Sashe 82
Zaujatu Jinnul Ashiq Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Usman Ahmad Kafin Hausa shi ne aihinin cikakkan sunan Malam, asalinsa ɗan garin Jigawa ne a wani gari Kafin Hausa. Su biyu ne a wurin iyayensu daga shi sai Yayansa Alhaji Mu'azzam amma akwai tazara mai yawa tsakaninsu ta kusan shekara goma, Mahaifinsa manomi ne don kafin rasuwarsa har sai da aka bashi sarautar sarkin noman yankinsu. Mahaifiyarsu ta rasu tun suna ƙanana daga nan Mahaifinsu ya auri wata mata mai suna Hajjo amma ba yarinya bace, don ko da ya aureta bata haihu da shi ba. Lokacin da Malam ya fara tasowa yaro ne mai ƙwazo da son ilimi ganin haka ya sa Mahifinsu ya yanke shawarar kai shi almajiranci, da yake yayan matarsa a garin Maiduguri yake yana da tsangaya sai Mahaifinsu Malam ya ɗauke shi tare da ɗan'uwansa ya kai su can neman ilimin Muhammadiyya. Yayansa ba a son ransa ya je ba sai don babu yadda zai yi, saɓanin Malam da yake farinciki don kullin burinsa bai wuce ya zama malami kamar limamin garinsu ba. Shi kuma yayansa burinsa ya gaji mahaifinsa ya zama babban manomi, don haka koda aka kaisu Malma ya fi mayar da hankali wurin karatu fiye da ɗan'uwansa. Daga ƙarshe ma sai Yayansa ya riƙa bin kasuwanni yana ƴar buga-bugarsa da haka ya samu ya tsinci abin da ya tsinta saɓanin Malam da ya mayar da hankalinsa kacokan kan harkar neman ilimi. Ba ƙaramar kulawa suke samu ba kasancewar Mahaifinsu na yawan kai musu ziyara akai-akai, kuma duk lokacin da za shi sai ya tafi musu da kayan abinci niƙi-niƙi. A haka suka yi saukar Alƙur'ani suka dawo gida, suna dawo wa yayansa ya faɗa harkar kasuwanci da Noma kamar yadda yake buri. Shi kuma Malam ya sake komawa garin Maiduguri a nan Malaminsu ya saka shi makarantar boko tare da ƴaƴansa sannan ya fara ɗora su akan harkar kasuwancinsa saboda ya fahimci Malam mutum ne Mai amana. Ana cikin haka Malam suka daidaita da Amina Mahaifiyar Al'amin wacce ta kasance cikakkiyar babarbariya. Amina Umar Babagana shi ne ainihin cikakken sunan Mahaifiyar Al'amin, asalinta babarbariya ce ɓangaren uwa da uba duk haifaffin ƴan Maiduguri ne. Ƴar aminin Malamin su Malam ce kusan komai a gidan su Malam take yi, tun suna soyayayarsu a ɓoye har aka fara fahimtarsu. Alokacin da ta kammala firamare (Primary) Malamin Malam ya yi wa iyayensa maganar halin da ake ciki, ba a ɗauki lokaci ba aka saka musu rana lokaci na yi aka ɗaura aure a lokacin tuni Malam ya gama sakandire. Kasuwancin da suke yi Allah ya saka masa albarka don har garuruwa sun fara zuwa suna sarin kaya suna kawo wa Maiduri, kwatsam aka wayi gari da mummunan labarin hatsarin da ya ritsa da Malaminsu. Wannan mutuwa ta ratsa shi bayan kwana arba'in aka yi wa iyalansa rabon gado, akan dole Malam ya koma Kafin hausa tare da iyalinsa da zama. Daga haka ya fara buga-buga yana haɗa wa da aikin noma har ya fara tunanin buɗe ƙaramar tiredar sayar da mayukan habbatussauda da sauran magungunan musulunci, kasancewar yana da ilimi a wannan fannin domin Malaminsa ya koya masa iliminsu tun zamansa a Maiduguri da yake yana da babban shagonsa da yake taimakawa marasa lafiya da masu matsalar aljanu. Da wannan shawarar ya amicewa zuciyarsa har ya yi tunanin buɗe tiredar a jikin shagon Yayansa da ke cikin garin kano, da ƙaramar tireda ya fara sannu a hankali har Allah ya sa masa albarka ya dawo da iyalinsa sakamakon yana zaune a gidan Yayansa. Dawowarsa keda wuya Mahaifinsa Allah ya yi masa rasuwa, wannan rashi ya taɓa su sosai bayan wani lokaci kowanensu ci gaba da neman kuɗinsa, sai dai Malam ya ci gaba da neman kuɗinsa haɗe da neman ilimi sannu a hankali Allah ya riƙa buɗa musu.
Al'amin su biyar ne a wurin iyayensu shi ne ɗan su na uku domin sun haifi yara biyu mace da namiji duk sun rasu, daga Al'amin sai ƙannensa mata huɗu, Aisha, Shamsiyya, Hauwa sai Zarah. An yi wa mata aure Aisha da Hauwa aure ya yin da Zarah da Shamsiyya suke karatunsu a jami'ar Ahmadu Bello da ke Zariya. Al'amin ya yi karatunsa tun daga na boko har na islama a cikin garin kamo, ya karanci ɓanagaren Islamic a jami'ar Bayero yana da matuƙar ƙoƙari da hazaƙa don haka wasu suke kiransa da Babban ƙwaro. Bayan ya kammala Degree ɗin sa Malam ya tura shi jami'ar Madina ƙaro karatu, bayan ya kammala karatunsa suka riƙe shi saboda yaba wa da ƙwazonsa da ƙoƙarinsa da suka yi. Wannan abu ba ƙaramin daɗi ya yi wa Malam ba amma sam Al'amin bai so haka ba saboda ya fi son zama kusa da iyayensa, sai da ya shafe sama da shekara biyu sannan ya zo ya ga iyayensa Amma kafin zuwansa lokaci-lokaci suna kai masa ziyara. Ya shafe kusan shekara biyar yana koyarwa sannan ya nemi dawowa ƙasarsa don ya ci gaba da tallafawa ƙasarsa, yana dawo wa Jami'ar Bayero suka bashi gurbin zama domin dama ba baƙo ba ne a wurinsu, a lokacin da Raihan ta haɗu da shi bai dawo ƙasa Najeriya da zama ba ya dawo ganin gida ne ya shiga saboda akwai wata takarda za a yi masa signing a jiki.
Mu dawo Labari.
Shirye-shirye ya kankama daga gidaje uku na ƙaratowar bikin, daga ɓangaren Amarya Sumayya babu wani shiri da take yi hasalima bikin duk ya fice mata daga rai. Fushi ta ɗauka sosai da Al'amin sai da kyar ya lallasheta ta sauko, sanann suka shiga tsara yadda bikin zai kasance. Duk wata lalura ta Raihan sai da Malam ya sanar wa Al'amin don gudun samun matsala, kuma ya tilasta masa zuwa wurin Raihan don ya tambayeta abin da take buƙata game da biki kuma su fahimci juna kafin auren. Wannan karon ta gan shi ba yabo babu fallasa sai dai babu wata doguwar hira da suka yi, bai jima ba ya yi mata sallama ya tafi saboda ya tambayeta abin da take buƙata na biki ta ce masa bata buƙatar komai don babu wani abu da za ta yi. Idanun Kabiri akan Al'amin har ya zo ya tafi, haka kawai ya ji baya ƙaunar Raihan da Al'amin don ya lura babu soyayyarta a tare shi. Haka ya ci gaba da lallashin zuciyarsa amma kullin ji yake kamar sake rura watar ƙaunarta ake a ransa. Ana saura kwana biyar biki Malam ya kammala haɗa lefen Raihan a daren Ranar shi da wasu abokansa da Yayansa suka kai gidansu Raihan. Ranar juma'ar da ta zagayo cikin satin aka ɗaura auren Raihan, Sumayya da Al'amin. Babu wani shiri da Raihan ta yi don ko event ɗaya babu wanda aka kama aka yi biki a ciki, ƴan uwa ne kawai suka taru aka yi yinin biki. Su Inno sai murna suke don har cewa suka yi irin wannan auren zazzafan rabo ne yake sa a yi shi cikin gaggawa, Kabiru yana ji yana gani aka sake ɗaura wa Raihan aure babu yadda ya iya. Da daddare bayan an yi wa Raihan Nasiha Malam da kansa ya zo ya ɗauki Raihan ya wuce ya ɗauki Summaya dama Al'amin tare suka taho, tun a mota Summaya ta zame mayafinta tana watsawa Raihan wulaƙantaccen kallo. Sai da Malam ya biya ya yi musu siyayya irin wacce ake yi wa amare a daren amarcinsu sannan ya kai su gidansu da ke Kuntau. Kowacce ɓangarenta daban don haka kowacce sai da ya kai ta ɓarinta, kafin tafiyarsa sai da ya haɗa su ya yi musu nasiha mai ratsa zuciya sannan ya yi musu sallama ya fita daga gidan.
Littafin kuÉ—i ne 300 idan kina mgn ki min mgn 0706 206 2624
44