haka dole na hallaka shi." Mommy ta tunkari wurin tana son Raihan ta wurgar da ƙadagaren hannunta amma tsoron abin da kaje ya zo ya hanata. Don a lokacin da take da shekara goma ntana da makamancin ciwon ta ya tashi ta taɓa cirewa wani almajiri ɗan yatsa, a lokacin shi ma zuwa ya yi zai ƙwaci agwagwar malaminsu da ta fito kiwo Raihan da Mommy sun fito daga mota, a lokacin da suka kai ziyara Albasu. Tuno da haka ya sa mommy take son tunkararta amma tana jin tsoro. Daga nesa da ita Mommy ta leƙa fuskarta tana faɗin, "Raihan ki yarda abin hannunki." Cikin wani irin ƙaraji ta nufo wurinsu gadan-gadan da ihu tini ba shiri su Mommy suka fice a guje kowa yana gudun ceton ransa.
Chapter 16 · 0% Book details