Sashe 74
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da farko na yi niyyar kashe shi faraɗ ɗaya amma sai na fasa don na san idan na kashe shi lokaci ɗaya mutuwarsa za ta zo masa da sauƙi, ni kuma wanda ya bayar da kwangilar cewa ya yi a kashe shi da kisa mai muni. Kakana ya so hana ni ɗaukan wannan aikin a tunaninsa na shiga halwar soyayya ba zan iya taɓuka komai ba, amma sai na nuna masa sam ba haka ba ne hasalima na yi amfani da surarsa don cimma tawa buƙatar, ranar da na fara zuwa gidansu Raihan har a raina na tsorota don na yi tsammanim Mahaifinta zai zargi wani abu har ya hana ni aurenta, amma sai da na ci galaba akansu suka amince min suka ba ni aurenta. Ba zan daina faɗa ba babu maccen da nake so a duk duniya kamar Raihan, don haka da na aureta na ajiyeta a ƙasaitaccen gidana da na fi ji da shi sai dai ko kaɗa ban samu nasarar kusantarta ba, daga ƙarshe a ranar da na so yin galaba akanta na wayi gari da matsanciyar gobara hatta ni kaina ban tsira daga kaidin wannan gobarar ba, kuma na tabbata ba komai ya haddasa min haka ba face kaidin addu'o'in da kuke yi tare da wanda ita kanta Raihan take yi ba dare ba rana. Shi kuma wannan Huzaifan lokacin da na tashi yaudararsa a siffa budurwa na je masa saboda na san ya ƙware wurin neman mata, a ranar na je wurinsa ban sha wata wahala ba don ina yi masa tayin kaina muka jone, muna shiga ɗakin da suka saba aikata baɗalarsu na ɓace da shi ban sauke shi a ko ina ba sai a tsakiyar kogin wani ƙauye, na danna shi can ƙasan ruwa na yi tafiya saboda na tabbata ko awa guda ba zai ƙara ba zai baƙunci lahira, tun a wannan kogin Aljana 'yar Dugwal take ita kuma bata da aiki sai zuƙe jinin bil'adama idan ta gama da shi ta turo gawarsa sama. Hasalima duk wani kogi da kuka sani mai cin mutane zuri'ar 'yar Dugwal ne a ciki domin ita tana daga cikin jinsin jinnu masu zuƙe jinanen mutane. Dalilin da ya sa kuka ga su Daddy sun ɗauko Huzaifa lafiya, sun kawo shi ba tare da wani abu ya faru da su ba saboda ina matuƙar daraja soyayya. Daddy ya nuna min ƙauna matuƙa kafin daga baya ya fara ƙyamatarka, ni kuma ina daraja shi ne saboda soyayya ita ce abu na farko da ya fara nuna min ba ƙiyayya ba domih sai da ya san wanene ni yake ƙi na. Shi kuma wannan yaron zan isar da saƙo ku gaya masa hawainiyarsa ta kiyayi ramata domin na lura yana son tsalla gonar da ba tashi ba, to ahir kabewar kan kabari tafi ƙarfin taushe idan kuma taurin kansa ya kai shi zan nuna masa shayi ba ruwa ba ne don sai na nuna masa ba a ja da ni a soyayya. Yaron da nake nufi ba kowa ba ne face Kabiru idan kuma ya yi gaddama zan bambamce masa tsakanin tsaba da tsakuwa. " Malam Usman ya ja kujera ya zauna sannan ya ce, "Tabbas Huzaifa ya cika gawurtaccen hatsabibi." Huzaifa na jin haka ya bushe da dariya yana faɗin, "A cikin hatsabibancina ba na jin na tsakuro maka cikin cokoli, ni kaina na san ba ni da kyau hatta ni kaina tsoron kaina nake yi." Malam Usman ya kafe Huzaifa da ido ya furta, "Don na faɗi haka ba ina nufin ka gagare ni ba, Huzaifa ba za ka taɓa gagarata ba balle ka gagari ayar Allah. A wannan karon ba zan saurara maka ko na baki dama ba domin na lura kai zuma ne sai da wuta, zan ƙoneka idan ya so kowa sai ya huta." Huzaifa ya fara takawa a hankali sai kuma ya huyo ya sake kecewa da dariya sannan ya ce, "A wannan karon ba zan baka haƙuri ba ka yi duk abin da za ka yi Malam, amma na tabbata ba za ka taɓa hallaka ni ba. Na yi gawurtar da sai na futune ka kai da iyalinka, a da ban yi niyyar taɓa wani naka ba amma a yanzu ni da kai ɗan Halak ka fasa. Zan ganye daga jikin Huzaifa domin wanda ya kawo mana aikin bai cika mana alƙwarinmu ba, zai binne jariri sabuwar haihuwa da ransa ya aiwatar amma bai yanka mana farar jaka ba. Zan bar jikin takwarana amma ka sani ba wai na bar jikinsa kenan ba lokaci-lokaci zan riƙa kawo masa ziyara. Ita kuwa Raihan har abada ina tare da ita, ba za ta taɓe gujewa halwata ba domin ni ne mijinta na har abada." Huzaifa na gama maganar sai Malam Usman gani ya yi ya yanke jiki faɗi yana wani irin numfarfashi, da sauri Malam ya kira sauran yaransa da suke kula da marasa lafiya. Zuwan su keda wuya suka riski Huzaifa yana ta zabga atishawa, turaren habbatussauda aka yi masa sannan Malam ya shafa masa wasu magunguna. Sun jima a kan Huzaifa sannan ya dawo hayyacinsa, a hankali ya riƙa bin mutanen wurin da kallo, miƙe wa ya yi yana tangaɗi sannan da mamaki ya furta, "Su waye ku? Don Allah ku yi haƙuri kar ku cutar da ni wallahi na daina bin kowacce mace, kema da muka haɗu da ke tsautsayi ne." Malam ne ya ƙarasa wurin Huzaifanya ruƙo hannunsa sai da ya kai shi kan gado ya zaunar da shi sannan ya ce, "Huzaifa!" Malam ya kira shi da dakakkiyar murya, kallonsa Huzaifa ya yi yana waige-waige sai kuma ya sa hannu bibbiyyu ya dafe kansa haɗe fa faɗin, "Wash kaina." Da sauri Malam ya sa aka ɗauko wani turare aka turara masa sannan aka shaƙa masa wani a hanci tare da shafe masa jikinta da wani ruwan tofi. Lokaci ɗaya jikinsa ya saki ya faɗi yaraf can gefe yana sauke ajiyae zuciya da sauri, Malam ne ya sa aka kunna masa fanja saboda gumin da Huzaifa yake sharɓawa. Huzaifa ya jima a haka sannan ya ɗago yana sake ƙare wa mutanen wurin kallo, a hankali ya buɗe baki yana faɗin, "Su waye ku? Don Allah nan a ina nake?" Malam ya ƙarasa gabansa ya ce, "Huzaifa!" Da kallo Huzaifa ya dubi Malam yana shirin yin magana ya riski muryara Malam ya ci gaba da cewa, "Ko za ka iya fahimtar a ina kake yanzu." Kallon wurin Huzaifa ya sake yi ya ce, "Don Allah ka yi min rai kar ka halaka ni, wallahi duniya da lahira ba zan sake neman mata ba har abada wannan ma sharrin Shaiɗan ne." Kafaɗarsa Malam ya dafa ya ce, "Dube ni da kyau Huzaifa ka nutsu ka ji." Shiru Huzaifa ya yi yana bin Malam da kallo, kai tsaye ƙofa ya buɗewa su Baba suka shigo Huzaifa na ganinsu da gudu ya maƙale shi yana faɗin, "Don Allah ku zo mu gudu wallahi a taiku za ta jefa ni." Nan take Huzaifa ya sake rikice musu sai da Malam ya yi da gaske sannan ya samu ya koma kan fado ya zauna. Jan Mahaifin Huzaifa ya yi suka fita waje sannan ya dube shi yana faɗin, "Alhamdulillah na san duk abin da yake faruwa kuna ji sheɗanin nan ya fita daga jikinsa, amma duk da haka yana buƙatar kulawarmu domin bai gama dawo wa daidai ba. Za a bar shi ya zauna a nan na tsawon mako guda mu ga yanayin yadda jikin za yi, shi kuma wannan karon ba zai taɓa tsallake wa ba domin na lura taƙadari ne don haka duk in da ya shiga zan saka a kamo shi kuma duk inda ya shiga zai an nemo shi na ƙone shi ƙurnus." Baba gyaɗa kai ya yi cikin farinciki don tuni ya sanarwa da Mahaifiyarsa halin da ake ciki suma sai murna suke yi, Daddy ne ya ƙaraso wurin a kunyace ya dubi Baba ya furta, "Don Allah ka yi haƙuri ku gafarce ni akan abin da ya faru. Wallahi na shiga ɗimuwa akan wannan lamarin don haka nake ganin kamar Huzaifa ne ya tafi mini da ƴa ashe ba haka ba ne." Baba ya dubi Daddy ya ce, "Ka yi abin da kowanne uba zai iya aiwatarwa don haka ja daina ba mu haƙuri, Allah ya kiyaye gaba ya katange mu daga kaidi da hatsabibancin shaiɗanun nan." Lokaci ɗaya suka amsa da Amin.
Kafin wani lokaci tuni labarin dawowar Huzaifa ta watsu a cikin danginsu, ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa duba shi suke yi suna yin Allah sanya alheri. Abin ba iya nan ya tsaya ba har zuwa kafafen watsa labarai haka ka yi ta maganar cikin ta'ajibi don har sai da ƴan jarida suka ji ta bakin Daddy da Baba suka watsa wa duniya. Daga ƙarshe wasu mutanen har ganu suke kamar ƙarne wannan sharhin abin da ta faru, har sai da Ƴan jaridu sula sake hira da Malam Junaid Malunfashi ƙwararran masani ne kan abin da ya shafi harkar aljanu, bayani ya yi sosai na kusan minti ashirin dangane abin da ya shafi jinnu da al'amuransu. Daga ƙarshe ya shawarci al'ummma da su riƙe azkar na safe da yamma, su yi riƙo da addu'a domin takobin muminu ce. Haka Huzaifa ya ci gana da samun kulawar da ta kamata har ya shafe tsawon waɗannan kwanakin, kuma cikin ikon Allah jikinsa ya warware hatta surutan da yake yi ya daina. A ranar da Huzaifa ya ƙarasa warware a ranar ne abokinsa Abubakar ya wayi gari da hausa tuburan don shi har yagar nama jikinsa yake yi yana cewa zai ci, tun abokansa na bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun taimaka masa har suka gaji daga ƙarshe suka tattara shi suka kai shi garinsu, da yake iyayensa tsofaffine kuma ba su da ƙarfi ya sa suka gagara kula da shi ƙarshe ya ɓige da yawo akan bola. Ranar da Huzaifa ya cika kwana takwasa a wurin Malam ne aka sallame shi sakamakon ya warke garau babu wani abu da yake damunsa.
Kafin wani lokaci tuni labarin dawowar Huzaifa ta watsu a cikin danginsu, ƴan uwa da abokan arziƙi sai zuwa duba shi suke yi suna yin Allah sanya alheri. Abin ba iya nan ya tsaya ba har zuwa kafafen watsa labarai haka ka yi ta maganar cikin ta'ajibi don har sai da ƴan jarida suka ji ta bakin Daddy da Baba suka watsa wa duniya. Daga ƙarshe wasu mutanen har ganu suke kamar ƙarne wannan sharhin abin da ta faru, har sai da Ƴan jaridu sula sake hira da Malam Junaid Malunfashi ƙwararran masani ne kan abin da ya shafi harkar aljanu, bayani ya yi sosai na kusan minti ashirin dangane abin da ya shafi jinnu da al'amuransu. Daga ƙarshe ya shawarci al'ummma da su riƙe azkar na safe da yamma, su yi riƙo da addu'a domin takobin muminu ce. Haka Huzaifa ya ci gana da samun kulawar da ta kamata har ya shafe tsawon waɗannan kwanakin, kuma cikin ikon Allah jikinsa ya warware hatta surutan da yake yi ya daina. A ranar da Huzaifa ya ƙarasa warware a ranar ne abokinsa Abubakar ya wayi gari da hausa tuburan don shi har yagar nama jikinsa yake yi yana cewa zai ci, tun abokansa na bakin ƙoƙarinsu wurin ganin sun taimaka masa har suka gaji daga ƙarshe suka tattara shi suka kai shi garinsu, da yake iyayensa tsofaffine kuma ba su da ƙarfi ya sa suka gagara kula da shi ƙarshe ya ɓige da yawo akan bola. Ranar da Huzaifa ya cika kwana takwasa a wurin Malam ne aka sallame shi sakamakon ya warke garau babu wani abu da yake damunsa.